Skip to content
Part 13 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Kotu Zama Na Biyu

Kamar kowane lokaci kotun ta cika da jama’a. Haka duk wanda ya kamata ya bayyana a wajen ya bayyana. Bayan shigowar Alƙali kowa ya miƙe kamar yadda aka saba. Me gabatarwa ya gabatar da cigaban shari’a ya koma ya zauna. Barista Abdallah ne ya miƙe, ya soma magana.

“Ya mai shari’a zan so kotu ta bani damar ganin Dr Badamasi”

“An baka”

“Godiya nake ya mai girma me shari’a!”

Lokacin da Dr Badamasi ya fito ga ɗaya ya fita a hayyacinsa duk ya yi wani zuru-zuru da shi. Kamar mahaukaci. Kallonsa ya yi tare da furta,

“Kai ne Dr Badamasi?”

“Ni ne”

“Shin ko za ka iya faɗa mana alaƙarka da Alhaji Labaran?”

“Ni likitan gidan sa ne”

“Shin kana da ja akan abin da me ɗakinsa ta faɗa a kanka”

“Ina da ja ya mai girma mai shari’a”

“Mece ce hujjarka…?”

Wuf barista Haladu ya yi ya miƙe,

“Ya mai shari’a barista Abdallah na neman wasa da hankalin jama’a ne, domin kawo Dr Badamasi tamkar wasa da hankalin shari’a ne. Ana tuhumar Alhaji Labaran ne kan yin garkuwa da barista Aufana shin me ya kawo likitansa cikin lamarin?”

“Ƙorafi ya karɓu, barista ka kiyaye”

Alƙallin ya furta bayan ya yi ‘yan rubuce-rubuce. Risina ya yi alamar girmamawa daga bisani ya nemi a bashi damar ganin Hamana. Duk da yana da yaƙinin ba lalai ya samu abin da yake muradi a wajen Hamanan ba. Kai tsaye ɗaya daga cikin jami’an tsaron suka fito da shi hannunsa a ɗaure da ankwa. Suna haɗa ido da Alhaji Labaran ya sakarwa Hamana wata muguwar harara. Tare da ɗauke kansa.

Hakan ba ƙaramin baƙanta ran Hamanan ya yi ba, musamman da ya  tuna komai yana yi ne dan shi.

Shi kuwa Alhaji Labaran ya yi haka ne saboda gargaɗin da barista Haladu ya yi masa kan duk rintsi kadda ya nuna akwai alaƙa tsakaninsu.

Gaba ɗaya Hamana ya gama fahimtar so suke su sakashi a kwana su saahi basila. Taune gefan bakinsa ya yi yayin da zuciyarsa ke faɗa masa abin da ya dace ya yi koda hakan zai sa ya rasa ransa.

Zagayawa ya yi ya tsaya a wajen da ake tsayawa a yi magana. Kallonsa barista Abdallah ya yi,

“Ko za ka iya bayyana wa kotu sunanka?”

Sai da ya cije leɓe ya wani huro baki sannan ya furta,

“Sunana Hamana”

“Sunanka na yanka ba na titi ba”

“Suna na Aliyu Abbas”

“Shin za ka iya bayyanawa kotu alaƙar da take tsakaninka da Alhaji Labaran?”

Kai ya sunkuyar ƙasa, yana tuna garfaɗin Alhaji Sammani da kuma Dr Badamasi kan matuƙar ya sake ya bayana wa duniya akwai alaƙa tsakaninsa da Alhaji Labaran sai sun san yadda za su yi sun kawar da shi ko da an kai shi gidan kaso. Kuma sun tabbatar masa da duk yadda za su yi sai sun fitar da Alhaji Labaran. Ya sa ni sarai gaskiya suka faɗa, idan kuma be yi wasa ba zai ta shi ba shi ga tsuntsu ba shi ga tarko.

“Ubangidana ne!”

Ya faɗa da muryar da shi kansa ya kasa tantance yanayinta. Dubansa barista ya yi yana me jin wani nishaɗi a zuciyarsa kuwa hamdala kawai yake yi.

“Ka tabbata?”

“To ka tambayeshi mana ai ga ka ga shi”

Juyawa  ya yi tare da kallon Alhaji Labaran,

“Shin ko kasan wannan?”

“Ban san shi ba ban kuma haɗa komai da shi ba, na fi tunanin irin yaran nan ne ‘yan jagaliyar siyasa”

Ba Hamana ba, hata barista sai da ya girgiza da batun Alhaji Labaran, amma kuma da ya tuna wani abu sai ya yi murmushi domin Alhaji Labaran ya haɗa tarkon da Hamana ba zai wahalar da shari’a ba.

“Amma mene ne hikimar ganinsa a gidan da aka gano Aufana da kuma kai da aka samu a gidan….?”

Tun kan ya dire abin da yake san faɗa ya tareshi,

“Yar fa ne irin na siyasa, domin ni ranar ma tunda na fito tare da driver na ban sake sanin inda kai na yake ba sai tsintar kai na na yi na gani an zagaye ni ana wasu surutai”

“Kana nufin ka ce maƙiya ne suka yi maka haka?”

“Ga amsar nan ka faɗa barista”

Murmushi ya yi, sannan ya juya,

“Ya mai girma mai shari’a Alhaji Labaran na neman yin wasa da hankalin shari’a ne. Amma bincike ya tabbatar da akwai alaƙa me ƙarfi tsakanin Hamana da shi.

Hasalima akwai hotuna mabanbanta da suke bayyana wurarren da suka haɗu kuma alamu sun nuna suna wata muhimmiyar magana ne.

A ranar ɗaya ga watan daya gabata an samesu a lambun fikra inda suka share awowi masu dama suna maganganu. A ranar biyu ga watan kuma an gansu a titin kusada cikn wata mota me lamba bakwai bakwai uku huɗu. Kuma a wannan motar ne ak sace Aufana a ranar huɗu ga wata. Ga ɗauka da kuma bayanan da suke bayyana haka”

Barista ya risina yana miƙawa Alƙali takardun, daga bisani ya nemi damar ganin Aufana. Cikin mutsuwa ta fito. Ta tsaya kan abin da kowa yake tsayawa,

“Za ki iya bayyanawa kotu sunanki?”

“Sunana barista Aufana Halima Labaran?”

“Shin ko za ki iya bayyana mana abin da ya haɗaki da Alhaji Labaran har ya yi garkuwa dake?”

“Na soma gabatar da bincike ne akan yaron wajansa me suna Muddasir wanda ake zargi kan yi wa Sadiya ɗiyar me yi musu hidima fyaɗe. A ranar da na ziyarci office ɗin likitan gidansu Dr Badamasi ya bani file ɗinta domin shi ne likitan da ya dubata, a bayanin dake ɗauke da file ɗin ya nuna kawai Sadiya ta yi zazzaɓi ne ta rasu. Amma kuma a bayanin dake ɗauke cikin file ɗin jami’an tsaro ya bayyana Sadiya ta rasu ne sanadin haike mata da aka yi daga bisani aka sa igiya aka zarge wuyanta. Akwai hotina da suka bayyana hakan…”

“Ƙarya ne ya mai girma me shari’a barista Aufana nasan amfani da damarta ne ta huce haushinta akan Alhaji Labaran…”

Cewar barista Haladu a fusace,

“ƙorafi be karɓu ba barista. Aufana za ki iya cigaba”

Alƙali ya furta yana rubuce-rubuce. Dr Badamasi kuwa gaba ɗaya jikinsa ne ya jiƙe da gumi ganin asirinsu zai tonu. Domin a satin da ya gabata Sajan ya nemeshi shi da Alhaji Sammani kan ya bashi miliyan biyar ko kuma ya bankaɗo abin da suka ɓoye ya hanashi tare da yi masa barazanar rasa aikinsa. Yana da yaƙinin shi ya ba wa Aufana komai domin ruguza bayansu idan kuwa haka ne ba zai wahalar da shari’a ba zai fito ya bayyana duniya gaskiya ko wa ya rasa. Risina Aufana ta yi tare da cigab da bayani.

“Ya mai shari’a abin da na faɗa maka gaskiya ne domin ina ɗauke da duk wani file me ɗauke da bayani game da rasuwartata, ina kuma roƙon kotu ta yi mata adalci koda bayan kammala wannan shari’ar ne domin mahaifiyarta da me ɗakin Alhaji Labaran sun tabbatar min da akan idonsu komai ya faru. Garkuwar da Alhajin ya yi da ni ya hanani damar shigar da ƙara”

Risina ta yi ta miƙa takardun ga barista shi kuma ya miƙawa Alƙali ya soma dubawa. Kai kawai ya shiga jinjinawa. Daga bisani ya nemi ganin Sajan ya fito ya tsaya gaban shari’a. Alƙali ne ya dubeshi,

“Ka tabbatar da wannan file ɗin na gaskiya ne?”

“Ƙwarai ya mai girma me shari’a domin ina ɗauke ma da muryoyin Alhaji Labaran da yaronsa da kuma wasu cikin abokan tafiyarsa in da suke roƙona akan na ɓoye file ɗin za su bani maƙudan kuɗi naƙi amincewa”

“Ko za ka iya bayyanawa kotu ɗaukar”

“Ga ta ya mai shari’a”

Ya risina tare da miƙa masa, ana kunawa sai ga muryoyinsu raɗau. Take kotun ta hautsine da hayaniya. ‘Yan jarida kuwa sai ɗauka suke domin ɗaukar ta kasance live ne. Sai da Alƙali ya yi tsawa sannan komai ya lafa. Daga bisani aka nemi ganin mahaifiyar Sadiya da me ɗakin Alhaji Labaran. Bayaninsu ya tabbatar da zargin da ake kan Muddasir ba gaskiya ba ne a ƙarshe aka gano Alhaji Labaran ne ya haike mata, kuma matarsa ta tabbatar da ba ita kaɗai ba duk wata me aiki da ta rasu a gidan da sa hannunsa. Sallamarsu aka yi suka koma mazauninsu. Alƙali ya zare glass ɗinsa.

Gaba ɗaya kansa ya ɗaure game da shari’ar ya fahimci Alhaji Labaran yana da tarun laifuka waɗanda suka kasance ƙudunddunannu kuma cike da sarƙaƙiyar da sai an yi taka tsantsana. Dan haka ya nemi a je hutun awa biyu daga bisani a dawo.

Lokacin da suka fito gaba ɗaya ‘yan jarida sun cika bakin kotun maƙil. Kowa burinsa ya sami tattaunawa da Aufana. Wannan dalili ya sa Alƙalin ya ne mi da a dawo da ita ciki, domin ya fihimci bayan Alhaji Labaran to akwai masu mara masa baya. A wannan tsakanin Salisu Ya bayyana cikin matsanancin hali, gaba ɗaya ya rame ga wasu ciwuka marasa kyan gani a tare da shi. Ba ƙaramin daɗi barista ya ji da bayyanarsa ba dan haka ya yi saurin kilaceshi ta hanyar neman alfarmar Alƙali gudun a sami matsala.

BAYAN AWA BIYU.

Kotun ta cika fiye da tunanin me tunani. Ga ‘yan jarida mabanbanta ta kowane fanni. Bayan an sake gabatarwa barista Abdallah ya miƙe,

“Ya mai shari’a har yanzu mun san jin bakin Hamana kan tabbatar da alaƙarsa da Alhaji Labaran”

“Ko tu ta baka dama”

“Na gode ya mai shari’a”

Juyawa ya yi ya dubi Hamana”

” ka ce kana da alaƙa da Alhaji Labaran shi kuma ya musalta hakan ko kana da abin kare kanka?”

Hamana tsabar takaici hawaye ne ya kwaranyo masa, ya tabbatar haƙƙin al’umma ne ya kamashi ba zai ƙayyade adadin rayukan da ya ɗauka ba domin faranta ran Alhaji Labaran lallai duniya ta yi masa atishawar tsaki kuma zai fasa ƙwan kowa ya rasa.

Dan haka ya ɗago da kai ya watsawa Alhaji kallon baka da wayau.

“Kamar yadda na faɗa sunana Aliyu Abbas amma bangar siyasa ta sa na koma Hamana. Ni ɗaya ne daga cikin yaran Alhaji Labaran bayan ni akwai Salisu akwai Kamala wanda muka fi kira da Gundul. Salisu shi ne me ɗaukowa Alhaji Labaran duk wasu bayanai masu faruwa cikin gari. Gundul shi ne yake yi masa safarar miyagun ƙwayoyi duk inda yake buƙata. Ni kuma ni nake kashe masa duk mutumin da ya sha masa gaba.

Sannan kuma ina ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan wannan ƙasa waɗanda muke gudanar wa da Alhaji Labaran duk abin da yake buƙata ta hanyar garkuwa da yaran manyan mutane da kuma shiga ƙauyuka da dama domin kisan al’umma babu gaira babu dalili. Ni ya sa na kashe masa Alhaji Alhussan Gilɓowa da matarsa na kuma ƙona gidansa saboda yana san mallakar kadarorinsa. Ni ne ya saka na kashe mahaifiyar Gundul saboda a ja kunnuwansa.

Haka kuma ni ya saka in kama Aufana domin in kasheta bayan na gama gargaɗinta. Haka kuma ina ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan da suka hallaci ƙauyuka da dama domin murƙushe masa su tare da won gaba da shanunsu da dukiyarsu. A cewarsa da wannan dukiya za su yi amfani wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe.”

Alƙali kawai sai ya tsaya yana dubansa, yayin da kotun ta hautsine. Bayan wani lokaci aka sami nutsuwa shari’ar ta cigaba da gudana. Alƙali ne ya nemi ganin Salisu take kuwa Salisu ya fito. Alƙali ya dubeshi,

“Ko za ka iya bayyanawa kotu sunanka?”

“Sunana Salisu”

“Shin gaskiya ne kana da alƙala da Alhaji Labaran?”

“Tabbas akwai alaƙa tsakanina da shi kamar yadda Hamana ya furta, sai dai zan so Alƙali ya ba ni damar bayyanawa duniya ko waye wannan azzalumin”

Ya furta yana nunashi da yatsa, take ya ƙwalo idanu domin gaba ɗaya ya muzanta. Sai tsuma yake kamar wanda aka jefa a kogin ƙanƙara.

“Kotu ta baka dama”

“Kamar yadda na faɗa ina ɗaya daga cikin yaransa. Sai dai kuma akwai yaransa da suke masa aiki ba tare da son ransu ba sai dan tursassawa da kuma barazana. Da fari Gundul be san me yake ɗaukowa Alhaji Labaran ba domin shi ɗin yana da lallurar cutar mantuwa wadda take tashi lokaci zuwa lokaci.

 Alhaji Labaran ya yi amfani da damarsa ne da sunan zai nema masa magani suka haɗa baki da likitansa Dr Badamasi suka dinga ba shi magungunan da zasu dinga ƙara girman cutar tasa. Lokacin da Gundul ya yi fahimci abin da Alhaji Labaran yake sakashi ɗaukowa ya nemi ya bijire masa sai ya yi amfani da wannan damar ya yi masa barazana kan rayuwar mahaifiyarsa da ƙanwarsa da kuma ɗiyarta wadda ita ce Aufana da ya yi garkuwa da ita a yanzu.

Wannan dalili ne ya sa Gundule rungumar aikin Alhaji Labaran ba tare da musu ba, hakan ya sa ya ke yi masa bauta kamar ba gobe. Fahimtar sa Halimatu ta yi kan waye Alhaji Labaran ya sa ka ta shiga ƙoƙarin fitar da ɗan uwanta ta kowane hali da taimakon Brr Abdallah. Haƙƙanta be cimma ruwa ba domin kuwa a sanadin hakan ne yasa aka kashe mahaifiyarsu. Kuma a sanadin hakan ne ya nemi rayuwar Halimatu wadda a yanzu haka tana raye.

Na kasance ɗaya daga cikin masu kawo masa rahoto shi da muƙarabansa kan abin d ya danganci siyasa ina samun na abinci.

Kwana ashirin da suka gabata an kama motar su Hamana wanda bincike ya ba wa Alhaji Labaran tabbacin da hannun Gundul a ciki da kuma barista. Dalilin hakan na samesu a office da sunan sanar dasu an kama motar a lokacin da na shiga ɗakin taron tsabar ina cikin  ruɗu ban fahimci hirar da suke yi ba, ni dai na ji ana batun ‘yan mata ‘yan makaranta za anemi kuɗin fansa.

Kwata-kwata hankalina be kawo komai ba.  Sai bayan komai ya lafa har ya biya ‘yan sandan cin hanci an saki kayan kuma ya yi umarni da akama Gundul a yi masa dukkan da zai ji a jikinsa. Sanan na zauna na dinga tufka da warwara amma ban gano komai ba. In taƙaice muku labari sai da na koma gida labarin kama yara ‘yan makarantar kwana ya riskeni. Cikin yaran hadda ƙannena biyu da yaran yayana guda biyu da kuma ɗiyata tal dana haifa a duniya.

Lokacin da labari ya riskeni ne na yi tarawa da kwashewar hirarsu anan na fahimci abin da suka shirya. Hankalina ya tashi matuƙa domin ban taɓa tsamanin yana wannan harkar ba. Ba ni da nutsuwa ko kaɗan, matata tana kwance a asibiti saboda tashin hankali hakama mahaifiyata jininta ya hau.

Da kuka na je masa amma ya nuna min cewa in bayar da hotunan yaran zasu san abin yi. A bayanin da ya yi min za a waresu ne ba za yi musu komai ba saboda kuɗaɗɗen da suke buƙata daga gwamnati me nauyi ne, a cewarsu yaran duk na makarantar gwamnati ne iyayensu basu da kuɗin fansarsu.

Lokacin da ya furta min hakan na yi farin ciki matuƙa. Sai dai lokacin da na koma gida na riski zuciyar mahaifiyata ta buga sanadin jin labari a rediyo cewa ‘yan ta’adda sun haikewa wasu cikin yaran na ji a duniya na tsani kaina na kuma tsani Alhaji Labaran da duk ira-iransa a cikin ƙasata.

Zuciyata ta yi nauyi na dinga tuna yanzu rai nawane zai salwanta kamar yadda na mahaifiyata ya salwanta? Abin mamaki ko gaisuwa be zo min ba kuma ya sami labari ina kuka na kirashi ina sanar masa amma sai ya ba ni haƙuri da sunan za su je yaƙin neman zaɓene.

Zuciyata ta yi rauni, na shiga dana sani mara tushe. Na dinga tuna yanzu irin wannan ya kamata mu zaɓa da sunan shugabanci? Mutumin da zai jagori a haikewa ‘ya’yanmu a ɓata matasanmu a lalata gonakinmu? Wannan dalili ya sa na fito na bayyanawa Brr. Komai sai dai kuma a ranar da za a soma gudanar da shari’a su Alhaji Sammani abokansa suka sace ni.

Satina ɗaya suna gana min azaba tare da gargaɗi me ƙarfi, ina can amma hankalina yana nan ban sami kuɓuta ba sai yau da safe a sanadin bacci da yaran da suke gadina suka ka yi. Ina roƙon wannan kotu me albarka data huƙunta ni da Alhaji Labaran daidai da abin da ya aikata”

Tsit! Kotun ta yi, yayin da masu raunin cikinsu suka soma kuka. Kasancewar shari’ar live ce ya haddasa ƙone-ƙone cikin gari hatta gidan Alhaji Labaran matasa sun yi nasarar saka masa wuta. Bayan rubuce-rubuce Alƙali ya nemi ganin Dr Badamasi, Alhaji Sammani da sauran abokansa huɗu waɗanda suka kasance manya ne a ƙasar. Sai kuma aka nemi ganin Halimatu. Wadda fitowarta ta tsurar da Alhaji Labaran. Har be san lokacin da ya furta,

“Dama ba ki mutu ba?”

Alƙali ne ya daka masa tsawa ya yi muƙus. Bayan an gabatar da ita ta amsa tambayoyin da suka kamata. A inda ta bayyanawa Alƙali Hamana na ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga ƙauyansu. Tana kuka tana bayar da tarihin abin da ya faru a garinsu. Gaba ɗaya jikin mahallata kotun ya yi sanyi. Masu raunin zuciya kuwa tuni suka soma sharar hawaye. Yayin da ‘yan jarida ke ta aikinsu baɓu ƙaƙƙautawa.

Alƙali ne ya yi rubuce-rubucen da suka kamata ya ɗago tare da furta,

“Bayan dogon binciken da aka gabatar tare hojojji masu ƙarfi kotu ta yankewa Alhaji Labaran da kuma Hamana hukuncin kisa ta hanyar rataya, tare da horo me tsanani na wata biyar. Bisa tsari na kundun shari’a shafi na tara da ɗigo uku da arba’in. Abokansa kuma tare da Dr Badamasi kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da horo me tsanani.

Kamala kuma kotu ta yanke masa hukuncin tara tare da buƙatar a sadashi da ƙwararrun likitoci domin bincikar ƙwaƙwalwarsa.

Haƙiƙa kotu ta yi nazari ta kuma yi amfani da shaidar Salisu da kuma Dr Badamasi kan rashin lafiyarsa. Yayinda shaidar da barista ya gabatar game da takardunsa na asibiti domin ƙoƙarin wankeshi suka gamsar da kotu. Salisu kuma kotu ta yanke masa hukuncin shekaru huɗu tare da horo me tsanani.

Muddasir kuma kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai domin bincike ya tabbatar da cewa ya kaɗe Aisha ne bayan ya sha kayan maye, wanda hakan ganganci ne mutum ya bugu sannan ya kuma ya hau titi yana tuƙi. A ƙarshe kotu tana kira ga gwamnati da ta yi ƙoƙari wajen tsaurara tsaro a ƙasa tare da gggauta binciko wurarren da aka killace yaran da aka yi garkuwa da su”

Alƙali na gama wannan bayanin ya miƙe ya tare da furta,

“Kotu”

*****

A kan idon kowa aka saka su a mota, cikin ƙasƙanci. Yayinda barista ya kwashi, Kamala da Halima da Baba Laure da Baba Ladi da Indo mabaraciya da kuma Aufana a motarsa. lafiyarsa. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya iya magana har suka isa gida.

*****

Kwanci ta shi babu wuya wajen ubangiji, an gudanarwa da su Alhaji Labaran hukunci. Barrister Abdallah ya fi kowa murna har walima ya yi. Sossai hakan ya ƙara fito da ƙimarsa musamman a faggen aiki. Shari’ar ta ƙayatar da mutane da dama.

Cikin ikon Allah aka gayyaceshi hira ta musamman a gidan talabishin. Sossai ya ware ya faɗakar da al’umma musamman kan matasa masu tasowa. Hirar ta ja hankali fiye da tsamani. Bayan sati biyu da hirar ne shugaban ƙasa ya nemi ganawa da shi domin ya saurari hirar da aka yi da shi.

Lokacin da saƙon ya sameshi hankalinsa ya tashi, ya soma tunanin ko ya yi wani abu ne wanda be yi musu daidai ba. Sai dai ya cika da mamaki lokacin da shugaban ƙasa ya bashi tabbacin suna son bashi damane ya kafa wata ƙungiya da zata miƙe domin ƙarfafa guiwar samari kan hanyoyin karɓar ‘yanci. Hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba.

Da wannan damar ya yi amfani ya shigar da buƙatarsa kan mabaratan da Aufana taketa ƙoƙarin inganta rayuwarsu. Cikin ikon Allah shugaban ƙasar be watsa masa ƙasa a ido ba. Cikin tsakanin aka ƙaddamar da Barrister Abdallah inda shugaban ƙasa ya fito ya yi bayani me tsauri kan yadda za a tsaurara tsaro a ƙasa baki ɗaya. Bayan sati biyu ya zauna tare da jagororin tsaro na ƙasa, inda suka fitar da tsarrukan kawo cigaba a ƙasa ta fanin tsaro.

Matakin farko da aka ɗauka shi ne yanke network ɗin ɓangarorin da aka fi gudanar da ta’addanci tare da rufe kasuwani. Ba akwana biyu ba jami’an tsaron suka samu nasarar kama ‘yan ta’adda sama da guda ɗari. Haka ya yi matuƙar faranta al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma jami’an sun haɗa kai da ma’aikatan sadarwa wajen gudanar da binciken yadda ya kamata. Cikin ƙanƙanin lokaci aka sami zaman lafiya a ƙasa tare da tsattsauran tsaro game da rayukan jama’a.

Ɓangaren mabarata su ma an ɗauki matakin kame kan kama masu bara a bakin titi, sai dai kafin hakan an kafa ƙungiyoyi manya da ƙanana inda aka ware masu ƙarfin cikinsu ana koya musu sana’o’i. Tare da yi musu rigister a ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman.

Nakasassun ciki kuma sossai da sossai aka ware wasu kuɗaɗɗe na musamman ana basu duk ƙarshen wata tare da gargaɗi me ƙarfi kan yin bara duk wanda kuma aka kama ana cinsa tara me tsoka. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga sunan Aufana na zagawa matsayinta na garkuwar nakasasu. Tana ƙoƙari matuƙa wajen aiwatar da aikinta, ta kuma ƙara ƙaimi wajen amfani da yanar gizo domin ƙara hanyoyin tallafa musu.

Mahaifiyarta na tsaye a bayanta tsayin daka wajen bata shawarwarin da suka kamata, tare da ƙara koya mata dabarun zama cikin mutane da kuma hanyoyin da zata kyautatawa waɗanda take jagoranta. Kafin shekara biyu sai da ta karbi shaidar girmamawa sama da shida saboda jajjircewarta.

Sossai hakan yaa ragemata tunane-tunane domin da fari tunanin rashin cikakken asali ya so taɓa duk wani karsashinta amma kasancewarta cikin aiki kodayaushe sai ya zamana bama ta da lokacin zama mara amfani bare wani tunani ya shiga kanta.

Ganin hakan sai ya ƙara mata ƙaimi wajen yadda za a tallafi amjirai na tsangayu, ta yi shawara da barrister Abdallah inda ya tsaya mata suka shigar da koke kan hakan kuma alhamdulillahi kokensu ya karɓu. Wannan matakin da aka ɗauka ya yi matuƙar taimakawa wajen rage mabarata a bakin titi dama tsangayoyi.

ƘARSHE.

<< Fitsarin Fako 12

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×