Skip to content

Fatalwar Sinu | Babi Na Biyu

4.5
(2)

<< Previous

Aku mai bakin magana

Harbi yana ga kunama

An yanka ta tashi.

Haka dai wannan iska ta yi ta gudu da ni kamar za mu bar duniya, har sai da na manta iya lokacin da ta ɗauka tana wannan gudu da ni. Bayan mun daɗe a cikin wannan yanayi, sai can na ji ni tim…! Na faɗo kan wani abu mai kama da tarin raugar gyaɗa, wanda ina kyautata zaton laushinsa ne kawai ya hana ƙasusuwana karyewa tare da yin rugu-rugu. Kasancewar na galaɓaita ainun, ban ma fahimci cewa wannan igiyar da ta ɗaure ni ta kwance ni da kanta ba balle in lura da inda nake, hakanan dai na langaɓe ina numfashi sama-sama sai ka ce tsohon karen da cuta ta kwantar da shi.

Ina nan kwance ina tunanin ta yaya aka yi har wannan al’amari ya faru da ni? Yaya daga buɗe littafi kawai shikenan waƙi’a irin wannan za ta antayo kaina? Ban kai ga gama wannan tunani ba sai na ji wata murya na cewa,

“Barka da zuwa Haiman, lale-lale marhabin da makafcin zamani, aminci ya kai wa tsafin gidanmu. Haƙiƙa na tabbatar da cewa za ka zo, kuma ga shi ka zo ɗin. Hahaha!

Tsabar galaɓaitar da na yi, tare da rashin ƙwarin jikina suka sa na kasa furta komai kuma na kasa Waigawa inda wannan murya ke fitowa domin in ga ko wanene, kuma na kasa furta komai. Ko da mai maganar ya ji shiru, sai na ji yace,

“A’a, ya na ji ya yi shiru kuma, Ko dai ya mutu ne? Bari mu gani.”

Ko da ya zo nan a zancensa sai na ji wata irin iska mai sanyi tana shiga cikin jikina, ba a daɗe da yin haka ba sai na ji duk gajiyar da ke jikina ta gushe, wahalar da na sha ta kau, sannan wani gagarumin ƙarfi ya shige ni tamkar na yi baccin awa goma na tashi na yi wanka kuma na ci abinci. Ko da na ji wannan canji a jikina, sai na yi zumbur na miƙe tare da waigawa inda wannan murya take fitowa domin ganin ko wanene.

Tooooofah! Me zan gani haka? Ba kowa na gani ba face Kwarkwar Sinu zaune cikin sigar Kafcensa na fim ɗin Racha Hatsabibi. Kujerar da yake zaune a kanta kyakkyawa ce ba laifi, Singiletin da ke wuyarsa kuma koriya ce, yayin da ya ɗaura wani farin zani a ƙugunsa ya kuma ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗaura a kan ɗayan. A hannunsa na dama kuma kwalbar barasa ce wacce a daidai wannan lokaci ya yi rabinta. Ko da muka haɗa ido sai ya yi min wani azzalumin murmushi.

Tsananin mamakin ganina tare da shi a wannan wuri kuma a daidai wannan lokaci yasa na wangame baki kawai ina kallonsa. Bayan mun samu ɗan lokaci muna kallon juna ba tare da ɗayanmu ya ce da ɗayan komai ba. Sai ya ce da ni,

“Zauna mana.”

Kafin in ƙyafta ido sai ga kujera ta bayyana a gabana alhalin da can babu ita. Har na yunƙura da nufin in zauna sai na lura cewa ashe duk allurai ne soke a jikin kujerar, zama kawai suke jira in yi su tsire ni, don haka sai na ƙi zama. Ko da ya ga haka, sai ya ɓarke da dariya kamar sabon hauka, yayi ta yi har ya gaji, daga baya kuma sai ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. A daidai lokacin da ya ɗaure fuskar ne kuma kayan jikinsa suka canja launi izuwa ƙananan kaya. Daga nan sai ya miƙe tsaye ya nufo inda nake yana kaɗa kai cikin murmushin antakaranci kamar dai yadda ya dinga yi a cikin shirin Masheƙi. Ko da ya zo dab da ni sai ya buɗe baki da nufin yin magana. Ai kuwa nan take na ji wani wari, ɗoyi tare da hamami sun durfafo ni, ba shiri na kau da kaina daga saitin inda yake don na ga warin na neman yin barazana wa lafiyata.

Ganin abin da na yi ya sa ya sake fashewa da dariya sannan yace,

“Watau ba ka son warin barasa, amma ka iya yamaɗiɗi da ni kan cewa ni mashayinta ne ko a zahiri, ko ba haka ba? Lallai ka cika mara kunya, tir da kai!

Ko da na ji wanna kalami sai raina ya ɓaci, amma saboda ban san me ke faruwa ba sai na danne zuciyata ban nuna masa ba. Maganar farko da ta fito daga bakina ita ce,

“Waye kai?”

Ko da ya ji wannan tambaya, sai na ga ya yi tsalle ya koma gefe tare da riƙe baki wai shi ya yi alamar mamaki, sannan yace,

“Ai iyye! To in ba ka sani ba ka sani, ni ne nan Mailavarapu Surya Narayana, watau Kwarkwar Sinu kamar yadda ku ‘yan fassare-fassaren nan kuka liƙa min.”

Yayin da ya zo nan a zancensa, sai na ga ya sake murtuke fuska yana hararata.

Ni kuwa wannan bayani da ya yi ba ƙaramin mamaki ya bani ba, na sake dubansa da kyau na ga dai tabbas shi ɗin ne, sai nace da shi,

“To amma ba ka mutu ba? Ya kuma aka yi ka ci gaba da rayuwa?”

Ko da ya ji waɗannan tambayoyi nawa sai ya ƙara ƙyalƙyalewa da dariya sannan yace,

“Ai fatalwata ce kake gani yanzu, kasancewata ɗaya daga cikin mabiya abin bauta Rama da kuma kasancewata ɗaya daga cikin mutanen da aka fi zolaya a duniya, shi ne abin bauta Rama ya bani damar dawowa duniya a matsayin fatalwa bayan mutuwata domin in rama abinda aka yi min wanda kai da ire-irenka kuke sahun gaba wajen aikatawa! Na daɗe ina kafawa masu zolayata tarko suna shallakewa ba tare da na tarka ko ɗaya ba, sai fa kai yau. Don haka ya zama dole in gana maka azaba me raɗaɗi don hakan ya zama sharar fage na taron ɗaukar fansata da zan yi.”

Mamaki da taraddadin abinda ka iya biyo bayan wannan batu nasa ne suka sa na yi shiru na kasa cewa komai. Can dai sai na yanke Shawarar jan shi da labari ko wataƙila hakan ya sa ya bayyana min wasu al’amuran, don haka sai na ce,

“Eermm… Ka ga Kwarkwar ɗan Dakata ka ji…”

” Ai iyye! Watau ni kake kira da Kwarkwar ko? Lallai ka cika mara kunya yaron nan!

Sinu ne ya katse ni da wannan jawabi nasa ta hanyar daka min tsawa. Cikin rawar baki na ce,”

“Erm… To Sinu ka ɗan saurare ni…”

“Kai! Kada ka raina min wayau, sunan ba Sinu bane Srinu ne, kuma kada ka sake kirana da wannan sunan ka kira ni da sunana na asali watau Mailavarapu Surya Narayana!”

Ya faɗa a fusace.

“To Mailavarapu Surya Narayana… Erm.. Ina ganin kamar an samu saɓanin fahimta ne, ina so ka sani cewa ni ba kowa bane a harkar fassara, domin ayyukan da aka yi da ni basu da yawa, hasali ma ni aikin shirinka ɗaya zan iya tunawa na yi. Bugu da ƙari ni ban ga ta yadda za a yi ace wannan abu ya zafafe ka ba da har za ka dawo duniya a matsayin fatalwa ka ce za ka ɗauki fansa. Laifin me masu fassara suka yi maka? Hasali ma dai, shin wai wannan karon ne aka fara fassara ne? In gaskiya ne me yasa waɗancan ba su zafafe ka ba sai wannan? Kuma dama an taɓa mutuwa a dawo ne?

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×