Shigar su asibitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi . Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki , Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa, "Wai me yake faruwa? mene ne ka yo a ciki , nifa ka fara bani tsoro ." Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Babu komai kawai ki taho." yasa kai ya fita waje yana cewa, "Harun zan kasheka." Zainab sauri tai tasha. . .