Skip to content
Part 11 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Likitan ya yi baya a tsorace ya ji ya daki wani abu kamar dutse, ya waiga da sauri ya ga wannan ƙaton ne ya sanya ƙirjinsa ya tokare shi yana kallonsa cike da gargaɗi, ya sauke numfashi da ƙyar yana haɗe hannayensa guri guda alamun bai sake taɓata, cikin rawar murya ya ce,

“yallaɓai ina rantse maka da Allah na taɓa yarinyar nan da niyyar kwaƙule cikin nan za ta iya mutuwa. Bansan yadda zan yi aikin nan ba tare da na illata ta ba, ka taimake ni ka rabani da aikin nan na tafi ba hurumina ba ne.”

“Ni kuma kai ɗin kaɗai na yarda ka mini aikin…” 

Sai kuma ya yi shiru yana jijjiga kansa.

“…Ba ni abinda kuke bawa mata idan basu buƙatar cikin jikinsu.”
Ya ƙarasa a can ciki, muryarsa ba ta fita tsabar ɓacin rai.
Likitan ya girgiza kai yana waigawa ya dubi ƙaton da ke bayansa.
“Akwai kam, naga kwayoyin ma a chemist ɗin wani Inyamuri, muje to sai a baku. Amma na faɗa muku zubda cikin nan hatsari ne gareta.”
“Ado Maɗaci!”

Da sauri ƙaton mutumin ya matso kusa da shi yana amsawa.
“Mayar masa baƙin ƙyallen fuskarsa ku tarkata dukkan tarkacen gwaje-gwajensa ku fice, ka tabbata ya baka kwayoyin kafin ku rabu, ka kuma tabbata ba zai sake tuna ko da fuskar ka ba.”

Maɗacin bai ce kome ba sai juyawa da ya yi ga likitan ya danƙoshi shi da ƙatuwar akwatin ƙarfen hannunsa suka fice daga gurin.

Komawa ya yi gefe ya zauna yana dafe kansa cikin azabar tunanin abin yi, ya fi ƙarfin minti 30 a haka kafin ƙofar ɗakin ta buɗe Maɗaci ya shigo. Miƙewa ya yi da azama ya isa gare shi ya miƙa mishi hannu ya sanya masa kwayoyin. Sai kuma suka yi cirko-cirko suna dubanta. Maɗaci ya nisa a hankali a bayan ya sanya hannu ya dafa kafaɗarsa.
“Ka yi kome ka gama kafin nan da ƙarfe takwas na dare lokacin da za a zauna a Hamada,  kasan a wannan lokacin Oga zai iya ganin duk abinda muka ɓoye. Ba kai nake ji ba, kaina nake ji da tsawon shekarun da muka kwashe da shi ban taɓa yin wani abu da ba umarninsa ba sai a kanka. Kuskure ne an riga anyi, kuskure na biyu shi ne karmu kuskura  mu sake ƙoƙarin ƙin yin abinda ya umarta da zarar ya san tana da cikin.”

“Ba zai sani ba, daga nan ba zan ƙara kusantar ko garin da take ba! Itama idan da abinda za a mata ta mantani ka duba mini zan matan.”
Maɗaci ya yi wani murmushi me kama da dariyar Giwa. Ya ɗan bubbuga kafaɗarsa yana juyawa.
“Ka yi koma menene kafin nan da ya sani, tunda na zo Hamada ban taɓa ganin mutum mai Sa’a kan oga ba sai kai, za ka iya gwada taka dabarar, kar ka manta har abada ni me rufa maka asiri ne.”
Da haka ya fice daga gurin.

Ya ƙarasa inda take kwance idanuwansa cike da masifa, da ƙarfi ya hau jijjigata har sai da yaga yatsunta sun motsa. A hankali ya sanya hannu ya zare zoben hannunta ya aje gefe.
A sannu ta fara buɗe idanuwanta har ta buɗe duka suka yi tozali da juna, ta yi wata irin zabura tana tashi zaune, ta buɗe baki za ta zuba ihu ta ji wuyanta a cikin tafin hannunsa ya mata wata irin shaƙa yana haɗa kanta da jikin gadon. Wata kwallar azaba ta silalo ta gefen idonta, ta ware manyan idanuwan nata tana kallon yadda Huzaif ya zame mata dodo-dodo, farar fuskarsa ta yi jajur tsabar bala’in ɓacin rai hancinsa har tsiyaya yake.

“Bansan ke ce ajalina ba sai yanzu, ban ma san ke annoba ba ce sai da na yi kuskuren haɗa jiki da ke, tsabar jaraba irin taki abinda na yi ba acikin saninki ba, ba a cikin hayyacinki ba, ba ma da yardar ki ba shi ne kika buɗe jarababbiyar mahaifarki kika amshi ciki ko? Dan ki idasa halakani yadda aka daɗe da halakani, ki idasa zame mini baƙar annoba ni da nake fatan rabuwa da tawa masifar cikin ɗan lokaci. Hamdiyya banzo rayuwarki dan haka ba, na zo ne dan gyara tawa rayuwar da ta wanda ya zame mini dole, ban shirya  mutuwa nan kusa ba, ban kuma shiryawa aure balle ya’ya, abinda ke gabana ya shallake duk wata ƙawar duniya. Ki buɗe tosasshiyar ƙwaƙwalwarki ki saurareni, ni Huzaif ban zo rayuwarki da kome ba sai dan gyara tawa, ban taɓa son ki ba ba kuma zan taɓa ba, ke duk wani labari da kika san na faɗa miki ƙarya ne, ƙirƙira ne, sai na zo gabanki ma nake ƙirƙira. Idan na ce ƙarya ina nufin kome ƙarya ne, idan na ce kome ina nufin har labarin da na baki na mahaifiyata ƙaryane! Ke, kin tuna lokacin da na fara ganinki?”

Ya saurara yana sassauta riƙon daya yiwa wuyanta.

“Duk abinda na tambayeki Ki girgiza mini kai kina ji ko!!”

Ya furta ƙasa-ƙasa yana zare hannunsa daga wuyanta ganin idanuwanta na shirin ƙafewa.

Ta yi yaraf gefe tana kakarin azaba. Ya ƙara sanya hannunsa ya jawota ya dangwararta ta yi zaman ‘yan bori, ya danƙi kafaɗunta bakinsa na tiriri.
Ta buɗe baki za ta yi magana ya yi azamar saka yatsansa a bakinsa yana zare mata idanuwansa da suka zame mata na mayunwaciyar kura.
“Shiiiiittttttt! Ban ce ki ce kome ba har sai na gama, ai ke kin gama zuba zantukanki a kalaman soyayya, yanzun lokaci nane, ki sake ƙoƙarin magana ki gani idan ban sanya kwalba na kwashe gashin kanki ba, idan yaso gobe da sassafe a yanko mini kan na aikawa Iya ta yi romo da…”

Wata irin zabura da ta yi a bayan ta tattaro dukkan ƙarfinta ta hankaɗe shi ya katse masa zancenta, ta sake hantsilawa can baya tana ƙanƙame jikinta da ke kakkarwa ta ko’ina, ita gabaɗaya sai yanzu ta fahimci kome, sai yanzu ta fara gane wanda ke tsaye gabanta wannan ɗin nan dai da take mutuwar so ɗan yankan kai ne, gashi nan yana ce mata idan ta yi magana  zai yanka kanta ya kaiwa Iya ta yi romo. Ai sai ta wawuro hijabinta da ke gefe ta tusa shi a bakinta tana hawaye masu azabar raɗaɗi. Ta ƙanƙame jikinta curi guda, ji take tamkar duniyar ke kewayawa da ita.

“Da kyau!”
Ya furta yana matsawa inda take.
Ta ƙara matsawa baya idanuwanta a warwaje tana kallonsa sai kuma ta tuna abu ta sanya hannu a kanta ta ji ta shafo kitson kanta.
“Wayyo ni Iya wayyo Kawu, Huzaif ka nawa Allah kar ka bada kaina ka nawa Allah ka taimake ni ko dan son da nake maka.”

Murmushin gefen baki ya kuɓce masa cike da tsabar takaici.

“Ke yanzu baki fahimci an ƙona wannan motar ba ne dan su Iya su fahimci mun mutu kar a ga ɓacewa kika yi a kama yi mana saukar ƙur’ani lamuran da aka shirya su ɓaci? Ke wai meyasa ƙwaƙwalwarki bata ɗaukar haske ko kaɗan? To ba Iya ba, hatta sallamammen kawunki da ya sallamo mini ke garin Kaduna ba zai ƙara tunaki da sunan rayayya ba sai dai matacciya. Haka Iya nan da kwana arba’in za ta yi miki sadaka ta shafe babinki, kinsan irin jana’izar da za a ma su direba?”
Ya yi shiru yana kallonta, da sauri ta tuna abu ba shiri ta hau girgiza masa kai alamun a’a.

“Yauwa, to rami za a yi a tattara toka da ‘yan ƙasusuwan da suka rage a yayyafa musu ruwa a tura a ramin a maida ƙasa. Shi ne ƙarshenki da Ni a fuskar su Iya…”

Ta riƙe kanta da ƙarfi jin yana shirin rabe mata biyu. Ta tanɗe busassun laɓɓanta tana ƙara yin baya. Sai yanzu abubuwa da yawa ke surarewa cikin kwakwalwarta. Ta tuna ranar da ta fara ganinsa a asibiti ta fito waje nemawa Babanta goro da ya ce yana buƙata ta hange shi tsaye can gefe yana lissafa kuɗi, ta tuna sa’adda suka haɗa ido ƙirjinta ya buga kyawunsa ya ɗauke mata hankali har ta gagara ɗauke idonta kansa, ta tuna ita da kanta ta ƙarasa gurinsa dan kawai ta masa magana ta kama tambayarsa ko yaga wata yarinya da ke kawo goro nan gurin. Ta tuna yadda ya kalleta fuskarsa babu walwala har ta ji haushin kanta kafin kuma ya sake su fara hira, ta tuna har ta zo wucewa bai nemi sanin sunanta ba sai da ta dawo da kanta ta faɗa masa sunanta Hamdiyya Haallir, ta tuna yadda tsoro ya bayyana a fuskarsa kafin kuma kome ya washe cikin idanuwansa ya faɗa mata nasa sunan Huzaif, ta tuna bai taɓa faɗa mata sunan garinsu ba, ta tuna bata taɓa jin wani da ya ce ya san shi ba, ta tuna ta tuna abubuwa da yawan da suka haifar mata matsananin ciwon kai, ta runtse idanuwanta da ƙarfi a yayin da zafafan hawaye suka ƙara biyowa kuncinta.

Hannunsa da ta ji a fuskarta ya shafe hawayen ya sakata sake zabura tana kallonsa a firgice.

Ya mata murmushin da ke karya dukkan kwarin gwiwarta a bayan ya sake duƙawa gabanta.

“Me kika tuna? Haɗuwarmu ta asibiti ko? Kin fahimci ba ni na neme ki ba, ba ni na jawo ki tsayawa gabana ba, karambaninki da tsabar son farin namiji ya kawo ki. Ni kawai an umarce ni da na zo nan ne zan samu mai irin sunan da nake buƙuta. Ko kinsan a sa’adda kika doso ni sai da ƙirjina ya buga sau ɗari da sittin cikin second 20 tsabar tsoron kar ya zamana ke ce muke nema?

Hamdiyya na so ke ɗin wata matsiyaciyar karuwace da iyayenta suka ce mata je ki kya gani na tabbata idan ta haɗu da Ni to kuwa ta gamu da abinda suka mata fata.

Banso ace ke ce me sanyin hali da yin kome domin Allah ba, ban so ba idan kin yarda, amma ki sani da yawa-yawan abinda ya faru dake ke kika jawowa kanki!”

Kallon da ta bishi da shi baki buɗe ya saka shi yin shiru yana ɗaga mata gira. Ta ɗan ƙara nesanta kanta da shi tana haɗe tafukan hannayenta biyu.

“Huzaif domin Allah tunda ka ce tura ka aka yi ka faɗa musu baka same Ni ba, domin Allah ka taimake ni ka ga Ni kadai iyayena suka barni, domin Allah ka barni inga bayana.”

Kawai tsura mata ido ya yi har ya rasa me zai ce. Ta ci gaba da rera kukanta yana saurararrta yana kallon lokaci. Sai can ya nisa a hasale Yana danƙo ƙunnenta guda ya murɗe.

<< Hakabiyya 10Hakabiyya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.