Cikin bacin rai Baffa ya mike duk da ciwan ƙafa dake damunsa ya rufe ta da duka hannu biyu, yana cewa " kin cuci baiwar Allah, Innalillahi wa'innailaihi raji'un, mun tafka kuskure " ya faɗi yana tari.
Da sauri su Baffa suka kama shi zuwa kujerar, aka bashi ruwa.
Yace" a tafi gidan Radio da tibi a sanar da cigiyar Zahra" domin bazai yanke wa Suhaila hukunci ba sai ya ga Zahra.
Mahmud kuwa jin muryarsa akai yana cewa" Suhaila na sake ki saki ɗaya, Suhaila na sake ki saki biyu, Suhaila na sake ki saki uku kuma ban yafe. . .
