Skip to content
Part 9 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Kurman baƙi….

Murmushi ne ya suɓuce a kumatunta,

“Wai Ladi da gaske kike yi mini Aufanata ce ta tsaya tsayin daka domin kwatar ‘yancin Sadiya?”

“Ƙwarai kuwa ba ma Sadiya kaɗai ba, a yadda na fahimta hadda ɗiyar Indo ‘yar maula, domin bincike ya tabbatar da Muddasir ne ya buge ta wanda sanadin hakan ya yi ajalinta.”

Wata ƙwallar farinciki ce ta bayyana akan kuncinta, a yau tana jin zuciyarta wasai ko yanzu ta rasu ta san ta bar irin alkhairi. Kewar ɗiyarta tare da tsohon mijinta suka taru suka cunkushe zuciyarta har ƙirjinta ya soma nauyi.

“Halima ya kamata ace zuwa yanzu kin bayyanawa duniya kina raye ko dan ruhikan ahalinki su sami salama.”

“Akwai lokaci Ladi, akwai abin da nake jira da zarar ya faru kuwa zan fito duniya ta sani, ni ma ina kewar dangina. Ina buƙatar in ji ɗumin ɗiyata kamar yadda kowace uwa take ji.”

“Na ji amma ya kamata ki ba ni labarinki, da dalilinki na sa ni yin aiki a gidan Alhaji Labaran.”

Shiru ta yi kamar ba za ta tanka ba sai kuma ta murmusa tare da furta,

“Ƙi ƙara haƙuri.”

*****

A bangaren Aufana kalaman kawunta sun sakata sanyin jiki sosai. Sai dai tana muradin jin asalinsu da kuma inda suka fito amma kuma tana buƙatar lokaci dan haka ranar ma ba ta bada himma ta duba littafin ba hankalinta ya ta fi kan yadda za ta tara hujojji ƙarfafa. Duk da ta san cewa Baba Barista ya faɗa mata cikin littafin za ta samu ababban dogaro amma kuma tana ganin kamar karatun ɓata lokaci ne.

Daran ranar da za ta soma zuwa bincike kwana ta yi addu’a da safe ma sai da ta yi sadaka kafin ta fita. Misalin ƙarfe takwas a chamber ta yi mata, Baba Barista da kansa ya ɗauke ta zuwa asibitin da aka kai Sadiya wanda ya ba ta tabbacin abokinsa ne mai asibitin, kuma shi ne likitan kafatanin iyalan Alhaji Labaran. Amma ya ja kunnenta da kada na bari ya san akwai alaƙa a tsakaninta da shi.

Tun daga bakin asibitin ta tabbatar da tsaruwarsa, hakan ya tabbatar mata da ankashe maƙudan kuɗi a cikinsa. Bayan an yi mata iso ta shiga office na babban likitan, daga yanayin da ya amsa mata da kuma hannu da ya miƙo mata da sunan gaisuwa ta tabbatarwa kanta ta kawo kanta gidan da sai ta yi taka tsantsan.

Janye hannunta ta yi tana mai gyara tsayuwata, fuskata babu walwala ta ce,

“Sunana (barrister) Aufana.”

Dariyar shaƙiyanci ya saki,

“Aufana wa?” ganin ba ta ba shi amsa ba ya sa ya ci gaba cike da shaƙiyanci, “Oh sorry Aufna ɗiyar mace ko?

Da sauri ta kalle shi ƙirjinta na dokawa yayin da zuciyarta take matsewa da wani irin yanayi.

‘Me kalamansa suke nufi kada dai ya san wani abu game da rayuwata. Ko shi ya sa Baba Barista ya yi min kashedi kan sanin alaƙarsu da juna.’

Cikin zuciyarta take wannan maganar.  Amma sai ta gimtse ta ce,

“Na fahimci abin naka na yi ne, wai jifan sauro da guduma!”

“To ke ya kike gani in da babu ƙasa ai nan ake gardamar kokawa”

“Haka ne, ban sa ni ba ko ka fini gaskiya. Dan haka zan iya cewa ƙila hakan ne, ƙila kuma wani ƙulli ne da warware shi zai watsa rayuwar wasu. Ba ragon azanci ba ne idan yaro ya zabi alewa ya jefar da gwal, saboda a duniyarsa alewa ta fi daraja.

To amma, ya aka yi kai da girmanka za ka ajiye gwal ka ɗauki alewa? Ban san me ya ruɗe ka ba; amma idan don zakinta ne, ka sani, gwal na da darajar da za ka iya sayen hannun jari a kamfanin alewa. Idan ka gane, gwal ɗaya ya fi alewa dubu!”

Haka kawai ta ji idan ba ta ba shi amsa me gautsi ba kamar ya sha ta basila, ta kula shi ɗin mahaukacin kare ne bai san nuni ba sai duka. Bisa dukkan alamu so yake ya ɓata mata rai dan haka ba ta sake ba shi damar ƙofar magana ba ta ci gaba,

“Aufana kaɗai turken jaki ce bare kuma ka haɗa da rayuwar jigonta wato Halimatu dan haka zan iya zama?”

Gaba ɗaya jikinsa sai ya yi sanyi, murmushin gefan baki ta yi a ranta tana raya,

‘Wato wannan mutumin raina ni ya yi ke nan. Ko kuma yanayi na ne na salo-salo ya sa yake ganin zai sha ni ya warke, oho?’

Ba tare da jiran cewarsa ba ta zauna tare da buɗe file ɗinta,

“Na zo ne kan case ɗin Sadiya wadda rahoto ya bada tabbacin kai ne ka dubata kafin ta cika zuwa ga Mahaliccinta.”

Bai tanka ba sai ya buɗe wata drower ya ɗauko wani file ya miƙo mata,

“Ki je ki duba za ki sami komai a ciki.”

Ba haka ta so ba, amma kuma ta lura kamar ta kai shi bango dan haka ta miƙe cike da jin ƙarfin zuciya.

“Shi ke nan zan je in duba kamar yadda ka ce amma idan na ga ban gamsu ba zan dawo domin ka amsamin wasu tambayoyi.”

“Zan baki file na gaibu ne ‘yan mata?”

“A’a Baba tsoho amma babu rami me ya kawo rami? Shi hargagin damu ai name sanda ne!”

“To zai haɗu da me kokara”

“Allah ko?”

Ta yi furucin tana kaɗa idanu, abin ka da mayen mata sai hakan ya tafi da shi.  Ganin yadda ta tafi da imaninsa baki ɗaya ya sa ta saki dariyar shaƙiyanci,

“Allah ya yi gado bana hawa ba, in ji kuturu da ya ga kunama”

Furucinta ya fargar da shi kwaɓar da ya yi, amma kafin ya farga ta banko masa ƙofar ta kama gabanta. Cikin ranta kuwa dariya take tare da ganin jarumtarta. Tana tafe tana wani tunani a ranta.

Tana fitowa saura ƙiris ta yi karo da wani jibgeggen Alhaji. Wanda ganinsa ta sanya hantar cikinta kaɗawa. Idan ba ta manta ba wannan shi ne Alhaji Labaran Tanimu. Wani ƙwarin gwiwa ta ji ya zo mata, ta sake gyara tsayuwarta sosai maimakon ta ba shi hanya sai ta kanƙane.

“Yallaɓai barka da wannan lokaci”

Tsayawa ya yi yana dubanta da wani irin yanayi cikin idanunsa, kafin ka ce kwabo ‘yan jarida sun zagaye su.

“Dan Allah ko zan sami magana da kai game da case ɗin rasuwar mai hidima a gidanka. Ka yi haƙuri na tsayar da kai a in da bai kamata ba, ban kuma gabatar maka da ko ni wace ce ba. A taƙaice dai sunana Barista Aufana, ba ni da yadda zan yi in ganka a arha kamar haka shi ya sa na yi wannan kuskuren.

Wannan karon sai da bakinsa ya buɗe saboda mamaki, amma ganin idanu a kansu ya saka shi aro fuska ta biyu ya yaɓa, sai ya yi kalar tausayi,

“Bari ke dai, yarinya mai haƙuri, kada ki damu zan baki kowane haɗin kai amma ki same ni a gida”

“Ai dama ka san tsutsa ba ta cin ragwan goro, sai dai me ya hana har….”

“Na ce ki same ni a gida za ki sami abin da kike buƙata!”

Ya faɗa da tsawa tare da guntun ɓacin rai da ya bayyana a kan fuskarsa. Daga nan ya ratseta ya wuce yana wani murmushi na gefen baki cike da ma’anoni kala-kala. Jiki a sanyaye ta wuce office ba ta ɓoyewa Baba Barista komai ba, ta ga alamun damuwa a fuskarsa amma kuma sai ya nuna mata babu komai. Ko da suka tashi aiki tare suka tafi da shi babu wata hira da suka yi wanda ba haka suka saba ba.

*****

Yana shiga office ɗin ya zauna, yaransa suka yo waje. Kallon da ya yi wa Doctor Badamasi ya tabbatar masa da cewa akwai matsala. Dan haka ya maida dukkan hankalinsa a kansa,

“Me waccan kyanwar ta ce maka da ta shigo?”

Bai ɓoye masa komai ba game da yadda suka yi daga bisani ya ci gaba,

“Alhaji ina ganin kamar wani abu yarinyar ta taka!”

“Hasashenka ya zama gaskiya Badamasi, sai dai ta makaro domin zan yi maganinta kamar yadda na yi na mahaifiyarta na wulata ƙiyama. Ni Alhaji Labaran murucin kan dutse ne. Ɗan Gilɓowa ma ya yi ya bar ni duk wata fankama tasa ta tashi a banza tun da sai da na tura shi barzahu na kuma gaje duk wata kadara da dukiya ta su.

Tun jiya Sajen Atiku ya kirani ya ba ni tabbacin ta je office ɗin su kan case ɗin Muddasir, ya kira Gundul ya sanar masa shi ne ya buga masa gargaɗi. To a wannan karon zan yi abin da na ga ya fiye mini ko da Gundul zai guje mini sai na ga bayan kyanwar nan”

“Ka yi daidai yallaɓai.”

Cewar Doctor Badamasi, daga nan suka ci gaba da tattauna munanan burikansu tamkar ba za su mutu ba. Duk wata hira ta Alhaji da Doctor a kunnuwan Aufana tare da Baba Barista. Domin ta yi hikimar mana maɗaukar sauti a jikin teburinsa ta ƙasa wadda take haɗe da ƙaramar wayar salula kuma a kunne wayar take tare.

Dama dan hakan ta tanadi wayar, layinma na musamman ne wanda kuɗin da ake ja cikinsa ba masu yawa ba ne. Rigister aka yi masa na tsawon wata uku ba tare da saka masa sisi ba. Dan haka ta adanasu sosai. Domin babbar hujja ce gare ta. Tana da tabbacin ta taro babban aikin da zai ɗaga hankalinta. Sai kuma yau ta tabbatar ya zama dole ta karanta littafin da Baba Barista ya ce ta duba.

*****

“Zuwa wannan lokacin ya kamata ace ka yi karatun ta nutsu Kamala ba rayuwarka ce kaɗai abar dubawa ba, idan tunaninka a baya na sa ido ne saboda gudun ruguza rayuwar Halimatu da Aufana, ya kamata ka sani a yanzu babu wanzuwar Halimatu kuma Aufana ta kawo ƙarfi za ta iya kare rayuwarta dole ka zaɓi abu ɗaya!”

“Abdallah kana ba ni mamaki wai mene ne haɗin kifi da kaska  ne? Dola ne sai na yi rayuwa yadda kake so? Ka bar ni mana!”

“Ina mamakinka Kamala, ganin zumar wani, sai ta sa ka watsar da maɗacinka? Hakan gangancin gangan ne, domin dai su kayan aro har kullum ba sa rufe katara!”

“Eh! Da muguwar rawa ai gwamma ƙin tashi!”

“Haka ka ce?”

“Ba ce wa na yi ba, ai a aika ce nake yin komai Abdallah, rayuwata rayuwata ce!”

Da sauri ta bar bakin ƙofar wanda hakan ya sanyata ture abin zuba shara, dukkansu a firgice suka kali wajen sai dai rashin ganin kowa bai ba su tabbaci na ba wanda ya ji su ba. Kallon kallo suka yi kowa da abin da zuciyarsa take kitsawa.

*****

(Ɗaka cillum waje cillum marka-markar damuna)

“Ba ƙoƙarina in tursasaka ba amma ka sani wannan shi ne abin da ya kamaci duk ɗan ƙasa nagari, kuma mutumin da yake iƙirarin yana kishin al’ummasa da kuma jaharsa. Kada ka manta babu shukar da za ta fitar da yabanya mai fari matuƙar ta samu wadatuwar taki. Samun rayuwa ta gari tamkar samun ƙorama ne a cikin daji ba kowane yake da wannan sa’ar ba.”

Furucin Barrister Abdallah ne yake ta yi masa kuwa a kunne. Ya sani sarai yana cikin tsaka mai wuya sai dai hakan ba ya nufin ya juyawa muradin barrister ɗin baya. Babban tashin hankalinsa shi ne rayuwar Aufana ba ya so ya rasata kamar yadda ya rasa mahaifiyarta.

Baya jin zai iya yafewa kansa in ya kuma yin kuskuren da zai taɓa rayuwar ɗayansu. Ba zai manta taɓon da kwatankwacin hakan ya ja masa ba yana ji ya na kuma gani rayuwarsa ta samu babban giɓin da har yau ya yi tafiyar burgu da farin cikinsa.

Ƙiri-ƙiri suka rasa mahaifiyarsu wadda ta zamo musu bangin jingina a rayuwarsu. Tabbas ya sani sakacinsa ne, amma bai yi tunanin rashin imanin Alhaji Labaran ya kai haka ba. Akwai abin da yake san haskawa Abdallah amma yaƙi fahimta.

 A karo na barkatai ya kai ɗaya hannunsa da ba dungulmi ba yana share ƙwallar da bai san ranar ƙarewarta ba.

 Kiran sallahr asuba ne ya fargar da shi tsawon lokacin da ya kwashe yana tunani, jikinsa a mace ya miƙe. Yana saka ƙafa ƙofar ɗakinsa ya hangi Aufana da fitila tana ƙoƙarin haɗa wasu takardu.

Murmushi ya suɓuce masa, baya raba ɗayan biyu file ɗin shari’ar Sadiya take haɗawa, yana son Aufana yana gudun abin da zai taɓata. Zai lamunci komai ban da taɓa martabarta wanda ya san kaɗan ne daga aikin Alhaji Labaran amma ya lura daga ita har Baban nata sun gaza fahimta.

Yanyin da ya hange ta sai ya tuna masa da mahaifiyarta Lantana, kamar wannan lokacin da ɗiyarta ke fafutukar nemawa wasu ‘yanci ita kuma a irin wannan lokacin tana fafutuka ne wajen abin da za su rufawa kansu asiri. Ya so a ce a lokacin ya yi amfani da zuciyarsa wajen kaucewa faɗawa ramin kurege amma ya gaza aikata hakan. Bai ankara ba zuciyarsa ta tafi tunani….

Halimatunsa jajjirtaciya ce, duk yadda yake kallon tsaurin zuciya irin na Aufana  ba ta kai mahaifiyarta ba matuƙar a kan gaskiya ne. Halimatu ba ta yadda da abata ba, duk ƙoƙarin da yake a kansu ta gwammace ta tashi ta nema da kanta. Ba ƙaramin ƙoƙarinta yake gani ba.

A baya yana ganin kamar ta rainawa ƙumajinsa ne, sai daga baya ya fahimci ba ƙaramin gata ta yi masa ba. Hasalima murna ya yi.  Ko banza ta sauƙaƙa masa zunuban tufatar da su da haram da kuma hidimar karatunsu.

 Gabaɗaya ita take ɗaukar ɗawainiyar karatun Aufana da ake biyawa kuɗin makaranta kowane zangon karatu naira dubu goma shabiyu. Duk da ya san akwai tallafin Abdallah amma shi ma lokacin ƙarfinsa bai wani kawo yadda zai wadata wani da kuma kansa ba.

Ba shi da bakin godiya ga Barista Abdallah domin shi ne tsanin komai, haka kuma ba shi da abin da zai biya shi sama da taya shi yaƙin cika muradinsa amma kuma ta yaya? Tunaninsa ne ya katse lokacin da ya lura Aufana ta kafe shi da idanu ta hasken wutar da aka kawo lokacin.

“Kawu lafiya kuwa?”

“Babu komai Halimatu Lantana….”

Da sauri ya gyara kalamansa,

“Babu komai Aufana ina kawai yabawa juriyarki ne.”

Da a baya ne ya yi wanna furucin murmushi ne zai suɓuce mata, amma a yanzu sai ta gaza jin hakan. Hasalima wani tashin hankali ne ya samu kai wa ƙwaƙwalwarta ziyara. Wasu lokutan hakan yake kiranta cikin suɓucewar tunani da sunan mahaifiyarta amma yau sai hakan ya yi mata zafi sosai ta alaƙanta hakan da jin hirarsu da Baba Barista, tabbas akwai abin da suke ɓoye mata.

Dama cike take da haushin ɓata lokaci da ta yi wajen duba file ɗin da Doctor Badamasi ya ba ta, wanda babu komi cikinsa sai shirme. Domin akwai bambanci sosai tsakaninsa da wanda ta samu a office ɗin ‘yan sanda.

Kawai ya raina mata hankali ne dan haka za ta nuna masa ita yarinya ce amma kuma mai tunanin manya. Domin hujojjin da ta samu a jiya daga bakin mahaifiyar Sadiya da kuma wasu ma’aikatan sun ishe ta kafa hujjar tuhuma.

A gefe guda yabawar Kawun nata ta sanya zuciyarta tattarewa ta curar da wani irin zargi da ba ta san yaushe ya soma tofuwa a cikinta ba.

Ratse shi ta yi ta wuce ba tare da ta tanka ba. Hakan kuma ya ɗaure jijiyoyinsa matuƙa. Baba Barista da ba su san da fitowarsa ba ya ja da baya, ya koma zuciyarsa na ba shi tabbacin akwai abin da Aufana ta fahimta ko ta ji.

Kai tsaye Kamala Alwala ya ɗauro ya fita zuwa masallacin da yake bayan layinsu. Wayarsa ce ta yi ƙara ya ɗaga.

“Akwai rakiya yau zuwa ɗaukar amarya, sai dai kuma amaryar na da tsada domin waɗanda suka biya sadakinta gwaraza ne.”

Tamkar saukar aradu haka kalaman suka duro cikin kunnuwansa. Bayan ya amsa wayar da duk bugunta tafiya yake da nutsuwa da hankalinsa. Cije leɓe ya yi tare da tattaro duk wata juriya da ta rage masa,

“Wa ya ɗaura auren?”

“Hamana ne!”

“Sadakin ya yi min ƙanƙanta domin Hamana hannun jariri ne da shi, bana tusa wajen da ba zan ɓata numfashi ba.”

“Kada ka ɓata rawarka da tsale Gundul….”

Ya yi ƙoƙarin tunzura shi ta hanyar kiran sunan da ya san ba ya muradi. Ai kuwa ya yi nasara domin cikin ci da zuci ya tare shi,

“Salis dakata mana….”

“Ɗan gari sai ka shirya”

Salisun ya faɗa da muryar dariya, bai kuma jira cewarsa ba ya katse kiran. Shiru ya yi yana tunanin yadda komai ya gudana a baya. Tun bayan wanzursu a ƙarƙashin kulawar ubangidansa gabaɗaya rayuwarsu ta samu giɓi.

Kamar ba zai aikata ba sai kuma ya sa hannu ya ciro waya daga aljuhunsa. Karawa ya yi a kunnansa, sai da ya tabbatar da mammalakinta ne ya ɗauka sannan ya soma magana.

“A yau akuyar da aka himmatu wajen ba ta dusa ba tare da ruwa ba, ta ɗauki ɗamar shan ruwa domin samun ‘yancin rayuwa ko da zai zame mata shan iskar numfasawarta ta ƙarshe….”

Ɗan jima aka yi daga ɗaya ɓangaren, daga bisani kuma aka furta

“Da kyau yaya Kamalan Lantana sai dai wani hanzari ba gudu ba, ita akuyar ta himmatu wajen aiki da ɗingishin kwaɗo dumin kogin da za ta je shan ruwan akwai kadojin da suke farautarta.”

“Matuƙar zan zamo kariya ga rayuwar Aufana to kowa ma ya rasa!”

*****

Yau da wuri ta fita wajen aiki. Tun fitowarta daga gida ta lura kamar ana binta a baya amma kuma da ta juyo sai ta ga kamar babu kowa. Take zuciyarta ta soma rawa, ta ji ba ta kyauta ba saboda zargin da take da shi kan kawunta da Babanta ya hanata tsayawa su fita tare.

Dan haka sai ta soma jan addu’o’in da duk suka  zo bakinta. Tana shirin tsaida abin hawa ta ji tsayuwar mutum a bayanta kafin ta yi wani yunƙuri an shaƙamata wani abu ta baya wanda a yanayin aikinta kai tsaye ta fahimci ko mene ne. Tana ji tana gani suka buɗe mota suka jefa ta a ciki amma ta kasa kataɓus.

Daidai lokacin ta hango motar Baba Barista kuma da alama ya ga abin da ya faru dan wajen ya nufo da matsananci tuƙi amma kafin ya ƙaraso sun ja motar. Yana ƙarasowa ya fito da sauri, idanunsa na kan lambar motar har suka ƙule take ya fito da waya ya dana kira,

“Mota mai lamba 373465 ina so ka bincika min mallakin waye kafin na ƙarasa office.”

Yana katsewa ya sake danna wani kiran,

“Idan saboda rayuwar Aufana kake wa Alhaji Labaran aiki yau ya zama dole kabari. Akan idona aka ɗauki Aufana ta hanyar sheƙa mata abu wanda ina da tabbacin Alhaji Labaran ne batun ya yi maka barazana da ita kuma ya kau a yau.”

“Abdallah me kake son faɗa mini?”

“Da Hausa na yi maka magana ai.”

Bai saurari cewarsa ba ya katse kirana, jikinsa a matuƙar mace yake tuƙa motar zuwa office. Ya tabbatar dama akwai zuwan wannan ranar amma bai tsammaci zuwanta nan kusa ba. Alhaji Labaran zai iya yin komai dan ɓoye abin da zai taɓa giyar mulkinsa. Lokacin da iya office abin da ya buƙata ya iso, sai da zuciyarsa ta doka ganin wanda aka nuna yana da mallakin motar,

“Kamala?”

To me hakan yake nufi? Kansa ya ɗaure matuƙa tuni zuciyarsa ta soma bugawa….

*****

Gudu yake da motar kamar zai ta shi sama, ga wanda yake da tazara tsakaninsa da shi zai yi mamaki idan aka ce me hannu ɗaya ne yake shara wannan gudu. Kwazazzabai yake wucewa tare da bi takan duk wani rami da ya nemi kawo masa tasgaro cikin tafiyarsa.

Ya samu kamar mintuna talatin yana hakan ya samu gangarawa tsakanin wata hanya da ta kasance tsukakkiya kuma me duhuwa. Babu abin da yake tashi sai kukan tsuntsaye waɗanda sautinsu ya haɗu da duhuwar wajen ya haifar da wani yanayi mai kama da ban tsoro. Bayan kulle motar ya fito ya soma taku cike da sassarfa, tafiyar mintuna huɗu ce ta sada shi da wajen da yake muradin zuwa.

“Tunmin har na iso bana buƙatar ɓata lokaci. Matuƙar aure ya ɗauru kusaka mini amarya cikin mota na ɗaware.”

Ya furta babu alamun fara’a,

“Kai ƙaramin ƙwaro ne, amma dai kasan kowace amarya na buƙatar lalle ko?”

“Ba damuwata ba ce.”

Gira na kusa da shi ya ɗaga masa, ya girgiza kai,

“Oga kana taka mana burki a kan wannan Gundul ɗin me zai iya wai? Ka barni na nuna masa bambancinmu?”

Ya furta yana nufoshi gadan-gadan, tunaninsa ya ba shi zai yi nasara kansa sai dai kafin ta ƙaraso ya yi wata irin alkafura ya sa ƙafa ya daki ƙirjinsa. Take ya zube a wajan sumamme. Babu shiri sauran suka yi kansa, take ogan ya daka musu tsawa tare da umartarsu da su salame shi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka soma loda masa kaya, suna yi suna ƙunƙuni.

Da idanu yake bin su, yana mamakin lallacewar da tazo wa al’ummarsu. Gabaɗayansu matasa ne masu jini a jika amma kuma rayuwarsu ta gurɓace. Wani abu mai ɗaci ya haɗiya da ya tuna dukkansu suna ƙarƙashin ikon azzalumin duniyarsa, tabbas ya kamata ya yi wani abu ko dan goban ƙasarsa. Idanunsu ya faka ya jefa wayar da Barista Abdallah ya ba shi a wani saƙo na wajen tare da turɓuɗe ta da ƙasa wadda ya tabbatar da a kunne take.

Bayan komai ya kammala ya janyo mota ya fito zuciyarsa fal farin ciki. Bai damu da yadda al’ammura za su rikice ba, domin ya haƙiƙance bayan wuya sai daɗi. Amma tabbas zai ɓarar da garin kowa domin kare martabar Aufana amanarsa.

*****

Kamar an jeho shi ya faɗo cikin office ɗin, duk da kasancewarsa amintacensu sai da hakan ya tunzura Alhaji Labaran ya miƙe a fusace,

“Salisu ba ka da hankali, ba ka ga muna tattaunawa mai muhimmanci ba ne zaka shigo….”

“Kamawa take a ɗaure mai ɗaurewa yallaɓai. In ka ga kwarto na ƙoƙarin saka wando yayin tara-tara ya san me ya taka.”

“Bana san wani zaurance ka fito a mutum ka yi min magana nan duk babu bare!”

“An yanka ta tashi!”

“Ban gane ba?”

Ya faɗa yana ƙanƙance idanu, numfashi ya ja kamar wanda ya yi gudun famfalaƙi gabaɗaya rigarsa ta jiƙe da gumi,

“Ma ɗaura auren da suka sako amarya a mota ne suka shiga hannu a ƙoƙarinsu na ƙwatar amaryar daga hannun kwarrata.”

Ɗabas! Alhaji Labaran ya zauna ba tare da ya shirya ba, yayin da sauran suka miƙe, wasu na tambayar garin yaya wasu kuma na fifita da rigunansu. Kamar an mintsine shi ya miƙe yana huci,

“Ina uban amaryar?”

“Abin mamaki ya kai amaryar ɗakinta, ba tare da ƙwarzane ba!”

“Ina Salisu akwai lauje cikin naɗi, ni Gundul zai yaudara, wallahi ƙarya yake yi, ba a haife shi ba matuƙarina raye ko yaƙi ko ya so dole zai tabbata a ƙarƙashin yi min bauta.”

“Yallaɓai a dai duba ba lallai abin da muke tunani ba ne.”

A fusace ya buga riga ya fita, nan da nan ɗakin ya koma babu kowa sai Salisu da yake tufka da warwara. Ko kaɗan tunaninsa bai ba shi Kamala zai yi wani abu ba, dan haka a wannan gaɓar yana jin ba zai juri dakon ɗaukar wannan zunubin ba.

Sai dai abin da ya ji suna tattaunawa kafin shigowarsa ya yi matuƙar ɗaukar hankalinsa. Magana ya ji suna yi kan ‘yan makaranta amma bai fahimci ainihin abin da ake magana kai ba, ‘ ‘yan maranta, fansa’ su ne abin da yake ta nanatawa amma ya kasa haɗa kalmomin yadda suka dace. Ko da ya fito bai samu Alhajin ba kai tsaye ya hau machine ɗinsa ya nufi gida.

*****

“Yaya Kamalu aikinka ya yi kyau matuƙa, mun yi nasarar kama su ta hanyar amfani da wayar da ka ajiye amma kuma wani hanzari. Ina tsoron lamarin ƙasar nan musamman abin da ya shafi jami’an tsaro. Sai ka ƙara taka tsan-tsan domin yanzu Alhaji Labaran a kanka zai dasa ayar tambaya, babu wanda ya san wajen in ba kai ba, kuma bai taɓa aiken wani saɓanin kai ba, dan haka yanzu dabara ta ragewa mai shiga rijiya. Kamar yadda Alhaji Labaran yake amfani da takardun rashin lafiyarka kan muradansa dole mu ma za mu yi hakan. Za ka kwanta rashin lafiya ta sati biyu daga yanzu da nake magana”

“Abdallah ya kake mini magana kan in kwanta bayan Aufana na hannun maƙiya? Barrister ni fa na ƙone, babu dalilin ƙirƙirar rashin lafiya bayan ina cikin hankalina, wadda nake fama da ita ma ina fatan samun sassauci daga Ubangiji”

“Ba za ka fahimta ba, amma akwai amfanin yin hakan yanzu haka lambar motar da aka sace Aufana a ciki dana tsananta bincike takardunta sun fito da sunan shaidair kai ne mammalakinta. Idan muka ce za mu sanar da hukuma to kai ne za ka zama abin tuhuma a kan ɓatanta. Wani abu ma da ba ka sani ba, motar da a ka tsinci gawar Sadiya ita ma kai ne mammalakinta a takardun shaida shi ya sa Aufana ta soma zarginka. Wanda ina da tabbacin Alhaji Labaran shi ya tsara hakan.”

Gumi ne ya soma keto masa ta ko’ina,

“Lalai sai ka yi taka tsantsan idan kuma akwai abin da kake ɓoye mini ka yi gaggawar sanar da ni.”

“Abdallah kada ka ce min zargin….”

“Kamala kowa zai iya zama abin zargi a batu na shari’a ko da kuwa asalin mahaifin Aufana ne….”

“Ban fahimta ba?”

“Ba za ka fahimta ba sai mun je ƙarshen game ɗin.”

Ƙarar da wayarsa ta yi ne ya katse musu hanzari, kallon kallo suka yi gabaɗayansu ganin mai kiran,

“Kada ka ɗaga.”

“Idan ban ɗaga ba zarginsa zai tabbata a kaina. Na fi so mu yi masa tafiyar hawainiya cike da ɗingishin kwaɗo kafin ya farga mun yi wuf da shi.” Kai ya ɗaga masa ba tare da ya yi magana ba, karsashin Kamala na wannan lokacin ya soma burge shi uwa-uba tawakkalinsa. Lallai sai ya ƙara zage damtse, domin ceto irin su Kamala babban jihadi ne.

<< Fitsarin Fako 8Fitsarin Fako 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×