Skip to content

Gangar Shaidan | Tambaya

Bookmark

No account yet? Register

GANGAR SHAIƊAN 

01.

Da sunan Allah, 

Mai ikon kome da mai shi. 

02.

Allahu gwani, 

Wanda yai mana rai da kishi. 

03.

Manzon Allah, 

Wanda kaf duniya ba kamar shi. 

04.

Ya zo da gargaɗi, 

Akan Ibilis da mabiyan shi. 

05.

Sahabbai jimla,

Har malamai duka sun tsane shi. 

06.

Ita Gangar Shaiɗan, 

In har ya buga sai a bi shi. 

07.

Watau sautin Shaiɗan, 

Ko a ina kake za ka ji shi. 

08.

Taken Shaiɗan, 

Da ya tashi za ko a bi shi. 

09.

Mabiyan Shaiɗan, 

Tabbas su ne za su bi shi. 

10.

Hanyar Shaiɗan, 

In yai huɗuba sai su bi shi. 

11.

A zuci in har ya shigo, 

Zance ya ɓaci ga mai shi. 

12.

In ya kama ka, 

Addu’a ce kaɗai za ta kar shi. 

13.

Igiyar Shaiɗan,

In ta kama ka za ka bi shi.

14.

Ammbaton Allah, 

Shi kaɗai ke maganin shi. 

15.

Ya Ilahu Allahn mu, 

Muna neman tsari akan shi. 

16.

Ka kiyaye mu, 

Ka hana mu mu bi shi. 

17.

Ka tsare ahali, 

Da zuriyar mu daga gare shi.

Next >>

How much do you like this post?

Average: 4.4 / 5. Rating: 7

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Haiman Raees

Idan har rayuwata bata zamo mai amfani ga kowa ba, to mutuwata ba za ta zamo rashi ga kowa ba.View Author posts

Share the story on social media.

2 thoughts on “Gangar Shaidan | Tambaya”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.