Zuwa ƙarfe uku ta gama kintsawa, ta je ga Mami ta ce mata tana da lecture ƙarfe huɗu kar a turo Baba Direba sai shidda. Zawwa ta bita da kallo daga sama har ƙasa, wata doguwar baƙar riga ta zira ta ɗaura wani cukurkuɗaɗɗen niƙaf da alama da ƙyar ta gano shi cikin shirgi, hatta a hannunta sai da ta saka safa haka ƙafarta tamkar dai wadda za a bawa laƙanin shiga Shi’a.
“Lafiya ko?”
Ta furta tana daɗa ƙare mata kallo.
Ta yatsine fuska ta cikin niƙabinta ta haɗe hannayenta guri guda, cikin rawar murya ta ce.
“Mami sanyi nake ji.”
“Ko yaushe kika fara jin sanyi? To ki goge niƙaf ɗin mana ji shi fa kamar an kwato shi daga bakin kura.”
“Ba lokaci ne na makara kuma lecture ban so ta wuce ni, Mami na tafi sai na dawo.
“Au to madalla.”
Da haka ta fice zuwa gurin Huzaif.
Tun daga nesa ta hange shi zaune, saɗaf-saɗaf ta laɓaɓa gurinsa ta zauna, ya bita da kallo sai kuma ya fara ƙoƙarin miƙewa zai canja waje, da sauri ta ɗaga masa niƙaf ɗin fuskarta tana masa gwalo.
Ya ja siririn tsaki cike da takaici.
“Wai saboda Allah menene haka? Wannan da cikin dare ne ai sai ki firgita mutum.”
“Ni ma a firgicen nake, manta kawai.”
Sai kuma ta yi masa murmushi a bayan ta ƙare masa kallo.
“Sir wallahi ka yi kyau kamar ango, amma wannan shi ne zuwa zancenka na farko?”
Ya harareta yana yafito wani waiter ya kawo musu smooth. Sai kuma ya maida hankalinsa kanta yana kallon idanuwanta.
“Menene ke faruwa wai, duk na ganki a wani firgice.”
Ta waiwaiga hagu da damarta, ta ɗaga kai tana ganin yadda motoci sai ku yi jerin gwano a can nesa da su, ai sai ta yi tsam ta miƙe tsaye.
“Mu shiga daga ciki dan Allah, bansan zaman waje duk ƙura ta buɗe ma abin sha.”
Hannunsa yasa ya jawota ta koma ta zauna. Sai kuma ya yarfe hannun yana yatsine fuska.
Ta bishi da kallo Idanuwanta a ƙanƙance tana taɓe masa baki.
“Ji abinda kake yi sai ka ce ka taɓa ƙazanta.”
“Ban saba taɓa mace ba, gidanmu ma babu mata. Sannan ai nasan da cikin na zauna anan ko, Ni bansan can dan haka ki zauna zan kare ki daga duk wata ƙura.”
Ta masa murmushi a sanyaye.
Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon idanuwanta.
“Kina ji ko, magana mai muhimmanci nake so mu yi, ina so ki sanni ki san kome nawa kafin musan matsayar mu.
Ta tattaro hankalinta kansa duk da jefi_ jifi ta kan juya ta kalli inda aka ware dan parking motoci.
Ya daɗa nisawa tamkar yana jajanta abinda zai faɗa matan.
“Haƙabiyya, asalina ba ɗan nan ba ne, mun zo ne daga can wani ƙauye da ke cikin Gombe. Mahaifina ya…”
Ta yi wata irin zabura tana matsowa kusa da shi idanuwanta a warwaje.
“Huzaif! Maza waiga damarka ka gane mini akwai wani babban mutum jikin wata ƙatuwar Ash ɗin mota.”
A hankali ya zare hannunsa daga nata da ta ƙanƙane ya juya. Tana kula da sa’adda idanuwansa suka ƙara girma da zallar mamaki, sai kuma ya miƙe tsaye ita ma ta miƙe ko’ina na jikinta na kakkarwa.
“Wai baka ga kowa ba ne gashi can fa a tsaye.”
Ta murta tana daɗa nuna masa mutumin da ke tsaye yana kallonsu. A sannan taga mutumin yasa hannu yana yafito Huzaif, shi kuma ya tafi da sauri. Hannunta a ƙirji bakinta a hangame haka ta tsaya tana kallonsu.
“Ashe kana nan kana hutawa…”
Mutumin ya furta yana kallonsa cike da fara’a.
“Kana ji waccar yarinyar da kuke tare ya kuke da ita ne?”
Huzaif ya yi wani ɓoyayyen murmushi yana sanya hannu ya sosa ƙeyarsa cike da kunya.
“Abba Ɗaliba ta ce…”
“Au to to to.”
Abba ya furta yana sanya hannu ya zare hular kansa ya ajeta saman mota.
Hankali tashe yake duban likitan yana duban jibgegen baƙin basamuden dake gefensa yana sharce gumi da gabjejen bayan hannunsa. Hannunsa ya dunƙule ya naushi bangon da ke gabansa a karo na biyar sai kuma ya cije baki yana yarfe hannun. Da sauri ƙaton mutumin ya matso kusa da shi zai riƙe shi, ya yi azamar matsawa gefe yana ɗaga masa hannu alamun bai buƙata, sai kuma suka dubi juna kafin kuma su maida dubansu kan Hamdiyya da ke shimfiɗe saman gado tamkar matacciya, suka zarce da kallon ga firgitacciyar fuskar tsamurmurin likitan da ke tsaye gefe yana muzurai.
Huzaif ya furzar da zazzafar iskar bakinsa yana ɗaga ƙafarsa zuwa gabansa.
“Wai shin mene ya tabbatar maka da cikin gareta? Na ce maka so nake a gwadata kawai ko tana da irin ciwon da nake ɗauke da shi, uban ubanwa ya ce ka yi mata gwajin cikin? Ta ina za ta samu cikin? Ba ta taɓa aure ba haka bayan ni wani bai taɓa nemanta ba, Ni ɗin da na neme tan an tabbatar mini ba zan taɓa haihuwa ba, a nasan ba zan haihun ba ma ban yarda wani abu nawa ya shiga jikinta ba, to a gidan gyatuminka za ta yi cikin, ko kai ka ɗirka mata shi?”
“Ta yiwu kuskure ne yallaɓai, ana yawan samun akasi irin wannan, wallahi ka gani dai ciki gareta na tsawon wata biyu, haka naka gwajin bai nuna kana da wani ciwo ba.”
Ya furta cikin rawar jiki yana jere masa takarsun da ke gefen gadon.
Huzaif ya dafe kansa idanuwansa sun daɗa kaɗawa, shiru ya ratsa gun na tsawon mintuna, can ya ɗago da sauri yana isa ga fuskar Hamdiyya ya shafa gefen kuncinta.
“To ko ƙusa kai ko filaya ce ka zura a cikin cikin jikin nata ka kwaƙule mini tsinanne, kana ji ko? Ka tabbata ka kwaƙule shi tas yanzu-yanzu, kuma kar ka kuskura ka yi aikin da za ta rasa ranta!!”