Washegari Karin kumallo suke cikin hira da farin ciki Hajjiya Sa'adatu kawai abincinta take ci ba tare da tana shiga hirar 'ya'yan nata ba . "Alhamdulillah yau ba aiki sai zaman gida ." Zarah ta yi magna da farin ciki tana gyara zaman Bluetooth d'in dake kunnenta Umar ne ya ce ,"Hmmm aunty Zarah ke nan , kwana biyu kin dena rubutu." Wani kallo ta jefa masa tana cewa ,"Yanzu na fi bawa gidan television d'in mu muhimmanci , dah ni za su tura Dubai wallahi na 'ki zuwa." Mahmud kawai murmushi ya yi , sannan ya kalli Mommy yana cewa. . .