Da fa Faruk Al'ameen yayi yana cewa.
"Karka sake ka fita, bari ni naje bayan Motar naga miye ke faruwa".
Daga kansa kawai Faruk yayi, Al'ameen da zuciyarsa ke bugawa ya d'auki wani k'arfi dake a gaban Motar k'ark'ashin Motar ya zaro shi yana b'alle marfin Motar ya fito zuwa waje.
Zuciyarsa ce ta halba da k'arfi ganin wani Zombies ya rik'e masa riga da fitowarsa, sauran Zombies da hankalinsu baya Kai, sukayo kanshi kamar suna jira.
Yana zufa ya daddage iya k'arfinsa yana buga masu k'arfen dake rik. . .