Skip to content
Part 19 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Ya daɗe tsaye daga jikin kararen da ke kewaye da gidan yana hango Bawa da ke barci a farfajiyar gurin. Daga can gabansa bisa wani ƙaramin gadon icce Huzaifu ne, sai Hadiru kwance bisa tabarmar kaba a ƙasa, ya hanga kallonsa ga babbar bukkar da ke can gefe ya sani Zawwa na cikinta tana bacci. Ya baro jikin karan yana saita takunsa a hankali jin yana fidda sautin rumurmushewar busassun ganyayyakin bishiya. Ya cigaba da tafiya sannu yana kiyaye duk wani tarko da ya san Bawa ya kafa dan kama ɓarayi, ya tsallake wani gulbi da duk rani baya rasa ruwa cikinsa ya isa ga farfajiyar gidan ya ƙarasa ga makwancin Huzaif ya sunkuya ya ɗauke shi ya aza shi bisa kafaɗarsa.

Yaron ya buɗe baki zai yi kuka ya yi azamar rufe masa bakin yana lalubar kunnensa ya masa raɗa, “Yi shiru ni ne, Arɗonka ne ka ji.” Yana jin yadda ya sauke wata irin ajiyar zuciya wadda baya raba ɗaya biyu ta zallar kewarsu ce, sai kuma ya maida kansa bisa kafaɗar ya yi luff abinsa.

Ya ɗaga ƙafafunsa da zummar barin wurin wani abu ya fusge shi yana sakashi saita kansa ɓangaren da Bawa yake kwance. Ya tsura masa idanuwa  ƙirjinsa na kumbura na saka shi jin kamar ya tafi ya afka rijiyar da ta fi kowacce rijiya zurfi a yankinsu. Abin ya ci gaba da fisgarshi har ya taka ya isa ga Bawan ya duƙa tallafe da Huzaif yana kallon fuskarsa. Hawayensa da yake ta ƙoƙarin maidawa suka sauko suka biyo ta kuncinsa zuwa haɓarsa suna ɗiga a fuskar Bawan.

Yana ganin sa’adda ya yi wata irin jijjiga tamkar mai mafarki bakinsa na motsawa. Ya yi azamar miƙewa yana jin ƙaunar Bawan da kewarsa na sake zauna masa inda baya zaton zasu taɓa barinsa ya kwana lafiya.

Ya tsinewa ciwon da ya saka shi kwasar Innarsa cikin dare ya yanki daji da su, ya yi Allah wadai da rashin tawakkali irin nasa da ya kasa zuwa da Innar tasa gurin Bawan a lokacin. Ya sani shi Bawa yana da hanyar da za su nemi taimakon maigarinsu ya basu motarsa ta ɗiban kayan gona su kai Innar tasa asibitin cikin gari. Ya juya ya yi taku guda ya sake waigowa yana kallonsa ji yake shi ke nan fa ƙila har abada shi da Bawa dama karkararsu bakiɗaya. Ya ɗaga ƙafa da ƙarfin niyyar bai sake waigowa a sannan ne ya ji kici-kici ya waigo da sauri ya kalli Bawa ya tashi zaune a tsakiyar shimfiɗarsa, suka zurawa juna ido cikin hasken farin watan da ya fara shigewa lungun duniya, yana kula da sa’adda idanuwansa suka ƙara girma ya sa hannu ya mutsittsika yana ci gaba da kallonsa. “Hameedu kai ne? Ba wuta jikinka? Yanzu na yi mafarkinka ka faɗa wani rami cike da wuta, a’aa aski kayi ne? Ina Innar? Ina kuka shige ne,. Ka tada hankalinmu dan ma Yautai ya ce mana yaga kamar kai wai a wani gari…” Kalmomin suka fito a jejjeren da ya saka Hameedu juyawa cikin azama a cikin kunnuwansa yake jin kuwwar muryar Tunjim inda yake jaddada masa kar ya yi sallama da kowa har ya isa gare su idan yana son ko ƙuda kar ya taɓa Innarsa. Ya fice daga ilahirin gurin da gudu yana jin Bawa ya biyo shi yana kira sai dai bai waigo ba. Ya ci gaba da gudu rungume da Huzaif yana dosar hanyar jeji dan ma kar ya bishi gida, Bawan ma bai fasa bin shi da ya tsaya ba har sa’adda ya ji Bawan ya saki wani irin gigitaccen ihu yana faɗin, “Hameedu ƙafata, cikina, bayana zai karye!!”

Hameedun ya yi turus yana jin tamkar an saka ƙaton dutse an fasa wani abu cikin zuciyarsa. Ya waigo yana hango duhun Bawan da ke kwance cikin ƙasa nesa kaɗan da shi. Ya runtse idanuwansa zuciyarsa na Ingiza shi da kar ya tafi ya bar Bawa zai zama butulu maci amana, wani abu kamar walƙiya ya gifta ta idanuwansa hasken ya haska masa sa’adda ya samu Innarsa kwance a deɓe rabin tufafinta, kuwwar maganar ya haiƙewa Innarsa na cika dodon kunnensa. Ya fashe da kuka mai ƙarfin da ya saka shi toshe bakinsa da ɗayan hannun ya kuma razana Huzaifu da ke kwance bisa kafaɗarsa.

“Baba Arɗo kuka kake?”

Muryar yaron ta ratsa kunnensa ya ƙanƙameshi da ƙarfin da yake jin tamkar zai ruƙurƙusa ƙasusuwan ƙirjinsa, ya juya yana shigewa cikin duhun bishiyoyin dake gabansa sa’ilin da yaji sautin tafiya da maganganu na isowa muhallin da Bawa ke kwance. Ya shige tsakiyar gurin yana mai murza zoben hannunsa ya ɓace ya bayanna cikin ɗakinsu ya ɗauki kayan daya haɗa ya isa ga rumbunsu ya buɗe ya jawo akwatun nan waje, ya riƙe hannun Huzaif yana dubansa yana duban kayan dake gabansu.
“Baba tafiya za mu yi? Ina za mu je?”

“Duniya…Duniyar da za mu halaka Huzaifu!”

Ya furta masa yana saka ɗan yatsansa guda ya ɗauke kwallar da ta taru a gurbin idonsa!

“Wai menene? Wa ka biyo? Bawa lafiya kuwa kalli jikinka, kai Innalillahi wa inna illahir raji’un, kaga kana naɗewa, kai! kai!! Haadiru duba kaga waya taɗe shi ya faɗawa ‘ya’yan Aljanu…”

Muryar Zawwa ke nan cikin kiɗima tana tallafe da Bawa da duk bayan sakanni wani abu na halittarsa ke naɗewa ya motse tamkar ƙosan da mota ta bi ta kansa. Ya ɗaga hannunsa guda da ƙyar yana nuna mata saitin da Hamidu ya yi, ta bi hannun da kallo ta hanga ta daɗa hangawa ita bata ga kowa ba sai duhun bishiya.

“W..wa.wane ne wai ka mini magana mana!!?”

“Haaaaam!” Ya yi shiru yana jin tamkar an saka wuƙa an datse rabin harshensa.

“Hamidu wai shi ka gani yana ina?”

Ya gyaɗa kai, ya sake gyaɗa kan bakinsa na komawa gefen da ya tabbatarwa Zawwa Bawa ya daina magana. Ta bi bakin da kallo a gigice sai kuma ta saki wani irin gigitaccen ihu sa’ilin da taga hannunsa da ke tsaye saitin da yake nuna mata shi ma yana naɗewa har ya yankwane ya faɗo sharaf jikinta tamkar burodi a cikin ruwan shayi, mutanen da ke nesa kaɗan da su suka fara fiffitowa daga bukkokinsu suna doso nan inda suke jiyo kururuwa, bata gama watsttsakewa daga wannan ba ta ga idanuwansa sun juye zuwa fari tas ya sume musu nan gurin. Ita da Haadiru da ke ta kiran wayyo Allah suka rufar masa suna kiran sunansa suna jijjiga shi da duk ƙarfin da suka mallaka. Wani Dattijo da ya riga kowa isowa ya yi azamar janye Haadiru daga jikinsa, ya yi salati ya sanar da ubangiji sa’ilin da yaga makwafcinsa ya naɗe tamkar Alkaki, ba shiri shi da sauran mutanen suka goyawa Haadiru shi suka doshi gidan Kakan Zawwa da yake da tambarin sarautar laƙanin magunguna.

<< Hakabiyya 18Hakabiyya 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×