Tun bayan kammala makarantarta sai ya zamana kaɗaici yana nema ya yi mata yawa. Tun asalinta ba mace ba ce mai tarkacen ƙawaye ba, hasalima ƙawarta ɗaya ce Mardiyya, yanzu haka tana gidan mijinta tare da ɗiyarta Safna, suna zaune a garin Abuja.
Baba Barista in ya zauna a gida sai ƙarshan sati, kawu kuwa dama shi ba gwanin hira ba ne, yanzu ne ma yake ɗan janta da hira saboda bayanin da likita ya yi masa, kaɗaici zai iya asasa ciwonta.
Yau tun safe ta tashi da wani irin karsashi sakammakon mafarkin da ta yi da. . .