Hankalin ya gushe na tari moto ba tare na fahimci waca irin mota ba ce, ashe motar masu satar mutane ce.
Ina shiga cikin ni dai kawai ban san ya akai ba na bude idona na gani a wani daki da kayana a kusa ni.
Gurin duhu sosai amma ina iya jin kishin mutum a kusa da ni.
Bakina babu abunda yake faɗa sai innalillahi wa'inna ilaihir raji'un domin nasan rayuwata tazo ƙarshe.
Haka na kwana uku ba tare naga mutum ba ko naji muryar motsin da nake ji ba.
Sai dai a tura min abinci naci ta. . .
