G.R.A. Estate Residential Area, Katsina State Nigeria
ANAM POV
Da mugun gudu Anam ta sakko k'asa tana duban Mom dake tsaye hankali a tashe rik'e da waya a hannunta, sai kiran waya take amma ana cewa wayar a kashe.
"Mom wallahi nima sai kiran wayar Hanan nake ita da su Faruk amma a kashe, ya za'ai su bi su kashe wayoyinsu wannan wane irin hauka ne haka Mom?".
Mom dake cikin halin rud'ani itama ta sake gwada kiran nasu again a kashe, sauke wayar tayi kawai tana dafe kanta ta kalli Anam. . .