Skip to content
Part 1 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan littafi kacokan ga ɗana marigayi Abdallah Alhussain Abubakar, wanda ya rasu a ranar huɗu ga watan satumba 2021, tare da kakata Sa’adatu Usman Burran Matazu. Ubangiji ya jiƙansu tare da ɗaukacin musulmi baki ɗaya. Amin.

Tukuici

Wannan littafi tukuici ne ga ɗaukacin marubutan yanar gizo baki ɗaya, musamman Fikra Writers’ Association. Ina alfahari da ƙungiyata. Ubangiji ya ƙara mana haɗin kai da ƙaunar juna.

Alfaharina

Iyayena bani da sama da ku, ina matuƙar alfahari da jajjircewarku kan tarbiyata, Ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi. Haka kuma ‘yan uwana, MARWAKH, ina matuƙar sonku. Ubangiji ya ƙara haɗa kawunanmu ya tabbatar da junanmu kan turbar gaskiya.

Goro

Goro ne ga mijina, uban ‘ya’yana, Alhussain Abubakar. Allah Ubangiji ya ƙara mana fahimtar juna da ƙaunar juna. Ubangiji ya ƙara buɗa maka ta hanyar ciyar damu da kuma tufatar damu da gumin halak. Allah ya bamu ikon haƙuri da junanmu. Amin.

Kuna Raina

Maryam Idiris Katsina, Zakwan Salihu, Maijiddah Musa Muhammad, Rash Kardam, Ummu Nass, Ummu Samhat, Teemah Cool, Sainah Kt, Kamala Minna, Muttaka A Hassan, Barrister Jibrin, Avva Yhero, Maman Jeedah, Uncle Haruna, Aisha Sani Abdullahi, Sa’adatu Babba Kaita, Surayya Musa Maman Areef, Halima Suleiman Maman Abba, Anti Fiddausi Maman Khairat, Hauwa’u Na gambo Anti Lami, Aisha Maimota, Aisha Sani Gadanya, Abu Hisham Ƙarami, Kabiru Yusuf Anka, Sumayya Tijjani Nasir, Hindatu Mustapha Sani, Dr Sumayya

*****

Madubi

Da idanu ya ƙure file ɗin kamar shi ne zai ba shi amsar da yake buƙata. So yake ya tabbatar da zarginsa amma wani ɓangare na zuciyarsa ya ƙi ba shi damar hakan. Tun ba yau ba yake ɗora zarginsa a kan Kamala. Hatta rasuwar Halimatu yana da alamomin tambaya da yawa a kansa, saboda. Yanayin yadda aka haɗa gawarta, rashin lafiyarta, da rashin sanarwa kowa har ta rasu. Amma kuma tunanin yin hakan tamkar yi wa bayan Halimatu adabo ne, yakan karyar masa da zuciya.

‘Me ya haɗa motar da aka tsinci gawa da tabbatuwar shaidar mallakar Kamala?’

Ya yi furucin a zuciyarsa, ganin kansa zai ɗauki ciwo ya sa ya tattare file ɗin ya ajiye,  alwala ya ɗauro tare da tayar da sallah. Ya jima yana kai wa Ubangiji kukansa, daga bisani ya miƙe ya ɗauki file ɗin ya buɗe durowa da niyyar saka shi. Idanunsa suka sauka a kan muhimmin littafin rayuwarta (diary). Wata ƙwalla ya ji tana taruwa a gurbin idanunsa, yayin da kalamanta suka shiga dawo masa tiryan-tiryan.

“Yaya Barista ina so in shiga makaranta bayan na yaye Aufana. Ina muradin in rubuta tarihin ƙauyanmu da hannuna.”

“Halimatu ki ba ni labarin zan rubuta miki, ni tamkar bawa ne ga rayuwarki.”

“Duk yadda za ka rubuta ba kamar ni da abin ya shafe ni ba, zan yi rubutu ne cike da taɓuwar zuciya tare da tayar da mikin da har na koma ga ubangijina ba zai sami cikewa ba!”

“Halimatu..!”

“Dan Allah Abban Aufana…!”

Hawayen da ya gangaro masa ne ya katse masa tunaninsa, sai yau ya sake tabbatar da, tamkar saboda shi ta yi rubutun lokuta da dama ya kan gwammace   ya karanta labarinta duk da ba ya gamawa ba tare da ciwon kai ba. Tissue kuwa be san adadin da yake ƙararwa ba.

Ji ya yi yana son sake karanta labarin kamar hakan zai iya ba shi buɗewar ƙofofin da suka rufe a cikin kansa. A hankali ya buɗe shafin farkon, idanunsa ya sauka kan rubutun.

*****

“Kalmar ƙaddara wata kalma ce da ta ƙunshi tarin ma’anoni da yawa ta fuskar kyawu, da kuma akasinta. Kalmar na da nauyi ga wasu mutanen, yayin da take sakayau ga waɗansu, musamman waɗanda tauhidi ya zagaye rayuwarsu. Kuma suka yi imani, kyakkyawa da mummuna duka Ubangiji ne yake wanzar da su ga rayuwarmu, saboda su kasance jarrabi.

Zaren ƙaddarar wasu mutanan yana da tsayi, wasu kuma nasu gajere ne amma yana da kaurin da ba su da ƙumajin kokawa da shi. Shi ya sa akasari suke sarewa tun kafin su kai ga gaci. Wasu kuma sukan iya arar juriya su yafa, wajen nacin daddana sandarsu domin miƙewarta. Kamar haka ne ya kasance ga tauraruwa me wutsiyar da ta ke to cikin duniyarmu.

Mun soma rayuwa ne da tashi sama da fuka-fukan da ƙaddarar rayuwarmu ta mallaka mana. Kamar yadda al’amarin ya soma a wata safiya mai cukurkuɗaɗɗan yanayi.

Garin Namuyasamu ɗan ƙaramin gari ne da ke cikin jahar Zamfara. Allah ya albarkace mu da albarkar noma da kiwo, akasarin mazauna garin zuwau ne hakan ya sa a lokacin na damuna irin na wannan safiyar ba kasafai mazauna garin suke zaune ba. Da yawansu sun fantsama gonakinsu domin kasancewar ruwa da aka kwana ana yi a daren ranar.

Hakan ce ta kasance gareni, ni Halimatu Labaran, wacce aka fi sani da Lantana. Ina ta shiri domin leƙa gonarmu sai dai hakan ya gagareni. Kasancewar na tashi babu cikakiyar lafiya ya sa Yayana Kamalu wanda idan na so tsokana nake kiransa Kamala, umartata da in zauna a gida, shi zai kula da gonarmu. Ba haka na so ba, saboda mahaifiyarmu ma tana gida sakammakon tsanantar jikin mahaifinmu. Ina zaune na rafka tagumi da hannuwa biy-biyu ina tunanin rayuwarmu.

A yanayin da nake ciki, kallo ɗaya za ka yi min ka fuskanci wani abu na mintsinin tsokar da take tsakanin awazuna. Lokaci zuwa lokaci nakan ɗan kali gefena ba komai nake tunawa ba sai halin ɗar-ɗar ɗin da muke ciki sakammakon yau kwanaki uku ke nan muna samun saƙon ‘yan ta’adda na shigowa ƙauyanmu.

Hakan ba wai sabon abu bane, domin wannan shi ne karo kusan na uku, shigowarsu ta farko ita ce shigowar da ta bar min taɓon da har numfasawata ta ƙarshe ba zan manta ba. Sun shiga ƙauyen da aka kai ni ne a daren aurena, wanda yake maƙotaka da namu. Sai shigowarsu ta biyu, sun shiga ƙauyen gabanmu. Garinmu ne kaɗai Allah yake tsare shi ba su taɓa yunƙurin shiga ba sai a wannan gaɓar da suka saka mu cikin taradaddin zuwansu.

Kusan hakan ya zama jiki ne gare mu yadda ‘yan ta’adda suke wadaƙa da ƙauyukan jaharmu kamar zaki a filin faraunta. Daga wannan gari sai wannan gari, abin ya zame mana kamar zaman marina.
Tun da muka samu labari hankalinmu ya yi mugun tashi. Su yaya Kamalu sun yi iya ƙoƙarinsu kan maigari ya aikawa hukumar ‘yan sandan cikin gari labari, amma ya turje ya kuma shawafa idanunsa kwalin Audu saboda gargaɗin da suka aiko game da hakan. Hasalima, sun tabbatar suna da mutane a cikin ƙauyen da suke aika musu da rahoto a kan komai. Hakan ya sa suka zame mana kabewar kan kabari ko kuma na ce gaba kura baya siyaki.

Kwatsam muna cikin wannan taradadin kuma, sai ga wata masifar, wato watsuwar cuta mai sarƙe numfashi. Yadda muke jin labarin a gidan rediyo ya ɗaga hankulanmu. Musamman kasancewar garinmu na ɗaya daga cikin garuruwan da suke da ma’abota fita da kaya zuwa wasu garuruwan, sai zaman ɗar-ɗar ɗin da muke ciki ya ƙaru domin samun haurowar makusantanmu daga garuruwan da aka killace ta ɓarauniyar hanya.

Yayana Kamalu wanda nake kira da Kamala tun baya san sunan har ya soma binsa. Akasari mutanan karkararmu sun fi kiransa da Kamala. Ana jimawa kafin a sami me faɗar asalin sunansa na Kamalu. Tun yana masifa har ya zamana yana amsawa da duk ɗaya daga cikin wanda aka kirashin a cewarsa sunan ‘yan gayu ne. Shi ma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka dawo gida, tun dawowarsa nake fama da shi kan ya killace kansa kamar yadda na ji a rediyo suna bayani, amma ƙarshe da faɗa muke rabuwa. Innarmu da za ta tsawatar masa ita ce take min faɗa kan ina ƙyamatar ɗan uwana.

“Lantana kina ba ni mamaki, ke wa ya ƙyamace ki lokacin da taki ƙaddarar ta soma?”

Wannan shi ne furucin da ya kulle bakina, ina ji ina gani Yayana na fama da zazzaɓi da mura amma an hanani yin abin da ya kamata. Ban manta yadda muka ƙare da shi da safe ba kafin ya tafi gona.

“Yaya Kamalu…”

“Da magana ne sarkin surutu? Yau kuma kin ga dama kin kira asalin sunan ne?”

“Kowane na faɗa maka ciki, ai dai ma’anar ɗaya ce ko?”

“Wa ya sa ni abu a duhu ni sanar da ni buƙatarki in sa gabana gabas.”

Sai da na ɗan yi waige-waige kamar bana so wani ya ji sannan na furta,

“Yanzu ba za ka samu ka sayi abin kare kanka daga wannan annobar ba?”

“Kin ga Lantana, ki rufe mini baki, waya faɗa miki wannan cutar gaskiya ce? Duk fa bogi ne ake yi wa mutane”

“Ka daina yadda da jita-jita, ko ƙarya ne ko gaskiya ne ya kamata ka kare kanka saboda lafiya ta fi komai, ga shi ka ɗaura, ranar kasuwa ne na aika Manu ya siyo mana a cikin gari”.

“Ni ba zan ɗaura ba, wa kika fi jin rediyo? Ai ni ma ɗazu da safe na ji da kunnena kan cewar; masana ilmin ƙwayoyin cuta na shakku game da tasirin takunkumin kariyar ga kamuwa da cututtukan da ke yaɗuwa ta iska….”

“Ban tari numfashinka ba. Amma akwai bayanai da ke nuna cewa sanya takunkumin kariyar zai iya taimakawa wajen rage yaɗa cutar. Na ji yawan sa takunkumin kariyar da jama’a ke yi ba hanya ba ce ta kariya daga ƙwayoyin cuta ko ƙwayoyin cuta da ke yaɗuwa ta iska, wanda ta haka ne ake yaɗa ƙwayoyin cuta saboda sun kasance ba su da abin tace iska kuma idanu a waje.

Amma za su iya taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da ƙwayar cuta ta hanyar atishawa ko tari tare da samar da kariya ga yaɗuwar cutar daga hannu zuwa baki. Rufe baki a lokacin atishawa da wanke hannaye sannan kaucewa kai hannu baki kafin wanke su zai iya taimakawa wajen rage kamuwa da wata ƙwayar cuta ta numfashi.

Hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya ta Birtaniya NHS ta ce hanyoyin kare kai daga kamuwa da ƙwayoyin cuta su ne: Wanke hannu akai-akai da ruwan ɗumi da sabulu. Kaucewa taɓa idanu da hanci. Yawan tsafta da zama cikin tsaftataccen muhalli.”

Kallon uku kwabo ya watsa mini kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya karɓa ya ɗaura.

“Ke da haihuwar birni ce da ruwa ma sai kin hana mutum sha saboda ƙa’ida.”

“Na ji koma me za ka ce ni dai burina ka kula da kanka.”

“To Halimatu, Lantana ‘yar baba. Ni zan tafi amma kada ki sake ki fita ko’ina kin ga Inna yanzu za ta je karɓowa Baba magani, ki kula tun da kin ga a yanayin da garin yake ciki.”

“In shaa Allahu, Ubangiji ya kiyaye hanya. Manu ma da ya shigo ba zan bari ya je ko’ina ba.”

Tunanina ne ya katse sakammakon jin ihu kamar na muryar mahaifiyarmu, na sake kasa kunne tare da ƙoƙarin yunƙurawa ina cije leɓe saboda nauyin da cikina ya yi mini. Kamar an ƙara sautin kuwa haka ya ratso kunnena.

“Wayyo Allah!”

Muryar mahaifiyata na jiyo cikin kuka, a razane na nufo tsakar gida, ina faman haɗa hanya saboda rashin ƙwarin jiki. Ina fitowa na ganta yashe a ƙasa rungume da ƙanina Manu cikin jini, kamar an yanka wata babbar dabba. Ban san lokacin da na zuɓe ƙasa dirshan ba. Ji na yi gaba ɗaya duniyar tana juyawa, saboda tsananin tashin hankali.

“Sun kashe min ɗana…”

Sautin muryarta ce ta dawo da ni cikin hayyacina. Take na ji ƙarfi ya zo mini, na rarrafa na ƙarasa wajen da suke ina kallonsu. Don na kasa gasgata abin da nake gani.

Hannu na kai ina shafar fuskarsa cike da tsoro, wani sanyi na ji ya bi sassan jikina, ban san lokacin da na zabura a guje na nufi inda randa take ba. Ruwa na ɗebo cikin moɗa, na zo ina sheƙa masa, amma ina! Tuni rai ya yi halinsa, na rasa rai biyu cikin ƙanƙanin lokaci.

Wasu hawaye masu zafi na ji sun shiga wanke min fuska, ban hana su zuba ba, sai ma komawa gefe da na yi ina faman ambatar hasbunallahu wani’imal wakil. Ƙirjina kamar zai buɗe, yayin da ƙafaffuna suke rawar da suka tilasta min zama a wajen.

Ban san tsawon mintuna nawa na kwashe a zaune a wajen ba, ina faman lissafin yadda rayuwa take zuwar min a baibai.

A daren aurena ‘yan ta’adda suka fasa taron ‘yan kawo amarya suka yi min fyaɗe a gaban idanun mijina, sannan suka kashe shi suka yi gaba damu. Ƙwaƙwalwata ba zata iya tunawa da wahalar da muka sha a hannunsu ba. Sun azabar da mu ta hanyar duka, horon yunwa da kuma ƙishi kafin ubangiji ya yi ikonsa muka kuɓuta daga gare su.

Bayan sun kashe na kashewa sun tarkatamu mun ɗauki hanyar barin ƙauyen, abin tausayi yara duk sun fi yawa ga kuma mata masu juna biyu, sai kuma matan da aka zallunta irina waɗanda da ƙyar suke ɗaga ƙafa.

Amma haka suke koramu kamar shanu babu tausayi balle imani. Koda muka nausa daji ma, ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da dattijai da kuma ‘yanmata ba. Babu tausayi babu ɗigon imani a tare da su. Wadanda suka kasa jurar tafiya kuwa sai su jefa su a ruwa ko kuma sai mun je wajen da suke da tabbacin za a samu abin cutarwa sai a tafi a bar su a nan. Haka muka rika nausawa daji abin tausayi.

Cikin ikon Allah muka sami nasarar ƙwacewa a lokacin da baccin asara ya kama su. Allah Ya ba mu sa’a muka gudu, ƙayoyin da suka shiga cikin ƙafaffunmu wajen gudu Allah kaɗai ya san iyakarsu. Ga yunwa ga kuma ƙishi; ganye shi ne abincinmu, yayin da kogo ya zama makwancinmu.

A haka muka ƙaraso garinmu da waɗanda suka biyo ni a zuwan ‘yan gudun hijira. Tun dawowata ba ni da walwala, ga baƙin ciki halin da na samu kaina  ga kuma fargabar rashin tsaro. Domin sai da ta kai ta kawo an daina noma a wajen gari, kuna tsaka da aiki za a kamaku a kashe ko kuma a yanka. Idan ba a same ku ba kuma za a lallata amfanin gonar ko a kunna masa wuta. Ko kuma idan sun sameku kuna noma su ƙona amfanin noman su yayyanke muku hannuwa su zuba cikin aljihu su koroku. Waɗanda suke da kwana a gaba, haka suke komawa masu dungulmi. Waɗanda kuma kwana ya ƙare take azaba ke sa su baƙunci lahira.

Watana biyu a gida, cikin wannan mummunan yanayin, ciki ya bayyana a jikina. Wannan shi ya ƙara rushe ragowar nutsuwar zucin da nake da ita, na rasa ina zan sa kaina. A sanadin bayyanar cikin da ke jikina, mahaifina zuciyarsa ta samu raunin ɗaukar halin da nake ciki, dama ga hawan jini. Sanadin haka ya kamu da cutar shanyewar ɓarin jiki. Sai dai a kwantar, a tayar.

Wannan ya ƙara sanya mu cikin damuwa, abinci kansa ya soma gagararmu. Dama ba wata sana’a mai ƙarfi mahaifinmu yake yi ba tun bayan karayar arziƙinsa. Dole Yaya Kamalu ya soma fita fatauci duk da mahaifinmu ba ya so.

A haka muke samun ɗan abin sakawa a bakinmu da taimakon ƙosai da mahaifiyarmu take soyawa Manu yana fita da shi. Mun zama ababen tausayi, babban jigon rayuwarmu ya samu tawaya. Yau kuma ga Manu an kashe shi, ban kuma san a halin da Yayana yake ciki ba.

‘Wayyo Rayuwa’

Abin da nake ta nanatawa ke nan a zuciyata, yayin da nake kallon Innarmu da ta gama ficewa daga hayyacinta, numfashinta sai ƙasa yake yi yana sama, saboda tsabar kukan da ta sha.

‘Ita ma za ki iya rasa ta idan ba ki yunƙura ba.’

Na ji wani sashi na zuciyata yana sanar da ni haka. Ban san lokacin da na miƙe na nufi inda take rungume da gawar Manu ba. Amma kafin na isa wurin, na ji wani sauti mai ƙarfi da barazanar tarwatsa kunnuwa. Jikina ya shiga karkarwa kamar an jona min wutar lantaki, na toshe kunnuwana, lokaci guda na ji komai ya canja. Ina ƙoƙarin saita nutsuwata, na ji sautin gudun mutane daga bayan gidanmu, wannan shi ya tabbatar min komai ya zo ƙarshe. Don irin haka ce ta faru da ni a gidan mijina, wato dai ‘yanta’adda ne a ƙauyenmu.

Ashe da gaske za su zo ɗin kamar yadda suka faɗa? Me ya sa maigari yaƙi yadda da shawarar su Yaya Kamalu?

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!”

Abin da zuciyata take ta faɗi ke nan. Kafin na saita kaina, na ji dirar mutane a tsakar gidanmu. Da idanu na shiga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, kowannensu baƙaƙen kaya ne a jikinsa, fuskarsu rufe da hirami, jajayen idanuwansu kawai nake iya hangowa masu ɗauke da tsantsar rashin imani. Na kasa ɗauke idanuna daga kansu, har suka ƙaraso gabana.

“Ina mazajen gidan?”

Wani ya faɗa da kaurin murya yana zare min ido.

‘Baba da ba shi da lafiya’ wani sashi na zuciyata ya tunamin.

“Mahaifina, yayana!”

Bakina ya furta ba zato ba tsammani. Da sauri na juya ina kallonsu, ai kuwa cikin ɗakin da yake kwance tsawon watanni huɗu suka nufa. Ban san lokacin da na kwasa da guda na nufe su ba. Na ma manta da wani nauyi da rashin ƙwarin jiki. Sai dai kafin na shiga cikin ɗakin, na ji an ɗaga ni sama an buga da ƙasa kamar bulo ya kufto daga hannun magini.

Zafi da zugin da nake ji a jikina, ba su sanya na sare ba. Da ƙyar na iya miƙewa, bakina yana fidda jini sakamakon haƙorina guda ɗaya da ya fita. Ɗakin na sake nufa ina rangaji, wani daga cikinsu ya finciki hijabin da ke jikina, ya wurga ni gefe guda kamar kayan wanki.

Ina ji ina gani suka shiga ɗakin, suka janyo mahaifina suka fito da shi. Ban da nishin azaba babu abin da yake yi, idanuwansa sun fito waje sosai, sun kaɗa sun yi jajir! Da sauri na kau da kaina gefe, don ba zan iya cigaba da kallonsa a wannan halin ba.

“Wayyo Allah Malam!”

Mahaifiyata ta faɗa da ƙarfi. Da sauri na dube ta, yanayin da take ciki shi ya ƙara ruɗa ni.

‘Ina ma a ce ina da ƙarfin da zan iya ceton iyayena?’ Abin da na faɗa ke nan a cikin zuciyata.

“Kar ku kashe min miji, na roke ku don Allah?”

Innarmu ta cigaba da faɗin haka cikin muryar kuka, yayin da take bin su ɗaya bayan ɗaya tana roƙonsu, amma ba wanda ya san tana yi, balle ya tausaya mata. Ni ma take na isa gabansu cikin azama na zube bisa gwiwoyina, idanuwana sai kwararar da hawaye suke.

“Don Allah ku yi mini rai, ku bar min iyayena…”

Cafkar da na ji an yi wa sumar kaina ce ta sanya na kasa ƙarasa maganar.

“Iyayenki kike buƙata, rayuwar iyayenki kike so?”

Na ji wanda ya cafke mini suma ya faɗa. Gyaɗa kai kawai na yi, don ba zan iya motsa bakina ba, saboda azabar da nake ji. Wata muguwar dariya ta rashin imani ya yi, wanda hakan ya yi silar zamewar shiramin fuskarsa. Da hanzari ya mayar amma kuma ya makara domin na ga fuskarsa kuma na shaidata.

Ɗauke kai na yi da hanzari, domin na tabbata matuƙar ya fuskanci na shaidashi sunana mataciyya. Murtuƙe fuska ya yi, ya ɗaga bindigarsa sama, ya ja kunamarta, kana ya ɗora bakinta a kan mahaifina. Kafin na buɗi baki na ce wani abu, jinin mahaifina ya wanke min fuska. Ina ganin haka, na yanke jiki na zube ƙasa wanwar!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Fitsarin Fako 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×