Skip to content

Fitsarin Fako | Babi Na Biyu

4.7
(3)

<< Previous

Tsaka Mai Wuya

Koke-koken da nake ji shi ya farkar da ni daga dogon suman da na yi. A hankali na shiga bin kowa da ke gurin da kallo, har idanuna suka zo kan mahaifiyata da ke gefena a zaune, gefanta kuma Yaya Kamalu ne, amma in ba gizo idanuna ke yi min ba, babu hannu ɗaya a tare da shi.

Gabaɗaya Innarmu ta fita a hayyacinta saboda tsananin wahala da azaba. Dafe kaina na yi, domin ji na yi kamar ana sara min shi da gatari. Lokaci guda na ji komai yana dawo min cikin kwanyata, kamar yadda ake dawo da bidiyo baya idan ya ƙare.

“Ke nan rayuwarmu ba ta da daraja, rayuwarmu ba a bakin komai take ba. Sai yaushe za a dube mu, sai yaushe za a gane cewa muna cikin ƙuncin rayuwa, sai yaushe za a san muna buƙatar ɗauki, shin mu ba ‘yan ƙasa ba ne?”

Cikin kuka na ji wata mata na faɗin haka. Na tashi zaune, duk da ciwon da nake ji a jikina, musamman marata. Sai yanzu hankalina ya zo ga wannan wajen da muke zaune, wata irin dokawa na ji zuciyata ta yi. Mata ne ‘yan’uwana da yara ƙanana bila’adadin. Wasu na kuka, wasu kuma na kwance saboda wahalar gudun tseratar da rayuwarsu da suka sha.

“A haka shugabanninmu suke cewa suna tausayinmu?”

A hankali na kai dubana ga wannan matar da take magana. Sosai take rusa kuka, ɗanyen jaririn da ke hannunta babu riga a jikinsa, shi ya tabbatar min ko arba’in ba ta yi da haihuwa ba.

“An kashe mana mazaje, an hana mu rayuwa a muhallinmu, ‘ya’yanmu mata ana yi musu fyaɗe. Wannan wace irin rayuwa ce, wace irin ƙasa muke rayuwa a cikinta, wacce ba a tausaya wa talakawa?”

Cewar Innarmu da ta zama abar tausayi, hawayen idanunta sun gama ƙarewa, ga ta dai tana kuka, amma babu hawaye. Cikin raunanniyar muryarta, mai nuna alamun fidda tsammanin rayuwa, ta buɗi baki ta ci gaba da magana.

“Lantana sun kashe mana rayuwa, sun tattare dukiyarmu. Nan da kika gani jami’an tsaro ne suka je suka ɗaukomu a motocinsu, aka kawomu nan matsayin ‘yan gudun hijira. Domin ƙauyenmu ya zama tarihi, muna buƙatar a dube mu, mu ma ‘yan Adam ne!”

Tun muna jin abu a nesa, ga shi ya zo gare mu. Matuƙar ba a ɗauki mataki ba, haka za su ci gaba da kashe salihan bayi waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba! Daga waɗanda aka nakasa sai waɗanda aka tafi dasu.”

Ji na yi wani irin tashin hankali ya zo min. Ina so na yi kuka, amma na kasa, sai kawai na sunkuyar da kaina ƙasa, zuciyata tana tafasa, ƙwaƙwalwata kamar za ta tarwatse. Tabbas muna cikin uƙubar rayuwa, wadda ba mu san ranar ficewa daga cikinta ba, matuƙar shugabanninmu ba su waiwayi rayuwarmu, suka ji tausayinmu wajen ƙarfafa tsaro ba. To tabbas da alamu babu ranar da lamarin nan zai zo ƙarshe.

Idona ya sauka a kan Yayana wanda na kula da jinin daya bushe a ƙeyarsa da alama rauni ya ji, ga kuma hannunsa ɗaya da babu sai dungulmi. Hakan ya tabbatar min da cewa a gona ‘yan ta’adda suka riskesu kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda aka yi azaba ta hanyar cire hannu guda ɗaya.

*****

Kwanakinmu sun ja a sansanin ‘yan gudun hijira na cikin jaharmu, zuwa lokacin an samu damar kula da marasa lafiyar cikinmu. Sai dai kuma wata sabuwa, in ji ‘yan caca, gabaɗaya ba mu da sukuni, sakammakon yadda wasu ma’aikan suke ƙyamatarmu.

Wannan ya samo asali ne da wasu daga cikinmu suke fama da zazzafan zazzaɓi, ciwan kai da kuma atishawa akai-akai. Waɗanda aka samu tabbaci alama ce ta cutar sarkewar numfashi (corona virus) a kimiyance.

Wannan ya sa ko tsakaninmu ba mu da damar wata tattaunawa, domin an nesanta mu da juna. Yaya Kamalu dai ya tabbata mai hannu ɗaya, domin ‘yanta’adda sun yi nasarar raba shi da hannunsa na haggu a yunƙurinsa na guduwa.

Ina ɗaya daga cikin waɗanda suka samu kulawar da ta dace, sai dai sakammakon jigatar da na samu a cewar malaman jinya cikin da yake jikina ya samu girgiza, hakan ya sa suka ba ni tabbacin kwanakinsa za su iya komawa baya kafin haihuwarsa. A raina ban so haka ba lokacin da mahaifiyata ke karantamin,

“Innarmu dama ya zube.”

Shi ne abin da na furta amma ga mamakina sai na ga ta sauya fuska, cike da ɓacin rai take nunamin kuskuren furucina.

“Lantana kin isa ki ja da lamarin Ubangiji ne? Shin akwai wanda ya isa ya sauya ƙaddararsa ne?”

Jikina a matuƙar sanyaye nake bata haƙuri, sai dai kuma ƙasan zuciyata ina tunanin wace irin rayuwa abin da zan haifa zai fuskanta? Shin mace ce ko kuwa namiji ne? Ina burin ace namiji zan haifa domin yana da ƙumajin jure duk wata gwagwarmaya ta rayuwa. Wannan shi ne burina kuma duk lokacin dana ɗora goshina shi ne abinda nake roƙa.

Ranar da muka cika wata ɗaya ne muka sami baƙuncin wani shugaba daga jaharmu. A yadda nake ganin farin ciki a fuskokin ma’aikatan wajen na fahimci ko waye wannan, mutumin kirkin ne kuma me tausayi.

Ban tabbatar da hakan ba kuwa sai da ya iso, yadda ya dinga jan al’umma a jiki sai na ji soyuwar ɗabi’arsa a raina. Akan idona ya zaga ko’ina ya kuma ya raba kuɗi da abinci tare da bayani suna ƙoƙarin nema mana wajen zama na dindin. Da zai tafi ne na ga ya kira wani gefe sun yi ƙus-ƙus sai naga suna kallon Yaya Kamalu.

A raina nake jin Allah yasa taimaka masa zasu yi. Domin tunda muka zo sansanin Yaya Kamala ya zama kamar wani kwar-kwar da alama tashin hankalin da ya gani ya tafi da kaso mafi yawa na tunaninsa.

Cikin ikon Allah aka sama mana masauki, da yawanmu mun samu zama waje ɗaya wasu kuma sun nausa cikin gari. Ni da mahaifiyata da yayana muna muhali ɗaya. Sai kuma maƙotansu su Laraba me gasara. Kwanci tashi mun zama ‘yan gari. Haka muka kama sana’ar ƙosai da safe da rana kuma abinci domin rufawa kanmu asiri. A ɓangare ɗaya kuma ina rainon cikina amma kuma rabin zuciyata na tare da fargabar zuwansa duniya.

Yaya Kamala ya zama abin tausayi domin gaba ɗaya ba shi da walwala. In ka ganshi zaka samu ya zauna shi kaɗai, in ka kira sunansa zai amsa amma kuma daga nan sai ka yi magana goma be baka amsar guda ɗaya ba. Ganin halin da yake cikine ya sa muka soma yunƙurin neman taimako domin lafiyarsa.

Babu abinda ya faɗomin a rai sai bawan Allahn nan da ya zo ya dubamu a sansani. Zuciyata na faɗamin shi ne kaɗai zai iya taimaka mana. Amma kuma na rasa ta hanyar da zan nunawa Inna mu miƙa masa ƙoƙon bararmu.  Kwana na biyu ina jujjuya maganar a raina, ina san in tunkareta da maganar ina tunanin yadda za ta karɓi lamarin.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×