Tafiyar mintina ƙalilan ta kawo hanyar layin ta fara tafiya a slow zuciyarta na tariyo mata abubuwan da suka faru a baya idonta ya fara zubda ƙwalla.
Motoci ne suka shigo layin a guje wata nabin wata alamun babban mutum ko kuma wata tagawar ce zata wuce.
Dan haka tayi saurin taka burki don ta wuce da sauri amma ina! Sai ya nemi ya ƙwace mata .
Motar ta tafi zata daki ginin gidan Baffa cikin ikon Allah, ta tsayar da ita cikin firgici.
Ta fara nishi tare da godewa Allah. Mutanan da suke kofar gidan Baffa da ganin tahowar motar. . .
