Suna fitowa aka yi ƙoƙarin saka su Aufana da Salisu a mota domin ceto ransu, yayin da wasu jami’an suke riƙe tamau da su Hamana da yaransa. A gefe kuma Alhaji Labaran ne aka taso ƙeyarsa sai zare idanu yake kamar an jijjiga ɓera a buta.
Kan ka ce kwabo ‘yan jarida sun kewaye wajen sunata ƙoƙarin ɗaukar rahoto. Wanda hakan ya faru ne a shirin barrister domin so yake duniya ta juyo da hankalinta gabaɗaya a kan sanin haƙiƙanin Alhaji Labaran. Aikuwa haƙarsa ta cimma ruwa, domin fuskar Alhaji Labaran ta ɗauku raɗau tare da bayanin ‘yan jarida kan suna son sanin abin da ya kawo shi wajen.
*****
Lokacin da aka isa da su asibiti cikin gaggawa aka karɓe su, nan da nan aka shiga ba wa Aufana taimakon gaggawa. An yi nasarar cire mata harsashin, yayin da aka yi mata allurar bacci. Kamala na kusa da ita, ko nan da can ya kasa matsawa. Gani yake kamar idan ya motsa wani abu zai iya samun ta.
Salisu kuwa ruwa aka saka masa, bayan ya farfaɗo bai gushe ba sai da ya tabbatar ya ba wa barrister wayar da ya yi record ɗin muryoyin Hamana da Alhaji Labaran yayin da suke yi wa Aufana izgilanci da laifukan da suka aikata.
*****
Kafin ka ce kwabo labari ya kewaye gari, duk wata kafar sadarwa ɗauke take da rahoto kan samun Alhaji Labaran tare da ‘yan ta’adda a ƙeɓantaccen gidansa in da suka yi garkuwa da matashiyar lauyar nan.
Wasu ma hadda ƙari kan yadda al’ammuran suka wakana. Nan da nan hankalin shugaban jam’iyarsu ya tashi, domin kasancewarsa dan jam’iyarsu tamkar ɓacin sunan su ne gabadaya. A ranar ya kira meeting na gaggawa a kan yadda za su shawo kan lamarin. Nan da nan suka yanke abin da zai fisshe su. Hira ta musamman suka ƙirƙira kan muhimmancin kyautattawa matasa a gidan rediyon fikra.
Da wannan damar suka yi amfani, ɗaya cikin mabiyansu ya kira da nufin nuna jaje kan abin da ya faru. Ai kuwa nan shugaban jam’iyarsu ya fara alawadai. Ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba. Take ya yi sanarwa kan cewa, ai dama ya daɗe da barin jam’iyarsu shiru suka yi ba su faɗa ba sun tsige shi daga takara sun kuma kori ɓata gari irinsa daga jam’iyyarsu.
A kuma ranar wani cikin abokan jam’iyar adawa ya fito ya yi magana a gidan rediyo, da amsa kuwa kan suna da tabbacin za a iya munamuna a fitar da Alhaji Labaran. Abin da suka kira da ƙafar angulu.
Kafin ka ce kwabo mutanan gari sun faraa yin zanga-zanga tare da yage duk wata takarda mai ɗauke da hotansa. Duk wani waje kuma da suke da tabbacin mallakinsa, suka shiga ƙonawa. Hakan ya haifar da ƙaramar tarzoma da sai da ya haddasa saka dokar ta ɓaci na hana yawo tsawon kwanaki uku.
Abin da ya haifar surutai kala-kala hatta da gidan Alhaji Labaran sai da aka saka matakan tsaro saboda mutane sun nemi ƙona gidan, yayin da ma’aikata kaso goma na gidan sun haɗa kayansu sun gudu.
*****
“Halima! Halima!! Halima!!! Kina ina maza zo ki ji abin da yake wakana yau nesa ta zo miki kusa. Ubangiji ya yanke miki”
Daidai lokacin da ta fito daga banɗaki tana sauri,
“Haba Ladi wannan ƙwala kira kamar karen farauta”
“Ke dai in baki yi ba ni waje ana bikin duniya a kan yi na ƙiyama”
Ta faɗa tana kara mata rediyon a kunnanta, a daidai lokacin da ɗan jarida yake bayyanawa mai sauraro abin da ya faru da kuma halin da suka sami matashiyar budurwa. Take jikin Halimatu ya kama rawa,
“Ladi ban fahimta ba mai ya samu Aufanan?”
“Wannan ne ni ma ban sa ni ba amma dai tabbas asirin Alhaji Labaran ya fara bankaɗuwa kuma duk yadda aka yi da sa hannunta a ciki”
Sake nutsawa suka yi suna sauraron rediyon, sai ga hirar da aka yi da barrister raɗau muryarsa na bayyana, Aufana na karɓar kulawa asibiti da zarar komai ya yi daidai za su shigar da ƙara kotu domin ƙwatar ‘yancinta. Ya ƙara da cewar suna buƙatar gwamnati ta tsaurara tsaro domin kula da Aufana da Salisu.
Take wani farinciki ya bayyana kan fuskarta, tabbas yanayin da ta ji a muryar Abdallah kaɗai ya isa gamsar da ita akwai nasara cikin tafiyar dan haka ta shiga gode wa Ubangiji a kan abin da ya yi musu. Lallai mahaƙurci mawadaci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta tara ƙanannun yara ta soma raba musu alawa.
*****
Kwanci ta shi babu wuya wajen Ubangiji Aufana na samun kulawa daidai gwargwardo, duk wani so da gata tana samunsu daga wajen Kamala da Baba Barista, haka ma Baba Laure. Saboda sosai likita ya yi faɗa kan kulawa da ita saboda matsalar zuciyarta. Ta ɓangaren jami’an tsaro ma suna samun kulawa daidai gwargwardo.
Duk wata hanya da Barista ya san Alhaji Labaran na da ita wadda za ta ba su matsala ya yi ƙoƙarin toshe ta. Cikin ƙanƙanin lokaci ya shigar da ƙara kan neman kare haƙƙin ɗiyarsa da Alhajin ya yi garkuwa da ita a ƙoƙarinta na bankaɗo laifin da ɗansa Muddasir ya aikata.
*****
Duk wani mai haramtaciyya alaƙa da Alhaji Labaran a wannan lokacin hankalinsa ya yi mugun tashi, yayin da mabiyansa ɓoyayyu suka shiga neman mafita ganga-ganga. Sai dai kuma kash hakan ya gagare su domin dai kifi na ganinka mai jar koma.
*****
DAMBARWA.
Zaman kotu na farko.
Kotun maƙare take da ɗan adam, kowa a muhallinsa ko kyakkyawan tari babu mai yi sai da dalili. Kamar yadda dokar koto ta tanadar na zuwa da wuri, musamman ga lauyan da ke kare wani ɓangare da ke ƙara da kuma wanda ake tuhuma. Hakan ce ta kasance ga su Barista tun ƙarfe takwas da rabi suka isa kotun, yana zuwa ya samu abokin aikinsa har ya zo wato Barrister Haladu Ma’aji.
Ya miƙa masa hannu suka gaisa ya zauna suma su Aufana suka nemi waje suka zauna. Kutun tsit can (orderly) maga takardar alƙali ya yi (banging) ƙofar da Alƙali yake shigowa sau uku, take kowa ya miƙe Alƙali ya shigo daga bisani ya yi (taking bow), kowa ya yi (taking bow). Sannan ya zauna kowa ya zauna.
Ya jawo takardu ya yi ‘yan rubuce-rubuce aka soma gabatar da shari’a ta farko kan wata mace da mijinta aka gama yanke hukunci. Daga bisani kuma aka gabatar da wani hukunci na shekaru ashirin kan aikata fyaɗe da wani tsoho mai shekaru saba’in ya yi ga wata ƙaramar yarinya. Shari’a ta gaba da ta rage ita ce ta su Aufana dan haka suka kasance cikin shiri mai sanarwa ya tashi ya sanar kamar haka.
“SHARI’A TA GABA ITA CE SHARI’A TSAKANIN ALHAJI LABARAN TANIMU KORARRAN ƊAN TAKARAR GWAMNA, IN DA AKE TUHUMARSA KAN YIN GARKUWA DA MATASHIYAR LAUYAR NAN AUFANA HALIMATU LABARAN”
Komawa ya yi ya zauna, Barista ya miƙe cike da nutsuwa da kuma girmamawa,
sunana Barrister Abdallah Alhussain Gilɓowa, ni ne nake kare ɓangaran masu ƙara”.
Ya risina ga Alƙalin alamun girmamawa ya koma ya zauna. Sannan abokin aikinsa ya miƙe,
“Sunana Barrister Haladu Zakari Ma’aji, ni ne lauyan da yake kare waɗanda ake tuhuma”
Shi ma ya yi kamar yadda Barista Abdallah ya yi ya koma ya zauna. Alƙali ya yi ‘yan rubuce-rubuce sannan ya ba su damar magana.
(Clark) mai gabatarwa ya miƙe ya fara magana,
“Kotu na son ganin Alhaji Labaran da ake tuhuma”.
Take kotun ta yi tsit, cikin takun ƙasaita ya fito babu ko ɗar a tare da dashi ya nufi (dock) in da aka tanadarwa masu magana ya tsaya yana kallon kowa ɗaiɗai. Nan da nan wajen ya yi tsit ido ya yi masa ca. Mai gabatarwa ya koma ya zauna, Alƙali ya ya dube shi.
“Kai ne Alhaji Labaran Tanimu?”
“Ai kai ma ka san ni ne Alƙali”
Ya faɗa a gadarance, zare glass Alƙalin ya yi,
“Na san kai ne amma tambayarka na yi kai ne Alhaji Labaran Tanimu?”
Yanayin da ya yi maganar da tsauri ya sa ya amsa,
“Ni ne ya mai girma mai shari’a”
“Ka ji abin da ake tuhumarka da shi?”
“Na ji ya mai shari’a”
“Shin ka aikata?”
“A’a!”
Sai da ya ɗan dube shi sannan ya sake magana,
“Lauyen mai ƙara ko kana da abin cewa?”
Miƙewa Barrister Abdallah ya yi ya ɗan risina,
“Ina da abin cewa ya mai shari’a”
“Kotu ta ba ka dama”
“Na gode ya mai shari’a”
Ƙasawa ya yi ya kafe Alhaji Labaran da idanu,
“Ka daina kallo na malam da wasu idanunka kamar ɗan buda ya ji barkono”
“Ka tausasa kalamanka Alhaji Labaran”
Cewar Alƙali, murmushi Barrister Abdallah ya yi tare da gyara rigarsa,
“Alhaji Labaran ko za ka gaya mana ranar biyu ga watan nan kana ina misalin ƙarfe biyu da rabi na rana?”
Take hantar cikinsa ta kaɗa da ya tuna a daidai wannan lokacin suna tare da Kamala yana gargadinsa kan ya ja wa Aufana kunne da shiga gonarsa.
“Ina gidana tare da iyalina”
Ya furta muryarsa na ɗan rawa, juyawa barrister ya yi tare da cewa,
“Ya mai shari’a zan so kotu ta ba ni damar ganin Kamala tare da mai ɗakin Alhaji Lab….”
“Mai ɗakina ba ta da lafiya!”
Ya yi saurin katse barrister, ba tare da Alƙali ya dube shi ba ya furta,
“An baka”
“Na gode ya mai girma mai shari’a!”
Mai sanarwa ne ya miƙe ya yi sanarwa,
“Kotu na buƙatar ganin Kamala tare da me ɗakin Alhaji Labaran”
Kotun ta yi tsit! Sai ga su sun fito Alhaji Labaran tsabar mamaki kusan faɗuwa ya yi a cikin abin tsayawar. Ganin matarsa a tsaye kan duga-duganta ba ƙaramar kaɗuwa ya yi ba. Damar tsayawa Brr. Ya bawa Kamala,
“Bawan Allah ya sunanka?”
“Sunana Kamala Labaran Namuyasamu amma kuma an fi sanina da Gundul”
“Mece ce alaƙarka da Alhaji Labaran?”
“Ni babban yaronsa ne”
Juyawa Alƙali ya yi ya tambayi Alhaji Labaran,
“Shin gaskiya ne shi yaronka ne”
Kallon Barrister Haladu ya yi, ya ɗaga masa kai alamar ya amsa domin yana san shiryawa Kamala tuggu ne, dan haka ya amsa da,
“Shi ne babban yarona kuma amintacce na”
Rubutu Alƙali ya yi sannan ya ba Barrister Haladu damar cigaba da aikinsa.
“Ko za ka iya faɗa wa masu sauraro alaƙar da take tsakaninku?”
“Objection ya mai shari’a barrinster na san sako wani abu daban saɓanin abin da ya tsayar da mu”
Cewar barrister Haladu yana huci,
“Ƙorafi ya karɓu barrister ka kiyaye”
Cewar Alƙali, kai ya gyaɗa sannan ya ci gaba,
“Shin a daidai ƙarfe biyu da rabi na ranar biyu ga watan nan kana ina?”
“Ina tare da Alhaji Labaran a gidansa tare da ni akwai iyalinsa Hajiya Maryam. Wadda take zaune a kan keken marasa lafiya sakammakon matsalar shanyewar jiki. A wannan lokacin ne ɗan sa Muddasir ya shigo yana ƙunƙuni tare da mita kan Aufana ta bada shaidar da za a kama shi da laifi sakammakon ya bige ɗiyar wata mabaraciya cikin tuƙin ganganci har ta rasa ranta. A take mahaifinsa ya fito da waya da kira jami’an tsaron da suke da alhakin karɓar case ɗin ya ja kunnansu tare da ba su maƙudan kuɗaɗe kan su rufe lamarin.
Ya kuma ɗauki waya ya kira babban yaronsa Hamana tare da tabbatar da su saka ido a kan duk wani motsinta”
“Ka tabbatar da an yi hakan?”
Alƙali ya katse shi,
“Na tabbata ya mai shari’a, kuma ga Hajiya Maryam nan a tambaye ta.”
Ya ba shi amsa cike da karsashi da ƙwarin gwiwa.
“Hajiya Maryam abin da ya faɗa gaskiya ne?”
“Gaskiya ne ya mai shari’a”
Ta amsa kai tsaye, “shin mene ne tsakaninki da Alhaji Labaran?”
“Mijina ne kuma uban tilon ɗana, Muddasir”
“Shin kin yarda kan abin da ake tuhumarsa zai iya aikawata?”
“Ƙwarai kuwa ya mai shari’a, domin wannan mutumin ba ƙaramin mara imani ba ne, duk da kasancwarsa uban ɗan da na haifa ba zan gaza bayyana wa duniya haƙiƙaninsa ba. Mutum ne mara imani da tsoron Allah. Bai san kowa ba sai kansa, zai iya komai domin cikar burinsa a kan idona ya yanka yarinya ‘yar shekara goma ya zuba jininta a wata ƙwarya da take ɗakinsa. Wadda yarinyar ta kasance ‘ya ce ga amintacen likitansa, ko da yake har da uban ‘yar aka gudanar da komai saboda son duniya.”
Dalilin ganin da na yi musu ne, suka watsa mini wani ruwan magani gabaɗaya komai nawa ya daina aiki, ji da motsi sai gani da ido kawai. Komai yi mini ake yi. Kuma haka ya ci gaba da shigowa da ƙanann yara yana haike musu a kan idona. Yana mai bayyana mini wannan sirrin sai dai in mutu da shi.
Kullum burina shi ne Ubangiji ya ara mini damar da zan bayyana wa duniya waye mijina”
Take kotun ta kaure da hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakinsa, ‘yan jarida kuwa sai murna suke na samun damar naɗar labari domin ko ba komai wanda labaransu suka fi fita da yawa za su kwashi kuɗi ta ɓangaren abokan hamayya.
Alƙali ne ya yi tsawa ta hanyar doka gudumar umarni, kowa ya yi tsit. Barrister Abdallah ne ya risina ya yi godiya tare da tabbatar da ya gama tambayarsa, Alƙali ya dubi Brr. Haladu,
“Lauyan wanda ake tuhuma ko kana da abin cewa?”
“Ina da shi” Ya furta a taƙaice, zuciyarsa babu daɗi, Doctor Badamasi kuwa duk da ba a ambanci suna ba tuni ya tsargu da kallon da mutane suke yi masa. Musamman matarsa da ta miƙe tana rusa kuka ta fita ta bar kotun bayan ta yaɓa masa baƙaƙƙen maganganu.
Tasowa Brr. Haladu ya yi yana murmushin mugunta,
“Shin me ya kai ka gidan Alhaji Labaran a wannan lokacin?”
“Kirana ya yi kan wani aiki da zan yi masa”
An zo in da yake so, so yake ya jefa Kamala a tarko,
“Shin wane aiki ne?”
“Tsakanina da shi ne ba dole kowa sai ya sani ba”
Ya ba shi amsa kai tsaye, Kamala ka tausasa kalamanka” cewar Alƙalai kai ya gyaɗa tare da neman afuwa,
“Ya mai shari’a ya kamata kotu ta binciki me Kamala ya je yi a wannan lokacin domin bincike ya tabbatar mana da cewa a wannan rana jami’an tsaro sun kama shi Kamala ɗauke da wata mota shaƙe da buhunhunan kayan….”
“Objection ya mai shari’a Brr Haladu na ƙoƙarin shigo da wani abu da zai rikita shari’ar nan”
Brr. Abdallah ya furta yana share gumi,
“Ƙorafi bai karɓu ba”
Alƙali ya furta, daga bisani Brr. Haladu ya yi murmushin mugunta ya ci gaba,
“Ko ba haka ba ne Kamala?”
“Haka ne sai dai kuma ka yi tuya ka manta da albasa, domin wannan mota da kake iƙirarin an gan ni da ita ba mallakina ba ce, ba kuma kayana ba ne a cikinta, komai da komai da yake ciki mallakin wancan azzalumin mutumin da yake tsaye….”
Muryarsa ta soma rawa ya ci gaba,
“Tun da bankaɗa kake buƙata a shirye nake na bayyana ko waye shi ko da hakan zai saka na karɓi hukuncin da ya dace da ni”
Cikin kuka ya shiga zayyano alaƙarsa da Alhaji Labaran tare bayyana irin mugayen ayyukansa. Ya kuma tabbatar idan an shaku a zo da Salisu wanda shi ma ɗaya daga cikin yaransa ne. Nan da nan Alƙali ya cire hula yana share zufa tsabar mamaki. Kotu fa ta nemi rikicewa tilas Alƙali ya bada umarnin ɗaga shari’a tare da tabbatar an zo da Salisu da kuma Hamana wanda aka tabbatar yana hannu. Salisu kuma ƙasa da sama babu shi, abin da ya ɗaure kan barrister tamau domin da shi aka fara gudanar da shari’ar.
*****
Suna fitowa bakin kotun ‘yan jarida suka yi musu rumfa kowa na son jin ta bakin Kamala. Da taimakon jami’an tsaro aka saka shi a mota domin Alƙali ya bada damar a kulle shi. Kuka kawai Aufana take yi, sai yau take jin haushin kanta na rashin duba littafin da Baba Barista ya ce ta duba ta tabbatar da kukan da za ta yi ba zai kai haka ba.
Suna nan tsaye suna jimamin kama Kamala da aka yi, hannunta cikin na Brr Abdallah, yayin da Baba Laure take ƙara rarrashinta, kamar almara Halima ta bayyana gabansu, bayanta Baba Ladi ce mahaifiyar Sadiya mai aikin gidan Alhaji Labaran tare kuma da Indo mabaraciya mahaifiyar yarinyar da Muddasir ya kaɗe.
Idanu Aufana take murzawa domin sake tabbatar da cewa mafarki take yi ko kuma dai gaskiya ne, Anna ce a kusa da ita. Bakinta na rawa ta furta,
“Baba Barista, Anna”
Daidai lokacin da Barrister Abdallah ya juyo bayan sun gama gaisawa da commissioner domin shi ma ya halarci zaman kotun, ya kuma ji daɗin yadda komai ya fara bayyana sai dai ya tabbatar masa da kada ya damu da kama Kamala zai ji da lamarin, yayin da yake zargin akwai waɗanda suke da hannu a rashin Salisu a wajen.
Gabansa ne ya yanke ya faɗi lokacin da Halimatunsa ta haske shi da murmushi, har sai da ya kai hannu ya dafe ƙirjinsa,
“Yaya Abdallah!”
Ta furta da murayar da ko mutuwa ya yi ya farka ba zai manta da ita ba,
“Halimatu Lantanar Ba….”
Sai hawaye, da gudu Aufana ta faɗa jikinta ta sa hannu biyu ta yi mata kyakkywar runguma,
“Dama na faɗa muku Annata tana raye kuka mayar da ni mahauciyar ƙarfi da yaji”
Gabaɗaya suka ɗunguma zuwa gida, cikin tsananin farin ciki da walwala. Barrister tsabar mamaki kasa cewa komai ya yi. Baba Laure ce ta shiga hidima da su abin gwanin ban sha’awa. Bayan komai ya lafa Barista ya dube ta da kulawa,
“Halimatu dama kina raye?”
“Ina raye Yaya barrister, na kange kaina ne daga bayyana gare ku saboda wasu dalilai?”
“Kina nufin ki ce mini ba gawarki aka binne ba”
“Ba gawata ba ce Yaya”
“Ban fahimta ba”
Numfashi ta je, sannan ta dube su ɗaya bayan ɗaya. Murmushin takaici ne ya suɓuce mata, cikin rawar murya ta fara magana,
“Ranar da na nemi izininka kan zan je wajen Yaya, tun fitata gabana yake faɗuwa. Haka na ƙarasa gab da zan shiga soron na tsinkayi muryoyin su Yaya na tashi,
“Gundule akwai gawar wata yarinya da Alhaji ya gama da ita za ka fitar da ita a ɓoye, yallaɓai ya sallami jami’an tsaro ba za su tuntuɓe ka kan komai ba”
“Hamana ban fahimta ba kana nufin Alhaji har yara mata bai bari ba?”
“Babu ruwanka Gundule wannan sirrinsa ne!”
Baya na yi da sauri, jikina babu inda ba ya rawa. Motar na koma na leƙa ciki sai na samu yarinya a kwance amma lulluɓe da yadi, domin sai da na ɗaga na leƙa na gane mutum ne a kwance. Yarinya kayan makaranta ne a jikinta sosai. Motsin fitowarsu ya sa ka na yi maza na bar wajen ina laɓe suka zo suka wuce, Hamana ya sake jaddada masa abin da zai yi.
Sai da na ga fitar Hamana daga gidan sannan na saki ajiyar zuciya. Da ido na raka Yaya har ya shiga ciki. Yana shiga na bi bayansa. Yanayinsa ya nuna bai ji daɗin ganina ba, bayan mun gaisa yake tambayata me ya kawo ni. Ban nuna masa komai ba na fara yi masa nasiha kan rayuwar da yake gudanarwa amma sai ya hauni da faɗa. Rai na ya ɓaci matuƙa saboda ina san sanar da shi Hamana na ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan da suka je Namuyasamu amma bai ba ni wannan damar ba. A zuciye na rika kallonsa,
“Yaya kai wane irin mara imani ne? A kashe yarinya a ba ka a ce ka je ka yasar da ita kuma ka tafi? Ko tsoron a kamaka ba ka yi?”
“Babu ruwanki da rayuwata Lantana, aiki nake domin ahalina”
“Ƙarya kake yaya idan dan mu kake wannan aikin zuwa yanzu ya kamata ka haƙura da shi, domin ba mu rasa ci da sutura da kuma buƙatun ruyuwa ba!”
Hannu ya ɗaga zai ɗauke ni da mari, na riƙe hannun da sauri,
“Ka ba ni mamaki Yaya yanzu da kai aka haɗu ake zalluntar al’umarka. Bari ka ji abin da ba ka sa ni ba. Wannan Hamanan ɗaya ne daga tawagar da suka kashe mahaifanmu, domin na ganshi a cikinsu a ranar da hakan ta faru….”
Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin hakan ya sanya na sassauta murya.
“Wallahi yaya da gaske nake na gane shi, kuma ma abin da ba ka sa ni ba shi ne ya kashe mahaifin yaya Abdallah.”
“Baki ƙarya ba, ai dama na daɗe da fuskantar akwai abin da ki ka taka a kaina!”
Muryar Hamana ta ratso kunnuwanmu, a rikice duka muka juya. Yaya ne ya fara ƙoƙarin kare ni domin wuƙa ya ɗako ya nufo ni, a wannan taƙin na ji zuciyata ta ƙeƙashe kamar na tashi sama saboda baƙinciki.
Suna tsaka da wannan juyayin wuƙar hannun Hamana ta faɗi ƙasa, ganin ya kayar da yaya Kamala ya sa zuciyata yin zafi, duk wata fansa sai da ta motsa mini a lokacin na nufi kansa kamar mahaukaciyar karya. Hannu na sa na ɗauki wuƙar, da nufin caka wa Hamana a ƙahon zuciya take ya yunƙura da hanzari, sai dai kash wuƙar ta sauka a idanunsa na hangu wanda take a wajan jini ya wanke masa fuska ya dafe yana ihu.
A wannan yanayin ya ciro bindiga ya saita ni ya harbe ni a kafaɗata. A wajen na faɗi sumamiyya ganin hakan ya sa ya nufo yaya gadan-gadan sai dai bai samu nasara ba sakammakon tsawar da Alhaji Labaran ya daka masa domin Salisu ya iso daidai lokacin da abin yake faruwa kuma ya kira shi.
Ba tare da yaya ya tsaya sauraransu ba ya ɗauke ni ya kaini asibiti. Doctor Badamasi shi ne wanda ya kula da ni har aka cire mini harsashi. A ranar da na cika kwana uku na samu labarin suna shirin kashe ni ta hanyar alluran da aka ba wa Doctor Badamasi ya yi mini. Salisu ne ya sanar da ni wannan labarin.
Ba ƙaramin tashi hankalina ya yi ba, domin na san matuƙar suka furta abu to kuwa sai sun aikata shi. Sai dai ya yi alƙawari tare da ba ni tabbacin zai fitar da ni daga asibitin ba tare da sanin kowa ba. Hakan kuwa aka yi, bayan ya fitar da ni ya ba ni kuɗaɗɗe masu yawa tare da tabbatar mini in yi nisa da garin.
Da fari na so yin amfani da shawarar Salisu amma daga bisani zuciyata ta shiga faɗa mini ban yi wa ƙasata adalci ba idan na bar ire-irensu suna gudanar da zalunci a bayan ƙasa ba. Shawara ɗaya ce ta faɗo mini na tuna ƙawata Ladi gidanta na nufa a nan na ci gaba da gudanar da rayuwata tare da ɓoye kaina ta hanyar sauya kamannina idan zan fita. Na roƙi Ladi kan za ta yi mini wani aiki amma ba tare da bayyana mata maƙasudi ba.
Da wannan damar muka sami nasara ta fara aiki gidan Alhaji Labaran, kuma ta soma cikin nasara. Domin a ɓangaren matarsa take aiki. Duk wannan tsawon shekarun muna jiran dakon ranar da za mu samu nasara ne a kan Alhaji Labaran. Sosai ta sa ido take kawo mini abin da yake faruwa game da lamarin gidan. Ta sanadinta na san Alhaji Labaran ɗan ƙungiyar asiri ne. Domin ta sha ganinsa cikin dare rungume da ƙwarya da jini a ciki.
Ladi ta sha tambayata game da rayuwata amsa ɗaya ce nake bata ina da ɗiya Aufana kuma ina da buri a kanta. Bayan shekaru biyu na haɗu da Salisu a nan ya bayyana mini cewa bayan ɓatana daga asibiti Doctor Badamasi ya rasa yadda zai yi kada Alhaji Labaran ya gano bai yi masa abin da ya saka shi ba na aikinsa ya samu wata gawar ya haɗata ya ba su a zuwan ni ce aka haɗa ni, wannan dalili ya sa ba tare da kowa ya fahimci gawar waye ba aka sallaci gawa aka binneta a zuwan ni ce.
Ganin zamana gidan ni kaɗai zai saka mini tunani ya sa na fara aiki a gidan marayu. Ina jin daɗin zama a gidan sosai. Sai dai ban shekara biyu da fara aiki a gidan ba na fahimci rabin abincin da marayun suke ci yana samuwa ne ta hanyar yaya Kamala. Tabbas na ji matuƙar daɗi yadda na ga hakan, domin ko ba komai na fahimci alamun shiriya ne ga rayuwarsa. Ban taɓa yadda mun haɗu da shi ba, ban kuma taɓa bada ƙofar da za a fahimci akwai wata alaƙa tsakanina da shi ba.
Tsayin waɗannan lokutan ina sane da rayuwar ɗiyata kuma ina biye da duk wani motsi nata. Sau tari nakan yi kamar na bayyana kaina gare ta sai dai nakan saka wa zuciyata lokaci bai yi ba. Na bayyana a wurare da dama sai dai nakan yi ƙoƙarin na ɓoye wa ganinta. Wannan shi ne ainihin abin da ya faru”
Gabaɗaya ɗakin ya yi tsit! Kowa da abin da yake tunani a ransa. Aufana sai lokacin ta ji ta ɗokanta da san karanta littafin tarihin rayuwar mahaifiyarta. Dan haka tsam ta miƙe ta nufi ɗaki har da saka kuba kada ma wani ya katse ta. Mahaifiyarta ta rakata da idanu tana jin ƙaunarta na ƙara ninkuwa a ranta.
*****
Sosai Aufana ta zubar da hawaye, ba ta fito ba sai da aka yi sallahr magarba, lokacin gabaɗayansu suna falo a zaune. Jikin mahaifiyarta ta je ta zauna, kanta a ƙasa yayin da muryarta take rawa.
“Mama ashe ba ni da cikakken asali ashe ni….”
Hannu ta saka tare da rufe mata baki,
“Kada ki kuskura Aufana. Wannan ita ce ƙaddararki kuma idan kika yi haƙuri Ubangiji zai ba ki ladan masu haƙuri.
Gamuwa da ƙunci da wahala da tsanani da kuma damuwa duk mai yiwuwa ne ga kowa gwargwadon yadda aka ƙaddara masa. Kuma babu wanda zai iya kaucewa abin da aka ƙaddara masa na sauƙi ko tsanani a rayuwar sa, don haka a nan ma haƙuri da duk halin da ake ciki shi ne mafita ga kowa.
Haƙiƙa babu wanda zai zamo mai haƙuri face an ba shi lada mai yawa game da haƙurin sa, kuma an ɗaukaka darajar sa, mutumcin sa ya ƙaru, ya hutar da zuciyar sa, zama da shi zai yi sauƙi da daɗi. Ɗabi’un sa za su zamo abin sha’awa, kuma zai zamo abin misali nagari, kuma abin koyi gurin al’ummah”
Jikinta ne ya yi sanyi ta rungume mahaifiyarta.
“Lallai ne Annah, na gode da samun mahaifiya tamkarki Allah Ya ba mu ikon cinye ƙaddararmu”
*****
Cikin kwanakin da suka gabata gabaɗaya Barista ya mayar da hankalinsa kan yadda za su ƙarasa haɗa hojojjin da suka kamata domin sake kafa hujjar damƙe Alhaji Labaran. Sai dai abin da ya ba su mamaki shi ne rashin samun Salisu sama da ƙasa. Ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba saboda yana da tarin abubuwan sa za a samu daga gare shi. Ba su kaɗai ba hatta da commissioner kansa ya damu da lamarin.
Duk iya bincikensu sun rasa inda za su same shi. Abin da ya tayar musu da hankali shi ne hatta da iyalinsa hankalinsu a tashe yake saboda su ma nemansa suke yi. Ɗan uwansa kuma da aka kama yaransu tare ya rasu sanadin bugawar zuciya. Hakan ya ba wa Abdallah tabbacin lallai akwai lauje cikin naɗi.
Ko da ya je ganin Kamala ma lamarin da suka tattauna ke nan, domin har zuwa lokacin ba a sake shi ba alƙali ya hana a bayar da belinsa har sai abin da hukunci ya yanke masa bayan tabbatar da shaidu.
Ana gobe za su koma kotu ne ya ziyarci Hamana, duk yadda ya so su gana Hamana ƙi ya yi. Hasalima da zagi da cin mutunci suka rabu. Abin ya ƙona masa rai matuƙa ya kuma ji gwiwarsa na neman sagewa domin tunaninsa zai samu haɗin kansa duba da yadda shari’ar ke neman yin juyin waina da Alhaji Labaran.