Skip to content
Part 3 of 6 in the Series Fudayl by Aysha I. Ahmad

“Its late, ki je ki kwanta.”

Na ji an fada wanda yayi sanadin dawowa ta daga duniyar tunani da na tafi mintuna kadan bayan wayana da Haleefa. Juyowa nayi naga miji na ne, ni ko sunan shi bazan ce na rike ba ma dan lokacin da duk ake fada har aka daura auren bana cikin natsuwa ta asali ma ko gidan ban zauna ba. Gidan Sitti na tafi.

Mikewa nayi kawai na wuce shi zuwa dakin da ya zama nawa tun da muka iso ya nuna mun, shirin barci nayi cike da kewa dan ni ban taba kwana ni kadai ba in dai gidanmu ne, ina tare da Ammi na, su Haleeefa ne ke da daki amma ni da hanan dakin Ammi muke kwana. Sai naji tsoro ya kama ni, nayi adduo’i na na hau gadon na kwanta. Ba zance ga lokacin da barci ya dauke ni ba sai kiran sallah da naji ta asuba, na yi salati tare da adduan tashi a barci na mike na shiga bandakin da ke cikin dakin dan yin alawla. Ina kara gode ma Allah da samun iyaye na kwarai dan bama rasa sallah na asuba da izinin Allah, tare muke tashi da Ammi sai dai wataran tana riga mu tashi dan ita sai ta farka tun uku na dare haka ta yi nafila kafin asuba.

Na fito ina shirin tayar da sallah na ji knocking a kofan dakin har na dan tsorata sai naji muryan shi yana ‘lokacin sallah yayi’ gyaran murya kawai nayi yasan na tashi bani son Magana ne ma kawai, ina jin fitan shi wanda nake tsamman masallaci ya je. Bayan na idar na zauna nayi azkar dina sannan na dauko alkurani na da yake karamar jaka ta na fara karatu har zuwa shida lokacin naga haske ya dan yi, na saba ban iya komawa barcin safe ba sai dai ko weekends amma in ba haka ba da na tashi akan sallaya kicin nake wucewa in mana breakfast. Yanzu tunani na in na fita mai zanyi, ko sanin inda kitchen din yake ma banyi ba na kuma ji shigowar shi ya wuce daki tunda kusa da wanda nake ciki ne shiyasa ma naji karar bude kofan. Na samu nutsuwa bayan karatun da nayi yanzun kuma na yanke shawaran yima shi biyayya ko da ba son shi nike ba amma saboda Abbu zan zauna da shi sai dai zan mishi magana kar ya tsammaci wani abu daga wajena yanzu kam dan ban shirya zaman aure da shi ba. Da wannan tunanin na kishingide bisa sallaya da nufin zuwa anjima in fita sai dai kuma barcin da ya dauke ni bai ban wannan damar ba.

Bude ido nayi sakamakon hasken rana da ya hudo cikin dakin nayi salati na sanar da ubangiji’yaushe gari ya waye haka? Lallai na sha barci ko da yake satin nan da ya wuce ban samu wani barci ba saboda hidima ga bani da natsuwa sai yanzu na sake tunawa da inda nike ba gidanmu bane sai naji hawaye kadan na share dai na mike naa shiga wanka ganin lokaci ya ja har takwas na safe. Ina fitowa na shafa mai na goga yar hoda akan mirror da man baki sannan na nufi akwati na da aka taho mun da shi in dau kaya. Na dauka na bude durowa din dakin in jera sauran kayana amma abun mamaki duk an jera mun wasu kayan ma, nace lallai su mama binta sun sha aiki da suka zo, dinkuna ne sabbi kuma wanda ina tsamman cikin na kayan auren ne aka dinko dan naga daya side na durowan akwai wasu zannuwa da baa dinke ba. Simple riga doguwa na dauko na atampa, ni ba maabociyar son dinkuna matsassu bane ba kuma nafi son simple style (mai sauki) a dinki. Sai yanzu da nike gyara dakin bayan na sa kaya sannan naga irin kyau da yayi masha Allah su Abbu sunyi kokari gaskiya duk da yanda akayi bikin nan cikin sauri amma a satin bikin su mama binta kanwar Ammi na suka zo suka shirya komai, wardrobe din da ke dakin babba ne mai kofa shida sai madubi da ke hannun dama in ka shigo dakin mai kyau da shi kuma babba, gadon da ke bangon gabar a dakin babba ne shima dan mutum uku na iya kwana a kai, ko na Ammi ma bai kaishi girma ba, kalar su kalar sky blue ne da fari. Na gyara shi tsaf tare da bargon da ke kai wanda ban tsammanin yana dakin ma shigowa na amma dai kam da babu shi zansha sanyi saboda AC din dakin mai bada sanyi ne sosai ma nike ga yana daga cikin abun da ya sani barci sosai dan nikam Allah ya sani bani son zafi ko kadan.

Bayan na gama da dakin na kunna turaren wuta babba na tsinke, ina son kamshi a rayuwa shiyasa Mama Binta bata fashin kawo mun turaruka indai zata zo. Ina son ta sosai, a Maiduguri take da zama da yaranta biyar duka mun saba da su kuma. A falon da na fito banji motsin kowa ba a raina na ce an kawo ni nan ni kadai, shi kuma kila ma yayi fitan shi dama ba damuwa yayi da ni ba.

“Abbu me yasa kamun haka ne’?

Na share dan guntun hawaye na na cigaba da kallon falon da girman shi ya isa ya nuna mun cewa wanda nake aure na da hali ba laifi, kujerun da nike tsamman wanda Abbu yamun ne sunyi kyau a falon sosai, kalar su blue ne da ratsin fari, ina son kalar blue amma na sararin sama (skyblue). TV din da ke manne a bangon falon babba ne shima irin plasma din nan na kamfanin Samsung sai wani tabir guntu mai hade da durowa kanana amma yana da tsayi, receiver ce a kai sai remote na shi da na TV din a gefe, sunyi kyau su ma duk sky blue da fari ne. ni dama ba mai son tarkacen jere bace shiyasa tsarin yamun kyau ba kadan ba. Yunwa kuma na fara ji sai na shiga neman inda kitchen ya ke.

Ban sha wata wahala ba dan jiya da muka iso naga kofar da ya shiga a cikin falon ba inda na fito yanzu bace wurin dakunan saboda haka ita naje na bude kamar glass ta ke sai da naje na lura tura ta ake amma baka ganin cikin ta glass din daga waje sosai sai da na shiga naga ko ya yake, dining room ne zan kira shi kawai tunda naga dining table a wurin mai guda takwas kuma na glass ne kewaye da wani irin katako mai kyau, sai yanzu na tuna na taba ganin irin shi a wani series na india (fina finan indiya), zanyi missing serials dina a Bollywood amma nasan nan gidan baza a rasa channel din ba. Na wuce ciki ina kara yaba kyan wurin duk da ba wani kato bane ba amma yamun kyau sosai, ina son dining room haka shiyasa ko a gida ma in dai ba Abbu na nan ba nafi son muci abinci a kai shikam Abbu yafi ganewa a sauko kasa sai ya ce yafi dadin ci.

Akwai durowa daga gefen tebir din da na bude sai naga farantai ne da kofuna na shayi, a kan tebir din kuma akwai kayan shayi din, madara, ovaltin, lipton da cornflakes, abun da bai dame ni ba kenan, su Hanan kam nason cornflakes, nayi kewar su da yanzu nurain na tare da ni a kicin din nan dan shi baya komawa barci shiyasa har in mai wanka duk da ma yace shi yanzu ya girma sai dai a wanke mai baya kawai,ammi tace bata yarda ba amma sai yace shi kam ya girma,toh kuma gaskiyar shi shekara bakwai kam mana ya girma,nayi dariya ni kadai da na tuna su,ko yanzu me suke yi? Sai Allah,yau kuma kila ammi ce zata mai wankan. Daga gefe kuma yar kofa ce bude da na leka sai naga kicin ne babba da yaji komai dangane da kayan aikin kicin,gaskiya tsarin wurin ya burge ni ba kadan ba.

Sai yanzu da na fito a kicin din na lura da plate a kan dining din na bude naga dankali ne chips aka soya da kwai a saman shi, na daga ne naga wata yar takarda a kasan na dauko na duba, rubutun ne ma yamun kyau farko na ce duk me rubutun nan ya iya gaskiya,

‘Da fatan kin tashi lafiya, ga breakfast nan, ni na fita’

Abun da na gani kenan a takardar nace shikenan ba wani kulawa ba magana mai dadi? Haba ai wannan shine rashin son, a nawa tunanin wanda ke son ka zai zama mai kula da kai sosai kuma ma in ban da ki jiya fa nazo gidan nan a matsayin amarya amma yasa kafa ya fita, ‘mtsw’na yi tsaki sai naji abincin ma ya fita a raina amma dai saboda yunwa zan ci, toh ma ko siyowa ya yi ban sani ba, nifa bani son abincin siyarwa shiyasa ma zan fada mai indai abinci ne kar ya damu zan girka.

<< Fudayl 2Fudayl 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×