NI USTAZ
Ni Ustazu, Ni Ustazu, Ni Ustazu, Ni Ustaz
*****
Da sunan Rabbana Allah
Nake waƙe ni Ustaz
Da yai mini baiwa ba illa
Ga shi a yau na zama Ustaz
Kai min sutura da ba illa
Kowa na ce mini ya Ustaz
Amincinka da tsirarka
Sun tabbata gun manzonKa
Salatinka da yardarka
Su tabbata gu na manzonKa
Ahlul baiti da sahabbansa
Da duk masu son ɗan Ustaz.
*****
Na dage kan neman ilimi
Don shi ne aikin Ustaz
Tare da yaɗa shi ilimi
Don haka ne halin Ustaz
Ni burina a ilmantu
A bar gaba a gaban Ustaz. . .
Allah ya saka da alheri. Ustazai kuma ga naku.
Amin. Jazakallah Khair. #haimanraees
Hmmmmm ustaz
Yes, ust.