Skip to content

Fudayl | Babi Na Biyu

1
(1)

<< Previous

Ringing na wayata ne ya ankarar da ni, ban san lokaci ya ja har haka ba, karfe goma na dare, ni da tara nike barci a gida ma. Haleefa na gani a screen din wayata na dauka da sauri.

“Leefaaa” Na kira sunan shi.

Ya ce, “Ke nikam kar ki fasa mun kunne mana.”

Na ce, “Haba Leefa yanzu nake cewa zan kira ka, ka manta ni ba? Ko ka kira ka ji ya nake.”

Ya ce, “Kai Amnan Ammi kin cika mita ke kam to yanzu ba gashi na kira ba.”

Sai na ji hawaye yazo min na ce, “Leefa ina kewarku sosai Allah, zan iya kuwa?”

Ya ce “laa tabki (ki daina kuka) Amna, its going to be alright zai wuce kin ji?”

Na share hawaye. “Na’ ina fatan ya wuce din Leefa amma na kasa, baran iya son shi ba.”

Ya ce, “Ki cigaba da addua amna, kinsan kin fada mun zabin Allah ki ke so ba? Toh ina so kisa ma ranki wannan din ma zabin Allah ne a gare ki, kin ji?”

Na amsa da , “Na ji Leefa, yaushe zaka koma?”

“Next week, insha Allah, kin ga yanda dakina ya baci kuwa?”

Na ce “Ai haka Ammi tace wai kana can kana gyara.”

Ya ce “Oh kunyi waya ne ban sani ba,”

Na ce “Munyi video call, na kasa cin abinci shine ya kira mun su. Na ji dadi Leefa, ya kyauta mun.”

Dariya na ji Haleefa na yi, “Kinga akwai hope, he will be a caring hubby nah. Nikam dadi naji kin tafi na huta nima da surutu.”

Na yi dariya, “Leefa zan rama ka ji ba? Ya yi dariya.

“Just joking sis, zan fi kowa kewar ki ai kinsan hakan. Na ke ga ma gobe zan koma barin iya zaman gidan without you ba.”

Hawaye na cigaba da yi, “Leefa zanyi kewarka sosai nima, za ka ke zuwa mun ai ba?” Dariya ma na bashi.

‘Ni fa yayanki ne, ya za ayi inzo ina inlaw (siriki).’

Na ce ‘Dan kaga kayi tsayin kafa ko Leefa, kowa yasan dai ni ce babba.’

Ya ce ‘Ahaf namiji dai shine babba aka ce.”

Da haka muka yi sallama ina dariya. Haleefa ba zai taba canzawa ba, na shaku da shi sosai kasancewar shi ya ke bi na sai muka fi shiri amma kuma muna fada wani lokacin, har na tuno wani zuwan shi a ranan muka yi fada.

*****

‘Aunt Amna yaya Haleefa is back’ Nurain ya ke fada mun ina sallah. Ina idarwa kuwa da sauri na fita ina ‘Leefa oyoyo.’

Har wajen na fita, an dauko su da wani abokin shi, da Abbu yace zai je dama cewa yayi akwai wanda zasu dawo tare, ina fita kuwa ya tsume.

‘Toh meye na fitowa sai kace hauka.’

Ni dariya ma ya ban, ya wani tsume. Nan ma ba da Hausa muke magana ba ai da yasa na ji kunya tunda abokin shi da yayan shi da ya dauko su basu tafi ba fa.

Na ce, “Kai dai shigo gida kawai Leefa, la’anna ainaika tuzharu anna ka ja’I (akwai yunwa a idon ka).”

Wuce ni ma yayi ya bama Nurain jakan shi.

Na ce, “Lallai ma Leefa dan naje taranka din?”

Ya juyo ya ce, ‘Ba a so, ke bara ki yi hankali ba.’

Ya dage fa sai masifa yake, idan Leefa na masifa ina shan dariya, idon shi har wani sama zaka ga yana yi, he is so overprotective. Ko gyale na dauka zan fita in dai Leefa na nan sai ya ce, “Ammi yanzu ki ga da wannan rariyan zata fita.” Nan ma sai munyi fada, wataran ma ya ban haushi in fasa fitan kuma daga nan ya samu abun tsokana kenan. Ammi ma bata ganin laifin shi kai har Abbun ma cewa yake ya fi mu hankali wai har ya Abba ma.

Haleeefa ya na makaranta ne a ABU, university na zaria inda yake karantar architecture, tun yana yaro ya iya zane dan inya zana abu sai ka dauka hoto ne ma. Na shaku da shi sosai duk da abokin fada ne amma ina ji da shi. In zai tafi har kuka nike kuma ni zanyi ta tambayan yaushe zai tafi na gaji da ganin shi amma da anzo tafiyan kuma zaka ga kuka a waje na, abun ma dariya yake bama su Ammi.

Tun hudu na asuba nike tashi in mai wani abu, cincin, meatpie ko sambosa ya tafi da shi. Already dama an mai miyan nama da zai tafi da shi, bana so yaje yana dora girki daga komawa. Ina son kanne na sosai, su ma suna sona, bani da tamkar su.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×