SADIYA
Sallama na yi gunku mutane ga wani labari
Labarin soyayya ta mai haɗari
Na san in kuka ji shi tabbas za ku yi tausayi
Ƙaddara ce ta sani na faɗa yanayi.
*****
Na faɗa kogin son Sadiya
Ita ce burina kullum a zuciya
Har ma an sa mini suna na Sadiya
Ko ina na bi sai ka ji an ce na Sadiya.
*****
Bari in ɗan baku misalin ta Sadiya
'Ya ce mai kyau tamkar zinariya
Haske na idanunta kai ka ce zara ce
Murmushinta yakan iya sa ma a haukace.
*****
Kyawawan laɓɓanta ke sani na ɗimauce. . .
Allah ya jiƙan Sadiya da rahama.
Amin..