Gabatarwa
Wannan kagaggen labari ne da ni Autar marubuta na zauna na kirkire shi .Ban kuwa yi dan kowa da komai ba, idan ya yi kama da tsarin rayuwar wasu ma auratannn, tom ni dai kawai arashi ne mai kashe auren wawa. Editing d'in ma a wannan karan bai samu ba.
Saudiyya
Dawowarsu ke nan daga asibiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyar su , bama dai wannan ba tafkeken gidan da suka shiga ga wasu motoci a zube. . .