Shi da Oga Tunjim suka dubi juna suna sheƙewa da wata irin dariya har tsawon rabin minti. Can Tunjim ya ɗaga hannunsa sama sai ga wani ɗan ƙoƙo cike da ruwan jini ya bayyana a tafin hannun, bai yi wata-wata ba ya sheƙawa Hameedu shi ya rage ɗan kaɗan.
Ya farfaɗo da wata irin gigita ya rarumi ƙafafun Alhaji Hashim ya ƙanƙame, ya ɗago idanuwansa da ƙyar ya dubi saitin Innarsa da aka riga aka yaye zanin jikinta daga cibiyarta zuwa ƙafarta a bayyane, ya sake fisgo numfashinsa da ƙyar kafin idanuwansa su kakkafe ya daɗa sume musu.
Suka sake bushewa da dariya Oga Tunjim hadda buga ƙafa.
Alhaji Hashim ya juye masa sauran jinin ƙoƙon ya farfaɗo, ya yi azamar miƙar da shi tsaye yana jijjiga shi da ƙarfi yana masa magana da ƙarfin da ba zai taɓa gogewa cikin ƙwaƙwalwarsa ba.
“Ba fa ranta na nema ba yaro ba kuma cewa na yi ka yanko mini kanta ba ko wani sassa na jikinta ba، ka nutsu sosai kar ka zauce ko ka zauce sai fa ka yi mini aikin nan ko za ka mutu! Na umarce ka ne ka haiƙe mata ka bani maniyyinku ni kuma na samu abinda nake so! Ba Innata aka nema ba Hameedu!! Da Inna ta ce wabillahil azimu da yanzu baka sanni ba dan kuwa ba zan yi tunani ko na sakan ba zanje na haiƙe mata na ɗebi abinda nake so ko da kuwa zai zama silar tafiyarta inda ba a dawowa!!! Babu abinda nake so da buƙata sai Uwa da Ɗanta mai irin siffofin Innarka, na kuma samu, shin me kake so na jira ne? Ina son mulkin nan fiye da duk jama’ar yankinmu da matana da ‘ya’yana, Ina son mulkin nan ta yadda ban ƙi na maida kafatanin dangina sulalla ba.”
“Sule ko!!!” Hameedu ya furta da ƙarfi yana sa hannunsa ya ture Alhaji Hashim, ya yi baya yana dafe bango kafin kuma ya zame ya zube a ƙasa yana duƙawa tamkar mai shirin sujjada.
“Sule… Sulalla ko, na tuna, na rantse da mahallicina na tuna, ina da sule mai yawa sule mai ƙyalli irin wancan! Ya furta da ƙaraji yana nuna ƙirjin Oga Tunjim da ke saye da wani Hatimi na zaiba.
“Eh zinari a akwati, cikin akwatin baƙin karfe, in baku ko? Wallahi na baku, ku kwashe duka ku haɗa har da tufafinmu da sauran hatsinmu ku haɗa har dankinmu da dukkan itatuwanmu, na baku duka amma ku bar mini Innata, na baku kaina ku kasheni ku bar Innata, ku bar Innata domin mahallicinmu ku bar Inn…”
Ya yi shiru yana jin yadda suka sake kece masa da dariya, ya yi shiru a cikin zuciyarsa yana jin dama ya hangi wani abu mai tsinin da zai sokawa ƙahon zuciyarsa ko ya mutu ya huta da ganin tsiraicin Innarsa. Ya ɗaga kansa sama ya hangi wata baƙar adda a saƙale tana ɗigar jini, ya zabura da gudun bala’i ya isa gurinta ya miƙa hannu zai ɗauka ta janye daga gurin, ya ƙara miƙa hannu a kiɗime zai ɗauka ya ga ta yi tsalle ta tashi ta sauka a hannun Tunjim da ke ta dariya.
Hameedu ya sake rushewa da kuka yana bubbuga kansa jikin bangon yana durƙushewa a ƙasan gurin.
Ya sake rarrafawa yana lalubar ƙafar Alhaji Hashimu ya riƙe gam-gam!
“Ka taimakeni domin Allah karka zalunce ni har haka, ka ji tsoron Allah ka roke shi ya baka mulkin nan! Domin Allah ka ji ƙaina kar ka keta alfarmar Innata domin Allah ka ba ni wani aikin na rantse da sarkin da ya busa mini rai zan yi maka ko menene idan har ba zai taɓa Innata ba zan yi maka ko menene ko ba zan iya ba zan nemo iyawar na ɗorawa kaina. Ka ganta sanda ta samu cikin Babana ba yada ko hatsin da za ta ci na rayu, da ƙanzo, ƙanzo irin na ƙarshen tukunyar maƙwafta ta dinga ci har ta rayu, da kuma rama, rama marar tsami sai ɗacin da yafi maɗaci ɗaci ta ringa ci har na rayu. Lokacin da take da cikina hatta tafasa wasu muggan kwari sun cinye bare zogale dasu yaɗiya. A haka bayan ta haifeni har kawo i girmana Innata ba ta taɓa kurɓar ko da daddaɗan nono ba ko da kuwa cikin ludayin duma ne ba tare da ta aje mini kaso na ba. Na rantse da mahallicina ba zan taɓa iya taɓa yatsan Innata ba ba zan taɓa iyawa ba koda zan mutu, ka suturta ta domin Allah ka maida mata zaninta, zan yi maka kome koda mutuwa kake so na yi zan mutu!!!
Ya daɗa rushewa da kuka yana bubbuga kansa a jikin ƙafafuwan Alhajin.
Alhajin da ya daɗe da dakatawa da dariyarsa ya ɗago ya dubi Oga Tunjim suka haɗa idanuwa.
Ogan ya girgiza masa kai da sauri yana turɓune fuskarsa tamkar baƙin kumurcin da ya tsare gafiya ta sulale cikin raminta. Ya canja harshensa zuwa wani irin murɗaɗɗen yare ya fara masa magana.
“Hashimu na hane ka da jin tausayi! Za ka ɓata dukkan aikinka, za ka ɓata dukkan shekarun da suka gabata muna wahala. Ka tura shi ya haiƙe mata yadda muka nema, ka sani ba za mu iya saka shi yi da ƙarfin tsafi ba, dole shi da kansa zai tashi ya take ta yadda kome ya bayyana gare mu, ka sani tunda har ka riga da ka kawo su dole sun zama zaɓi ga aikinka.”
Alhaji Hashim ya rausayar da kansa yana masa wani murmushi mai kamar gaigayin ɓera.
“Ba tausayi ba ne alfarma ce ta farko ta kuma ƙarshe, alfarma irin wacce ka taɓa yi mini a wani lokaci can-can. Me zai hana tunda ya ce yana da zinari cikin akwati mu bashi wata damar? Me zai hana ba za ka duba mana wata hanyar ba. Zinari fa ya ce, wai fa cikin Akwatu, ba zai yi ƙarya ba idan bai gani ba.”
Oga Tunjim ya jijjiga kansa yana bushewa da wata mahaukaciyar dariya.
“Dukiya!!! Duk dukiyarka da tabbatuwar mulkin nan gare ka daɗi kake nema?”
Alhajin ya matso kusa da shi sosai.
“Zinari fa aka ce, kana hango darajarsa da za ta ninku a shekarun da ke gabanmu, kar ka manta wannan sassan al’ummar da muke ɗiba muna maidasu kuɗi ba daraja gare su ba ko kaɗan, ba ma suda darajar da za su yi shekarun da idan zinari ne zai yi…”
Ya fashe da dariya yana shafo ƙaton tumbinsa.
“…Ka bincika mana abinda ke yiwuwa sai ya fanshi ƙetare umarninmu da ya yi da zinarin, ka duba mana yiwuwar samun mulkina ta ɗayar hanyar da ta fara bayyana gare ka shekaru biyar da suka gabata.”
Tunjim ya tafi kai tsaye ga Innar Hameedu ya tsaya saitin fuskarta ya yi nazarinta na ‘yan daƙiƙu sai kuma ya ɗago yana sauke jajayen idanunsa cikin na Hameedu da ke binsa da kallo a firgice.
“Hamdiyya sunanta ko?”
Da sauri ya gyaɗa masa kai.
Bai ce kome ba sai juyawa da ya yi ya doshi wani ɗaki da aka rufe shi da jan labule ya shige ciki.
Hameedu ya ɗago ya dubi Alhaji Hasheemu sai yaga ya kauda kansa gefe. Jikinsa na rawa ya mike da sauri ya isa ga Innarsa ya ja zaninta ya lulluɓa mata, wasu hawaye masu ɗumi suka zubo kuncinsa ya saka bayan hannunsa ya share yana mai sunkuyowa saitin fuskarta, ya gyara mata kallabinta yana tuttura gashinta cikinsa ya daɗa naɗe gashin ya ɓoye hawayen na daɗa cika gaban rigarsa suna sauka a ramin wuyanta.
Ya tsura mata ido yana ganin yadda take numfasawa cikin natsuwa ta yiwu har da tsafi, masani dai sai Allah sai waɗannan miyagun da suke gabansa da bai san ta yadda zai yi ya tambaye su yadda suka rabo su daga asibiti cikin daƙiƙun da lissafinsa ya kasa bashi daidai. Nan ya tasa ta gaba yana kallo hannunsa ƙanƙame da nata
Daƙiƙai ɗari biyu da sittin da takwas suka shuɗe sai ga Tunjim ya fito daga ɗakin fuskar nan tas tumbatse da fushi. Ya ɗaga sandarsa ya nuna wata kujera da ke can kusurwar gurin sai ga kujerar ta taso ta kawo kanta gabansa, ya ja ya zauna yana duban Hameedu da idanuwansa suka ƙeƙashe da azabar ruɗani.
“Ungo wannan saka a yatsanka na hagu…, Wannan kwabban kuma zuba su a aljihunka”
Ya furta yana miƙa masa wani zobe mai tsananin kyau da sheƙi.
Ya bi zoben da kallo cike da taraddadi zuciyarsa na bugawa tamkar za ta fasa allon ƙirjinsa ta fito, sai kuma ya miƙa hannu cikin rawar jiki ya karɓa ya zura a yatsan. Ya amshi kwabban ya watsa a aljihun wandonsa. Ga mamakinsa sai ya ji jikinsa ya ɗau wani irin zafi gumi ya fara tattsafowa a goshinsa.
“Ka nemi da abar Innarka a nemi ko menene za ka aikata mana babu tababa ko? Shin a saboda ƙaunarka ga tsohuwar halittar da ciwo ya gama cinyeta za ka iya ba mu sabon jini irinta? Sabon jinin da kai da kanka za ka kawo shi cikinmu ka sadaukar mana da kome nasa ka fanshi kanka da na Innarka! Shin za ka iya kisa, kisa irin wanda za ka kashe da hannunka ka haƙa rami ka binne ko ka jefa gawar tsakiyar ruwa?”
Hamidu ya cire kansa sama yana jin kashi goma cikin ɗari na damuwarsa na gushewa, zuciyarsa ta bushe yo wane irin dare ne jemage bai gani ba? Awanni barkatai da suka gabata shi ne nan tsakanin duniyarsa da ta miyagu ana umartar shi da ya haiƙewa halittar daya fasa jikinta ya iso duniyar. Ya girgiza kansa da sauri yana jan jikinsa cikin ƙarfin rai ya isa gabansa ya zuba gwiwowinsa a ƙasa yana mai sadda kansa.
“Zan yi ko menene babu shakka zan iya maida ran halitta irina tamkar na kiyashi na kashe na binne har ƙonawa da babbakawa kai duk zan iya!”
Tunjim ya bushe da dariya yana buga ƙafa.
“Lalle ka shirya zama cikinmu ka kuma shirya yin dukkan abinda muka umarce ka. Dukiyar da ka ambata mana tana ina?”
“Tana gidanmu, ba tawa ba ce ta Bawa ce ya bani ajiya, ɗazu kuskure na yi dana ce muku ina da.”
“Wane ne shi Bawan?”
Ya yi shiru bugun zuciyarsa na warwarewa daga nutsuwar da ya fara.
“..Na ce wane ne shi Bawan?”
“Amini nane ina jinsa tamkar uba gare Ni.”
“To ka ɗauko dukiyar tasa ka danƙata hannun Hashimu, sa’annan dodon tsafinmu Jiji ya nuna yana buƙatar ganin wani naka a kalmashe shi ne horonka na farko. Dan haka a yanzu mun gane halittar da kake so a bayan Innarka ita ce Bawa.
Za ka ƙuntata ma shi Bawan ta hanyar kwashe dukiyarsa ka ɓace daga cikin idanuwansa mu kuma za mu kalmashe ƙafafuwansa mu rufe bakinsa ruf! Ta yadda har abada ba zai sake motsawa da kansa ba sai dai a masa..!”
Hameedu ya cire kansa sama jikinsa na rawa bakinsa na kakkarwa ya dube shi, ya fisgo numfashinsa da ƙyar yana haɗiye wani abu mai ɗacin da yake ji ya tattare masa a maƙoshi, wani zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe shi da ya tuna ba Bawa ba ne halitta ta biyu da yake ƙauna sama da kome ɗan marayansa Huzaifu ne! Hatta kuwa jijiyar da ke amsar saƙon jinin da ke kewaya sassan halittarsa abinda ta tabbatar masa kenan!!
Tunjim ya gyaɗa masa kai alamun tabbatarwa yana kallon cikin idanuwansa cike da gargaɗi.
“…Eh haka muke buƙata, ko kuma ka zaɓi ɗayan hukuncin wanda ni da kaina zan tashi a gabanka na kwaɓe na taki Inn…”
“A’a, a’aaa ‘aaaa na yarda na yarda kuyi kome da Bawa.”
Ya furta yana haɗiye ruwan hawayen da ya sauko ya zarce cikin bakinsa.
“Yauwa! Sai abu na biyu…”
Ya furta yana cire kansa ya dubi Innar Hameedu.
“…Aikin samun mulkin Hashimu ya riga ya kwaɗaitu da uwarka, idan har ana son canjawa sai dai a samu wata irinta. Sunan Innarka Hamdiyya, to muna neman yarinyar da bata kai shekaru ashirin a duniya ba da irin wannan sunan da kuma irin gashin Innarka da ratsin furfura guda biyu ko uku a gashin nata, wacce za ta soka so na haƙiƙar haƙiƙa, sai dai ka sani a karon farko wani abu na halittarka muke so ya fara ɗauke mata hankali!”
Hamidu ya gigice ya miƙe tsaye “to ni ina zan samu wannan yaushe ka taɓa ganin budurwa da furfura, ina ma zan samu wata mai sunan Innata ko a ƙaryarmu Inna kaɗai ke da sunan nan?”
“Ka daina ambata mana ƙaryarku, daga rana irin ta yau ka manta kana da gari har sai ka cika aikinmu, haka da akwai, abinda babu shi baya taɓa bayyanar mana, sai dai ni kaina ban san inda za a samu ba, abinda ya bayyana gare ni shi ne ka tafi garin Kano anan irin abinda muke so yake. Kano kuma birni ne na mutane masu ilimi ta yiwu wacce za ka samo tana da ilimi ko kuma tana son mutum mai ilimi dan haka dole ne ka fara yaƙar danƙararran jahilcin da ke cikin kanka. Idan ka kawo dukiyar nan Hashimu zai baka gidan da za ka zauna kai da Innarka da duk wanda kake so a danginka. Za ka tafi Kano akwai Yaronmu Maɗaci da zan haɗaka dashi zai kai ka gurin wanda zai koya maka karatu da rubutu da Ingilishi a cikin shekara guda, kuna yi kuna bincika mana mai sunan Innarka. Idan ka samu muna buƙatar da ka shiga jikinta sosai ta yadda za ta ƙaunace ka sama da iyayen da suka haifeta, za ka canja suna za ka canja sunan gari za ka canja kome naka. A bayan ka nuna a cikin ranta a ranar da shekarar (1995) ta tasarma ƙarewa zan baka wani farin ƙyalle da za ka bata ta yi ƙunzugu da shi da yardarta. A bayan ta maida maka ƙunzugun ne idan na yi amfani da jinin al’adarta ita kuma za ta kwanta ciyo mai tsananin da zai kaita kushewarta. To ka ji aikinka, za ka ba mu Innar taka ko kuwa ka yarda ka kawo mana yarinyar da muke nema?Kana da wata damuwar da za mu magance maka? Ka riga ka zama namu dole mu tattauna da kai cikin sukuni.”
“Na yarda! Zan yi kome dan ganin na cika burinku. Sai dai Innata, naga shekarun da yawa ya samun lafiyar Innar tawa.”
Hashimu da ke gefe ya bushe da dariya. “Yaro ɗan Inna! Kar ka damu, a ranar da ka kawo mana dukiyar Bawa muka kalmashe shi ni kuma zan ɗau Innarka da kai kanka mu tafi Hindun kafin ka fara yaƙi da jahilcin…”
Tunjim ya karɓe.
“Wannan zoben na hannunka kuma sai yana jikinka za ka iya jin kiranmu idan muna buƙatarka. Waɗannan tsabobin kuma a jikinsu za ka yi fitsari dan ka iso nan inda muke. Tashi ka tafi inda dukiyar take, shafa zoben da ƙarfi da niyyar ɓacewa za ka ganka a cikin ɗakinku. Ka yi gaggawar dawowa nan inda kake a bayan ka kwaso duk wani abin buƙatarka, kar kuma ka yi sallama da kowa idan kana son ko ƙuda kar ya taɓa Innarka.”
Hamidu ya shiga jijjiga kansa da sauri yana shafa zoben hannunsa da niyyar ɓacewa.
Ga mamakinsa da kuma gushewar tunaninsa sai ya ganshi tamkar walƙiya ya bayyana a tsakiyar tubalin gadon Innarsa.
Ya mike tsaye a ɗimauce yana waige-waige yaga dai tabbas a cikin gidansu yake, ya leƙa waje da sauri yana mai ɗaga kansa sama yaga yadda dare ya kai tsakiya. Ya sharce gumin da ke ta tsattsafo masa ya juya ya fara bincikar ‘yan kayayyakin Innarsa da nashi da na maraya Huzaifu yana cusawa cikin wani buhu. Ya haɗa tsaf sai kuma ya fita lalubar Huzaif ya sani yawan kwanakin da ya kwashe bai garin dole Bawa zai ɗauki yaron, dan haka kai tsaye gidan Bawan ya dosa.