Baki mai yanka wuya
Tabbas an sha wuya
Jiki ya yi talata.
A yayin da dubun dubatar jama'a ke murnar shagalin ƙaramar Sallah a wurare mabanbanta a cikin duniya, ni kuwa Haiman cike nake taf da taraddadin abinda ya same ni tamkar randar da aka cika ta da ruwa. Hausawa kan ce 'ƙaddara ta riga fata.' Haƙiƙa wannan batu haka yake, domin kuwa duk iya addu'o'i da fatan alheri da mutane suka yi ta aiko min bai hanani fige kazar wahalar da na yanko wa kaina ba. Amma na san duk wannan bai shafe ku. . .
Tofa! Ana wata ga wata kenan.
Ai kuwa dai kam. Ina godiya
Ka ji wani labari mai kama da Kundin tsatsuba? Bari mu je babi na gaba kuma mu ji abinda zai faru.
Hakanan nan ne. Na gode sosai.
Allah ya ƙara basira
Amin. Jazakallah Khair.
Tirƙashi