Ya dubi su Mama yace" Yaya ne ya samu haɗari yana asibiti " cikin tashin hankali Mama tace" mu tafi gaba daya" Zahra mayafinta ta ɗauka tare da sunkutar Ajmal dake bacci suka fita gaban su na faɗuwa .
Tafiyar mintina goma ce ta kawo su asibtin , sai dai suna zuwa suka tarar da ƴan sanda a gaban wani an luluɓe shi ".
Mujahid ne ya kira layin da aka kira shi , sai ɗan sanda ya ɗaga suka kalli juna .
Wani babban ɗan sanda ya kalle su gaba ɗaya, yadda suke a ruɗe yace" kuyi hakuri , kusa ni dukkan mai rai mamaci ne. . .
