Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Fudayl by Aysha I. Ahmad

‘Assalamu alaikum,’ na yi sallama ina shiga gida, dawowata kenan daga wurin karatu na komfuta (computer certificate), Nurain ne ya fito da gudu jin murya ta, ‘assalamu alaikum habibi’ ya amsa da ‘wa alaiku massalam aunt Amna’ yau kin dade, why? Ya tambayeni.

Na ce, “Yalla habibi zan fada ma later, na gaji yanzu, get me something cold fast’ yace right away habibti’ ya tafi da gudun shi, ina son dan kanin nan nawa, sai lokacin na karasa shiga falon ina ‘wai nak Ammi? Assalamu alaikum, na ce mata ina zama a nan kasa kusa da kafanta, shafo kaina tayi ‘wa alaiku massalam, kin dawo kin biye ma Nurain baki nemi niba ai da.

Na ce, ‘Afuwan Ammi na shi na fara gani daga shigowa ta, ina Hanan kuwa?’ Ta ce taje hado ma bako ruwa, sai lokacin na kalla falon ashe Ammi ba ita kadai bane, kyakkyawan mutum na gani a zaune a carpet din falon daga gefe, duk inda ake neman namiji mai kyau ya kai, yana sanye da farar shadda da ta sha aikin blue da hula a kan shi ita ma blue, masha Allah na fada a zuciya ta, sallaman Hanan ne ya katse ni ta ajiye mai tray na ruwa da lemo hade da sambosa a dish.

Wurina ta taho tana ‘welcome back aunt Amna yau kin jima’ na ce “Oh Hanan am will you say salam at least, na hana ki magana haka without a salam amma la baki ji, ta ce afuwan ukhty barin sake ba, duk da larabci muke maganan saboda bani so bakon nan ya ji me muke cewa, ‘yanzu ke ma ai baki gaida bakon ba Amna am kin biye ma Hanan, hakuri na bama Ammi sannan na juya na kalle shi ‘Assalamu alaikum, how are you?’, Ammi ce ta kwade kaina ’yanzu Amna baki iya gaisuwan hausawa ba har yau, oh nikam Abbu bai kyauta muku ba, sosa wajen nayi ina jin haushi Ammi ta ban kunya a gaban bako, ‘wa alaiki salam, am good thank you’ maganar shi ta katse ni, lallai gayen nan ya hadu ta ko ina, muryan shi me dadi, ‘ka sha ruwa kafin Abbu ya dawo nasan yana kusa tunda kunyi waya’ cewar Ammi.

Ya ce, ‘toh Ammi zan sha.’ Nikam ta shi nayi ina ce ma Ammi ‘yau na gaji da yawa Ammi, barin je in ga mai ya saura kafin magariba ta karasa yi’ ta ce ‘yauwa da kin kyauta kuwa’ na fita a falon na shiga daki tukun in watsa ruwa in fito dan yanda na gaji din nan ba kan ta, nan ma exams muke amma mun jima yau din gaskiyar su Nurain, biyar da rabi nike dawowa amma yau har shida fa na shigo gida, ai kam na dade kuma jinkirin da aka samu na question papers da baa kawo da wuri bane ba, malam Idi direban mu ma ya dan jima dan kafin biyar da rabi yake zuwa saboda yasan bani son jira ni.

Nafi so daga na fito sai gida. Dama bani da wata kawa a nan, kawai dai in anzo zaa gaisa da kowa kuma in basu gane abu ba zasu tambaye ni musamman wani Abdul a ajin shi kam kusan komi ma baya ganewa nike ga dan kullum sai ya tambayi abu, har tausayi yake ban yanzu da ake jarrabawar nan dan a rubuce ne, ba amfani da komfuta kamar yanda akayi a aji da kullum kowa da komfuta a kan tebir nasa, toh haka nike fama da su har a exam din ma yanzu kafin a shiga sai na nuna masu in da basu gane ba, da yake sun ga nafi su kokari duka, zan kuma nuna masu sai dai bani sake masu sosai, Abbu kam ma ba so yake ba ba Amin ne aminin shi ya karba form din ya bani in cika dan ya ce zama na a gidan haka ba amfani tunda Abbun yaki in je jami’a, shiyasa Abbu ba yanda ya iya ya barni amma sai da na sha kashedi wurin shi kafin nan, yanzu gashi har na kammala muna jarrabawa na gamawa, wata shida muka yi, lokaci ba wuya kamar fa yau ne muka fara.

Fitowa nayi bayan na watsa ruwa na zira doguwar riga hade da yafa dankwalin rigar na wuce Ammi da bakon ta a falo, ko bakon Abbu ne ban sani ba, na ji ma karar motar Abbu din nike ga shi ya dawo, kicin na je na samu Hanan tana karisa hada fruit salad da Ammi ta bari, da alama zuwan bakon nan ne yasa ta ajiye, ‘Hana kawo in karasa ki huta.’

Turo dan bakin ta ta yi ‘haba mana Aunt Amna ni baza ku barni ina koya bane, in baki nan fa ni zan ke mana ko?’ dariya na yi na ja hancin ta ‘Na barki Hanan zaki yi harki gaji in dai aiki ne’ muka karasa tare muka tattare wurin, Hanan ta goge sannan muka fara shirin alawla kuma dan an fara kiran sallah, Ammi ce ta fito tana ‘har kun gama kenan? Nace ‘kalas na Ammi,’ ‘ki rabu da ni Amna da larabcin nan, in zaki yi hausa kiyi, nikam bani so ku cigaba haka ba hausa sai yaren Abbun ku kuka bama himma.’ Dariya muka yi duka, ‘A mmin mu kenan, kullum sai tayi mitar bamu iya hausa ba, ita kam bata damu da larabcin nan ba, zata ji dai amma bata mayar mana sai da hausa, mu kuma in dai ba da it aba bama hausar ma dan ko ba da abbu ban i da su Hanan ma bama yin hausan sai larabcin. Nurain ne ya fito shima yin alawla, ‘da ina ka shiga ne kam,’na tambaye shi, yace ‘na karasa homework nawa ne aunt Amna’ zaki mun English anjima, ‘nace toh naji ,tafi kayi alawla yanzu kam.

Idar da sallah na kenan Hanan tazo take cemun inzo mu fito da abinci, na tashi muka fita muka jera komai kafin Abbu ya shigo daga masallaci, bakon nan ya tafi nike ga tunda Abbu shi kadai ya shigo, zaunawa muka yi kowa yayi bismillah aka fara cin abinci, tuwon garin shinkafa ne fari sol da shi hade da miyan egusi Ammi tayi sai fruit salad ga kuma sambosa da bama rabuwa da shi kullum. Abbu na so sosai shiyasa. ‘binti ya exams din’? abbu ya tambayeni, Alhamdulillah Abbu, yau rashin question papers da wuri yasa muka jima’ na bama abbu amsa, ‘alhmdulillah tunda anyi ,sai next week ku karasa ba? Nace ‘eh Abbu inshaAllah.’

Ammi ce ta kallo mu ‘Abbu ka bata yaranka, basu yin Hausa sai Larabci, yanzu wani in yazo sai yace gulma kuke ai.’ Dariya Abbu ya yi, ‘haba hayaty, yara da yaren baban su sai kar suyi, Allah sarki da baba na nan ai fada zaiyi yaji suna Hausa ma, shifa kina gani har ya rasu hausar babu sai kadan kadan.’

Na ce ‘haka ne kam abbu’ko muma a wurinshi muka fi koya dan Abbu ba zama yake sosai ba. Ammi ce naji tana tambayan Abbu bakon ya tafi ne? yace ‘eh baki gane shi ba ko? ya cigaba da cewa makobcin su hajiiya ne fa dan wajen marigayi alhj Ibrahim, da yake bai shigowa sai yau da ya kira yace mun yazo nace toh ya shigo ku gaisa ina dawowa’ Ammi tace ayya, lallai sai yanzu na tuna, Abuja yake ba?’ ‘eh mana’ cewar Abbu. ‘nikam Abbu yaushe ya Abba zai dawo ne? Ko waya ba ayi da shi sosai fa,’na fada. Abbu ya ce ai kinsan karatun na su amma ko yau da safe mun gaisa sun dai kusa zuwa wani shekara zasu kamala duka.

Na ce ‘lallai fa shikenan mun sama doctor ba sai munje asibiti ba, ‘Ammi tace kinsan shi ai ba zai ma duba ki a gida ba ya fada ko kina ciwo sai dai ki bishi asibiti kaman kowa, nayi dariya. Da haka muka karasa cin abincin muka tashi. Abbu ya tafi masallaci sallar isha muma muka yi alawla muka miqa tamu. Falo muka koma na ma Nurain homework nashi. Hanan ma ta yi nata sannan muka dan yi kallo zuwa tara kowa ya shiga kwanciya.

Washegari bayan na dawo daga exams da yake sai yamma muke yi ba da safe bane, bayan mun ci dinner Abbu yace yana son magana da ni, na mike na same shi a falon shi yana sauraran labarai a redio, ‘Assalamu alaikum abbu’, ‘amin wa alaiki salam habibty’ ya amsa sannan yace in samu wuri in zauna akwai maganan da yake so muyi, zama nayi sosai na mika mai hankali na ina jiran me zai ce. ‘Hamna, Abbu ya kira suna na da yasa nasan muhimmiyar magana ce tunda Abbu bai kiran suna na sai dai ko Amna kmar yadda kowa ke fada. Ci gaba yayi da Magana, ‘Tunda kika taso ban taba maki dole ba saboda nafi so ku samu komai da ku ke so, to amma a yau ina so ki mun wata alfarma, kin ga bakon da yazo jiya?‘

Gyada kai na yi, ‘toh shi nike so ki aura Amna’ jin maganar nayi kamar saukar aradu, ban taba kawo maganar da Abbu zaimun ba kenan saboda yafi kowa sanin raayina sai wanda ya ganni yace yana sona kuma muka dan jima tare duk da ban ma kaina alkawarin zan so shi daga waje ba Amma ina so ya so ni in yaso in muka yi aure sai in nuna mai nawa son, haka shine tsarina, to Abbu in ban da shi ma ai jiya da bakon yazo bai nuna wani abu ba kuma ma ai da sai ya fada in ma sona yake ba wai haka kawai Abbu ya ce in aure shi ba, to a wani dalili?

Lokaci daya naji na tsane shi ma , na mance kyan shi da na gani jiya ,ni ba ruwana da wani wai yana Abuja kawai ba zan so aure irin haka ba, to ko dai abbu ma ya gaji da ganina a gidan ne?.’amna kar ki ce wai ko dan naga kina gida ne zan aurar da ke,ko daya’ maganar abbu ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na afka, ya cigaba da cewa ‘ban taba miki dole ba amna kuma yau din barin maki ba amma ina so ki san cewa a rayuwa wasu alakar muna shirya shi wani kuma Allah ne ke hada shi, ina so ki dauka cewa auren ki da Fudayl hadin Allah ne ba wai ni na hada ba, zanyi farinciki in har kika amince da auren nan ba dan komai ba sai dan nima hankali na zai kwanta kuma nasan ko bayan raina baza ki wulakanta ba, na yarda da tarbiyyar yaron Amna, na san shi ba tun yau ba kuma na yi istihara daren jiya da abun na kwana a raina, da na tuntube shi baimun musu ba shima nan take ya amince saboda haka ina so ki je kiyi tunani ba zan miki dole ba na sake fada.’

Zuwa yanzu hawaye ya gama wanke mun fuska, toh ni kuwa tunda Abbu ya fada ai ko bani so zan mai biyayya insha Allah kuma abun da zai sa Abbu farinciki zanyi ko da zan rasa nawa farin cikin ne, dafa kaina Abbu ya yi na dago na kalle shi da idona da ya yi ja,’’ Na amince Abbu, za..n a..u..r..e shi’ na fada murya na rawa, Abbu ya ce ‘kin tabbata?’ Na daga kai.

‘Allah ya miki albarka Amna, insha Allah baza ki taba dana sani ba, Allah ya baki ‘ya’ya da zasu miki biyayya kema,’ amin’ Na ce da Abbu na tashi na fita ina ganin jiri, da kyar na shiga daki na kwanta, yau ko falo ban zauna ba wurin su Nurain, da kyar na tashi jin kiran sallar isha na dauro alawla ina sallah hawaye bai daina zuba mun ba, addua nayi bayan na idar idan har aure na da mutumin nan alkairi ne Allah ya tabbatar , zabin Allah nike nema a kullum kuma ina fata hakan ya zamo zabin shi a gare ni.
Sai washegari Ammi ke tambaya ta meya faru ta ganni a damuwa, fada mata yanda muka yi da Abbu nayi duk da nasan cewa Abbun ma ya fada mata, haquri tayi ta bani ‘kalle ni nan Amna, kallonta nayi din ta cigaba da cewa ‘ina so ki dau hakan a matsayin kaddara kuma zabin Allah a gare ki toh insha Allah baza ki tozarta ba. Nasha fada miki kowa a rayuwa da kika gani Amna da irin jarrabawar da Allah ya masa saboda haka kisa Allah a ranki ki zamo mai bashi zabi. Abbun ki ba zai taba baki abun da zai cutar da ke ba kin san haka ai, nima kuma Amna na yaba da halin yaron duk da ba sanin shi nayi ba kin ga amma yanayin sa kadai ya isa kasan ba na banza bane ba, kullum addua ta Amna Allah ya kawo miki miji na gari kema kiyi aure shine burina.

Dan Allah kar ki sa ma kanki damuwa kinga jarabawa kike kin ji ba?’ Hawaye na na share nace ‘na ji Ammi amma ya zanyi rayuwa da wanda baya sona bana son shi Ammi?’ Dafa kai na ta yi’ kina da kyawawan hali Amna bayan kyau da Allah ya maki ba namijin da zai ki ki sai dai in ke kika zabi ya ki ki din amma zan zauna in koya miki dabarun zaman aure Amna dole na ma kar kije ki ban kunya, in dai kika iya kissa kin gama samun kan mijin ki Amna ba ruwan ki da wani magani ko wani abu.’

Kunya ma Ammi take ban in tana irin maganar nan, ‘bari in je in wanke toilet Ammi,’ Su Hanan kam sunyi makaranta bayan mun gama break, Abbu ma ya fita sai ni da ammi,’ ke kika sani Amna tunda zancen ne baki so kuma dole inyi’, na wuce ciki na bar Ammi dan in ta fara mitan ta ba gamawa zata yi yanzu ba ni ko wani hausan ma in tayi ban ganewa amsa ta kawai nike a wuce wurin.

<< Fudayl 5

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×