Skip to content

Fatalwar Sinu | Babi Na Hudu

2.5
(4)

<< Previous

Rigiji-gabji

An yi gwajin ƙwanji

An kori kaji.

Ta yiwu baka san ko baki san wanene Mugyambo ba, amma ni da yake na yi mishi farin sani, kuma na san me zai iya aikatawa. Nan da nan ban tsaya wani bin diddigi ko neman labari ba sai na arce a matakin gudu na 160m. Wannan arcewa da na yi ne ta sa Mugymbo da Sinu suka fashe da dariya, ina jin ƙarar tafa hannunsu amma ban damu ba, ni dai kawai gudu nake yi. Ina cikin wannan gudu ne kawai sai na ji kamar daga sama wani abu yazo ya gifta a guje ta gabana, kafin in ankara tuni na yi karo da wannan abin. Ƙarfin haɗuwar da muka yi ne ta sa na yi baya tare da yin tambul na wuntsula can gefe kamar an harbi makwarwar da ke roron gyaɗa a gonar sarji. Na yunƙura na miƙe a hankali saboda na bugu, me zan gani a gabana? Wani ƙaton biri na gani mai matuƙar munin gaske, ina ganin ma sai ya fi King Kong girma da muni da za a gwada su. Nan fa muka tsaya muna kallon juna ni da shi ba tare da na iya motsa ko ɗan yatsana ba saboda tsoro. Shi kuma birin ganin yadda na tsaya wani sololo kamar Karen da ke atini yasa shi ya harzuƙa ya yi gunji ya bugi ƙirji sannan ya yi kururuwa mai ƙarfin gaske!

Dakata! In faɗa muku gaskiya ko In muku ƙarya? Shikenan, na san gaskiya za ku ce don haka babu yadda na iya. Watau saboda tsabar tsoratar da na yi, da na saki wata ƙaƙƙarfar tusa sai da ta keta min wando sannan ta tayar da wata ‘yar ƙaramar ƙura a inda nake tsaye, shi kanshi wannan birin sai da ya toshe hanci saboda mugun warin da ya biyo bayan wannan ƙura, ermmm… Ina nufin hutu. Ganin ya tsaya toshe hanci yasa na yi sauri na bi ta tsakiyar ƙafafunsa na sake arcewa da wani sabon gudun. Ban yi nisa sosai ba na ji ƙasa ta fara girgiza tana tsagewa tare da lanƙwame duk abin da ta samu. Nan fa na fara ‘yan tsalle-tsalle don ganin na kaucewa faɗawa ciki, amma da yake rashin sa’ata ta kai matuƙa, kwatsam sai gani na yi na zo ƙarshen hanyar da nake gudu a kanta. In na juya baya ga biri na biye da ni, in na ci gaba kuma ga rami, in kuma na ci gaba da tsayuwa ƙasar wajen zata iya laƙume ni, to ya zan yi? Can sai wata tubara ta faɗo min, tun kafin in canja shawara kawai sai na juya na tsaya da kyau ina jiran birin ya ƙaraso. Abin ka da dabba be lura da cewa bayyana fili bane kawai babu komai, sai ya danno da gudu da nufin ya ƙwamushe ni. Ko da yazo dab da ni sai na yi sauri na shige ta tsakanin ƙafafunsa na wuce, ƙarfin gudun da yake yi da kuma nauyin jikinsa suka rinjaye shi yayi cikin wannan rami a sukwane, ni kuma saboda ƙarfin hali kawai sai na bishi cikin ramin. Ni da dubarata ita ce, idan ya faɗa ramin ya mutu ni kuma sai in faɗa kanshi hakan zai taimaka min wajen rage min zafin faɗi. Amma kaico! Ko da na bishi ya zamana muna ta yawo a iska ba mu kai ƙasa ba, cikin fushi kawai na ga ya juyo tare da kawo min mangari, kafin in yi wani yunƙuri tuni hannunsa mai kama da gungume ya buge ni a ƙafata ta dama. Hakan ya sa na yi ta katantanwa da juyi a sama kafin daga baya na faɗo ƙasa tim! Kamar kayan wanki.

Bana buƙatar a duba ni, nasan cewa ƙafata ta dama ta karye saboda wani azababben zogi da na ji tana yi min sakamakon bugun da birin yayi min. Ina nan kwance na kasa tashi sai na ji ana tafi daga bayana. Cikin firgici na yi ta maza na waiga inda nake jiyo tafin ba tare da na miƙe ba. Sinu da Mugyambo na gani tsaye a kaina suna min tafi. Cikin dariyar mugunta Mugyambo ya kalle ni yace,

“Yaro lallai dole in yaba maka domin ka yi kasada mai matuƙar girma, amma kada ka damu dama na fi son sheƙe jaruman gaske domin hakan ne zai tabbatar da girman izzata.”

Yana gama faɗar haka sai Sinu ya yi murmushi sannan ya ce,

“Gaskiya da ace za ka fara kafce da anyi babban jarumi, sai dai ba za ka yi tsawon rai ba balle ma ka kai ga ɗaukar wannan shawara, abokina cika masa aiki!

Cikin dariyar mugunta Mugyambo ya nufo inda nake yana taku ɗaiɗai, ko da ya zo dab da ni sai ya ciwo kwalata ya ɗaga ni sama, zogin da nake ji a ƙafata yasa  na yi wani irin nishin wahala. Na buɗe baki na kenan da nufin in gaya masa wata baƙar magana kawai sai ji na yi ya tura min wani abu a bakina. Da fari na ɗauka yaji ya tura min, ashe garwashin wuta ne ya tura min, nan take harshena da maƙogwaro na suka ƙone ya zamana hatta kukan da nake yi ma sautinsa ya gaza fitowa waje. Tsabar wahalar da na sha ce ta sani na sake sakin wata gagarumar tusar wacce hatta shi kanshi Mugyambo sai da ya ja da baya yana cewa Wayyo maƙogwaronsa. Nan fa na kama fagabniya da buge-buge saboda wahala.

Ina cikin wannan hali ne sai na ga wajen ya sauya kala, hadari ya haɗu sannan wajen gaba ɗaya ya ɗau cida. Kwatsam kuma sai na ga wasu abubuwa kamar tsuntsaye suna faɗowa daga sama, sai da na tsaya na lura dakyau sannan na fahimci cewa ashe mutane ne. Mutanen sun yi layi biyu ne suna tafiya ba tare da kowa ya ce wa ɗan uwansa komai ba. Ko da suka ƙara matsowa kusa sai na ji zuciyata ta buga dam! Waɗannan mutane ba wasu bane face jaruman Fina Finan Indiya gaba ɗayansu. Na arewacin Indiya a damana, na kudanci kuma a hagu. Wanda ke jagorancin na arewacin dai ba kowa bane face Shah Rukh Khan da kansa, yayin da Rajinikanth shi kuma yake jagorantar na kudanci. Na yi matuƙar mamakin ganinsu a wannan wuri, abin da ya fara zuwa min a rai shi ne; ‘suma sun mutu ne ko kuma sun zo ɗaukar fansa ne a kaina?’

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×