Ringing na wayata ne ya ankarar da ni, ban san lokaci ya ja har haka ba, karfe goma na dare, ni da tara nike barci a gida ma. Haleefa na gani a screen din wayata na dauka da sauri.
“Leefaaa” Na kira sunan shi.
Ya ce, “Ke nikam kar ki fasa mun kunne mana.”
Na ce, “Haba Leefa yanzu nake cewa zan kira ka, ka manta ni ba? Ko ka kira ka ji ya nake.”
Ya ce, “Kai Amnan Ammi kin cika mita ke kam to yanzu ba gashi na kira ba.”
Sai na ji hawaye yazo min na ce. . .