Skip to content
Part 16 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

March, 1993

“Hameedu ka ga fa bishiyar da ya ce mu tumɓuketa har jijiyarta wai a ƙarƙashinta aka ce masa maganin yake.”

“Ni fa Bawa ba tumɓukewar ba ce damuwata, wai baka ji duka aikin fam Ashirin zai ba mu ba, waye zai masa aikin a haka idan ba mu da yake ganin ya raina ba? Haba shi talaka kullu yaumin ba a nufarsa da khairi? To ba zan yi aikin ba, kai dai ka yi idan kaga za ka iya zan dinga miƙo maka ruwan sha…”

Ya ɗan nisa ganin Bawan ya yi tsaye yana kallonsa.

“Yanzu saboda Allah ka duba wannan sabon maganin da aka kawo na Inna sai na bada fam Ɗari za a ba ni shi, gashi kwana biyun nan jikin nata ya daɗa tsananta, haka maganin yana mata aiki sosai…”

Ya daɗa nisawa yana fidda wani zazzafan huci, akwai alamun abin na matuƙar sukarsa cikin rai.

“…Kayya! Wallahi wani bin ji nake kamar na ratsa tsakiyar jeji na zama ƙasurgumin ɓarawo ina kwatar dukiya ta dole, da gaske ba na so yunwa da talauci da ciwo su yi silar mutuwarta yadda suka kashe Yawale da Baba…”

Bawa da ke can gindin bishiyar tsaye yana kallonsa ya aje digar hannunsa da sauri ya ƙara so gabansa yana mai dafa kafudunsa.

“Hameedu na sha gaya maka ba za mu taɓa dawwama haka ba. Shin baka kula koyaushe kai na daɗa wayewa ba abubuwa na sabunta kansu, yanzu bar tuna wannan lamarin da aka shafe shekaru da yinsa, da yardar Allah albarkacin roƙon da muke yi ba za a ƙara yi mana farin yunwa ba har a naɗe duniyar nan ballantana wani namu ya sake mutuwa. Ka taso muje muyi aikinmu, idan ya biya mu kwabban sai na haɗa maka da nawa a sai mata maganin.”

“To kai kuma fa? Na san fa babu kome a rumbunka. Sannan aikin nan tunda na furta ba na yi, kasan ba na yin ko.”

“Kar ka damu, kasan surukina da ya gane gidana babu kome zai turo mana ko naman farauta ne mu gasa mu ci. Kai duk rashin da za a yi Zawwa ba ta taɓa bari na kwana da yunwa.”

Hameedu ya murmusa yana riƙe bakinsa.

“Oh, ni ma dai baɗi zan shiga daga ciki inji mai kuke ji, kaga dai tun Baba Yana raye sannan ma girma bai gama ratsani ba yake nuna mini da na yi aure. Ya kance Hameedu ina so muyi yawa a zuri’armu, da yawan lokuta yawan iyali maganin talauci ne, saboda kowane yaro da za a haifa da irin arziƙin da zai zo maka da shi, Allah sarki Baba, Allah ka jaddada rahma gare shi.”

Suka yi shiru na ɗan lokaci da alama kowannensu ya tuna rabuwarsa da nasa mahaifan, sai can Bawa ya nisa.

“To kaima dai na rasa wane girma kake so ka yi kafin ka yi auren, kana gani dai ni ɗin nan tun ban kai Ashirin ba aka mini auren fari, bana raba ɗayan biyu nan da shekaru biyu Haadiru zai iya tardo ka a tsayi, gashi dai bara da Inna ta maka tayin matar marigayi Yawale nan gurina ka ringa ɓuya har sai da ka tabbatar ta yi aure can wani gari tukunna ka fito, hala dai Zawwa kake jira ta haifa maka ɗiya mace bayan shekaru shabiyar a sakaku a lalle?”

Hameedu ya zaro ido tamkar yanzu abin ke faruwa, sai kuma ya sanya hannu ya dan shafo ƙeyarsa yana murmushi.

“To kai Bawa ai barka zaka mini da ban karɓi tayin Inna ba na auri matar Yaya Yawalen, da yanzu fa ta maidani ƙaramin bazawari an naɗa mini rawanin takaba tunda dai shekara bata zagayo ba ta mutu a yayin haihuwa. Ni fa a yanzu a kaf karkarar nan banga wacce zan aura ba da za ta riƙe mini yaron nan maraya, kasani Inna girma ya kamata ga ciwo, haka dangin mahaifiyarsa babu ko ɗaya kwakkwara da zai iya kula da shi, yo bare ma haƙƙi nane hakan, Allah Bawa yadda nake ji da yaron nan bana fatar zama da matar da za ta zalunce shi, so nake ma nan gaba kaɗan na yi noman riɗi mai yawa na samu na saka shi a makaranta irin tasu Haadiru.”

“I, lalle Hameedu ka girma tunda har kana jinka a matsayin uban Huzaifu.”

Ya kwashe da dariya tsabar jin daɗi.

“Ka bari kawai Bawa, idan babu uba a gida to fa dole girma ya kama babban ɗa. Bansan yaro nada daɗi ba sai da watarana dana shiga gida yaron nan ya rugo da gudu yana kirana Baba. Kayya! A abubuwan jin daɗin da na tarar a duniyar nan wannan shi ne mafi girman da ya sakani farin ciki a cikinsu. Allah dai ya raya mana su ya musu Albarka.”

“Amin, amma fa kasan kuskurene ka ringa tunanin auren matan ƙaryar nan zalunci ne ga yaronka. Kana ga dai Zawwa ta san Haadiru ya kusa tarda ta a shekaru amma haka ta riƙe shi kamar ɗan cikinta. Ina mamakin da shi kansa yaron shakkarta yake haka biyayya yake mata tamkar uwar da ta tsugunna ta haife…”

“Yo ai shi wannan dole ce, tsakani da Allah fa Bawa bari na gaya maka gaskiya. Kaga ni ɗinnan da ace gida ɗaya muke da Zawwa dole zan dinga mata biyayyar nan, yarinyar da ba ta ƙi a kira su farauta tsakiyar dare ta tashi ta tafi ba, kar ka manta fa har kwana uku suna yi a jeji ita da ubanta ka rasa me suke tsinta. Ga babban abin tsoron ma wannan kakan nata da ya koma zaman zaure yana duba da koyawa matan karkara yadda za su mallake mazajensu, wai ni anya ba anan suka shanye ka ba har ka karɓi tayin ‘yarsu da sau ɗaya aka taɓa samun wani baƙon bafillace ya ce yana sonta ubanta ya hana shi, naga kai kwata-kwata baka ma shakkarsu wai har so kake ka haihu da su ko?”

Bawan ya harare shi.

“Ah lalle za ka sa yanzu na haɗaka da Zawwar ta ji me kake faɗi kanta..”

“Haka fa, shi yasa ai kaki faɗi mini gaskiyar a mace ka same ta ko kuwa wani abu daban, na san dai tabbas kurayen jeji da dogayen bishiyoyin nan sun gama kwashe albarkar jikinta.”

Bawan ya ɗaga hannu zai kai masa zunguri ya yi maza ya kauce yana masa dariya.

“Yi hakuri Allah ya barka da Zawwa babban Yayana makwafin ubana.”

“To Amin.”

Ya furta yana juyawa zuwa ga bishiyar ya fara haƙarta.

Shi kuma ya bi bayansa da kallo yana daɗa godewa Allah da iyayensu da suka kulla amintarsu shi da Bawa, duk da kuwa ya bashi shekaru kusan goma sha biyar a lokacin. Sai dai da yake shi ɗin ɗan ƙuyas ne a bushe ga gajarta sai a zaci Hameedu da yake dogo sosai mai gaɓɓan girma shi ne sama da shi nesa ba kusa ba.

Ya daɗe yana haƙar bishiyar kafin ya fara hango jijiyoyinta. Himma ya ƙara sawa ganin iskar yammaci ta fara buso su wankin hula na shirin kai su dare, can dai ya saka hannu ya fara ƙoƙarin jawo wata jijiya da yaga ta bullotso to lokacin ne ya ji kamar ya taɓa ƙarfe, ya ƙara shafa gurin ya ji tabbas ƙarfe ne, ya ɗaga gatarinsa ya sari gurin sai ga sautin haɗuwar ƙarfe da ƙarfe ya fito. Da hanzari ya fara tone gefe da gefen ba daɗewa ya hango wata baƙar akwatin ƙarfe.

Da ɗumbin mamaki ya sanya ƙarfinsa ya jawota har ya fiddota bakin bishiyar yana numfarfashi. Shi ma ya fito daga ramin bishiyar ya dubi Hameedu da ke can gefe yana ɓasgar rake ya kwala masa Kira.

Ganin akwatin da baisan da wanzuwarta a gun ba ya saka shi rugowa da gudu ya tsaya gabansa.
“Wannan fa? Ji wata irin tsohuwar Akwati irin ta zamaninsu kakana Hambali.”

Bawa ya sharce guminsa yana haki.

“Yanzu na tsinceta a anan ƙasan bishiyar, da alama a wani lokacin can aka binneta har bishiyar ta fito bisanta.”

“Mu buɗe to muga menene a ciki.”

Suka dubi juna a tare kafin kuma kowa ya ɗau gatarinsa su fara sarar dakakken baƙin kwadon da ke jikinta. Da ƙyar suka iya ɓalle kwaɗon suka ɗaga murfin suka yi tozali da abinda ya saka su yin baya a tsorace suna ruƙunƙume junansu.

Sulallane masu tsananin sheƙi na zinari da wasu irin sarƙoƙi fal a ciki, sai wata faffaɗar jarida da aka liƙata a jikin murfin akwatin ta ciki, takardar kanta ta koma ja tsabar daɗewar ajiya, jaridar na ɗauke da hoton wani tsohon Bature mai yawan gashin baki fari fat duguzunzum, ya karkata malafar kansa gefe bakinsa na ɗauke da taba lofa a haka aka yi hoton.

Cikin kaɗuwa Bawa ya dubi Hameedu.

“Kasan Zinari ko? Wannan fa zinari ne sak irin wanda aka taɓa nuna mana a wani gari can da muka taɓa zuwa da Tsohona, wai a Alif ɗari tara da nawa ne ma aka ce baƙin turawa sun zo yankinmu?”
Da ƙyar Hameedu ya haɗiye wani kakkauran yawu ya ba shi amsa.

“Ni zan baka labarin Zinari Bawa duk da ban taɓa ganinsa ba ko a mafarki amma na sha jin ana cewa abu ne mai sheƙi da ɗaukar ido da tarin daraja. Hmm! A Alif duba ɗaya da ɗari tara da sittin da tara suka zo, hala tasu ce akwatun?”

“To kai ba ka ga irin mutunensu a jikin takardar nan ba, nufinka shekarun Akwatin Ashirin Da Huɗu (24) kenan, kai anya ba ƙarafun banza ba ne a ciki aka musu ado da zaiba, bari dai naji?….” Ya furta yana duƙawa a ɗan tsorace ya ɗauko sarka ɗaya ya riƙe.”

“Subhanallahi! Na rantse da Allah shi ne, ka ji nauyinsa ko? Ina tunawa duk da ina yaro ko sa’adda muka ga zinari da Baba ya tambayi yadda ake gane shi ance masa yana da nauyi. Ka ji nauyin Sarkar nan kuwa, amma anya dama ana maida zinari sule?”

Bawa ya furta da zallar mamaki.

“Ba mamaki fa idan kaga an maida zinari dutse ma, mamakin shi ne wanda ya binneta yana ina, tasa ce ko kuwa satowa ya yi? Mu kan mu yaya za mu yi da ita, shin anya ma ta mutane ce ko kuwa Ajiyar jinnu ce?”

Suka tsurawa juna ido sai kuma suka zube daɓass suna daɗa ƙarewa akwatin kallo.
Can dai Bawa ya nisa ya ce.

“Ka ga yanzu tunanin akwatin na waye bai taso ba, wannan bishiyar da ta ginu bisanta na tabbata ita za ta hana wanda ya ajiye akwatin fahimtar wurin. Haka tunanin ajiyar mutanen ɓoye ce ma bai taso ba, saboda idan ma ta sun ce to fa suna sane suka saka mu a hanyar da za mu tsinta. Dan haka mu aje a tunaninmu wannan akwatin tamu ce, haka ita ce za ta zama silar warwarewar kome a gare mu, mu nemi sanin yadda za mu yi amfani da zinari, idan ya so muyi sadaka ga mafi yawansa sauran mu amfana da shi. Amma kasan a ina damuwar take?”

Bai jira amsar sa ba ya ɗora.

“Damuwar ita ce idan muka fiddo dukiyar nan ga mutane yanzu tabbas duka zai iya zama ba rabonmu ba, ƙila ma a dalilin haka a kaimu birni a ɗaure ace munyi sata ga turawa.

Dan haka mu ɓoye su zuwa nan da shekara guda a hankali muna bincikar yadda suke da yadda za mu yi amfani da su. Ka ga tunda Haadiru yana cikin waɗanda aka tura birni yin karatu ko ta hanyarsa ma samu dabarar aiki da su ko kuma mu mu tashi da kanmu mu tafi neman sanin da irin namu dabarun har mu samu Alhajin da zai mana bayani. Dan haka yanzu kai ka je da akwatin ka ɓoye a inda babu wanda zai kula da ita, nan da shekara idan ta kama muyi ƙaura daga garin ka ga sai mu yi cikin rufin asirinmu.”

Hameedu ya numfasa yana dubansa a kaikaice.

“Dabararka ta yi, sai dai ni ba zan ɓoye dukiyar nan ba saboda ba tawa ba ce, taka ce, kaine ka haƙota, haka ba a yarda da zuciya kan dukiya…”

Da hanzari Bawa ya dafe hannunsa.

“Kar ka ƙara wannan furucin, wannan dukiyar tamu ce, tare za mu rabata kai da kai, kar ka manta tare muka zo gurin nan.”

Suka yi shiru gabaɗaya suna nazari.

Sai can Hameedu ya nisa ya ce. “Ɗazun nan ka furta mini kalaman da sam hankalina bai kai ga nazarinsu ba, da ka ce ba za mu taɓa dawwama a haka ba, tabbas bawa ba zai taɓa dawwama a yadda yake ba na ƙara gasgata haka a bayan bayyanar wannan dukiyar gare mu. Wato har na fara tunanin gidan da zan gina sai ya yi takwas ɗin na Maigari a girma, shiyyar Inna kuwa sai ya yi kwatar ƙaryar nan a faɗi. Na saiwa ɗan marayana Huzaifu ƙatuwar motar shanu biyar na masa aure da tsala-tsalan mata huɗu…”

Bawa ya sheƙe da dariya yana sosa tsinin hancinsa.

“Ni kam bayan gida wata tafkekiyar kasuwar Shanu zan assasa acan wani yanki wai shi marabar Jos. Maigari da ya yi silar tone bishiyar nan garke biyu zan bashi, ɗiyar da ake nemawa maganin garke uku zan bata. Zawwa kuwa can Hindu zan tafi na samo mata zarƙaɗeɗiyar Amarya. Kai kuma idan ka kawo mini matar da za ka aura ni zan biya sadakinta da sisin zinari uku.”

Suka ƙara bushewa da dariya suna kashewa.

“Amma ba kada dama da zaka rasa da abinda zaka saka mata sai kishiya, abin fa mugun daɗi ya yi mini aradun Allah, cab! Wa yaga Zawwa da kishiya? Garmaho! Sunan wani wanzami a can haka.”
Ya furta da shewa yana dukan kafaɗarsa ta dama.

Sai da ya bari duhu ya ratsa yadda ba wanda zai ankara da shi kana ya ja amalanke ya ɗora akwatin ya zuba rairayi bisanta ya kora jakin suka yi gida. Sai dai fa tun a ƙofa ya hango yaronsa yana ta kuka, ya ƙarasa da sauri ko bai tambaye shi ba yasan jikin Inna ne kawai zai saka Huzaifu kuka a ƙofar gida. Dan haka da hanzari ya yi ciki yana jan akwatin zuwa rumbunsu ya tura ta ciki ya aza mata guntun hatsinsu kanta, ya sheƙa da gudu zuwa ɗakin Innar ya tardata kwance bakinta na fidda wani irin jini a guda-gudansa. Ya kaɗu matuƙar kaɗuwa, har bai san sa’adda ya duƙa ya sureta ya aza a bayansa ya fara falfala gudu da ita zuwa can bakin hanyarsu da ake bi idan za a cikin birni ba tare da ya bi takan yaron ba, ya sani Laure maƙociyarsu za ta shiga da shi gurinta ko ta miƙa shi ga Zawwa.

Hanyar ya miƙe yana ta gudu da ita cikin rashin hayyaci da rashin sanin abin yi, ya manta ko kwana zai yi yana gudu ba zai iya zuwa birnin ƙaryar da suke da ƙafarsa ba.

Tun yana jin numfarfashinta har ya ji tsit ba ta wani alamar motsi, cikin duhun ya samu ya laluba gefen hanyar ya kwantar da ita yana jijjigata yana kiran sunanta cikin gunjin kuka, sai dai fa daidai da yatsanta bai motsa ba balle yasa ran jin sautin muryarta. Hameedu baya da kome sama da Innarsa baya da kuma wani buri sama da ya riga ta barin duniya.

Idan kana neman uwar da bata buɗe baki ta zagi ɗanta to Inna ce, idan kana jin uwar da bata taɓa buɗe baki ta zagi ɗan wani to Innar Hameedu ce, wata irin uwa ce da babu tamkarta har a zamaninkan da suka gabata.

Su biyu tal ta mallaka sai Babansu, Allah da girmansa ya ɗauke mata Babansu Da Yawale, sai auta Hameedu da jikanta Huzaifu, kenan ga Hameedu waɗannan halittun biyu tal gare shi a rayuwarsa sai Bawa da yake jinsa Amini yake jinsa makwafin uba gare shi.

To shi wanene da zai bar ciwo ya ɗauke masa Inna da ƙarfinsa da kome irin na namiji? Ya sake rushewa da kuka yana mata wata irin jijjiga. A sannan ne ya hango hasken mota ya fito daga wani surƙuƙin jeji da wata hanya ta ratsa ta cikinsa ya dallare shi, ya miƙe da gudu ya doshi gun motar. Wanda ke tuƙin da yake gudu yake sosai bai ankara ba ya hango wani ya doso gabansa a guje, ya yi-ya yi ya tsaya abin ya ci tura gashi hanyar siririya ce har sai da ya kwashi Hameedu ya yi watsi da shi can gefe.

A sannan motar ta tsaya da kariyar wani dutse Alhajin da ke tuƙin ya fito da sauri ya haske fuskar Hameedu da fitilarsa, ruɗewa ya yi sosai ganin yadda wani ƙarfe ya shafce masa kafaɗa tana ta jini.

Cicciɓoshi ya yi zuwa bakin hanyar ganin yadda yake ƙoƙarin yin magana sai dai ya kasa, sai hannunsa da yake ta ɗagawa yana nuna masa wani guri daga haka ya sume. Da hanzari mutumin ya miƙa ya bi hanyar da yaga yana ta nuna masa anan ya tarda Innar Hameedu kwance ba alamar rai a jikinta. Hankalinsa ya ɗaɗa tashi, sai dai abinka da ƙaƙƙarfa kuma dakakken mutum haka ya ɗaukota zuwa cikin motar, ya saka Hameedu ma ya ja suka tafi.

<< Hakabiyya 15Hakabiyya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×