Wannan kome da zai farun ne ya fi ɗaukar hankalin Zawwa har ya sakata dafe ƙirji tana sallallami, sai yanzu ta fahimci kome, wato Zinarin da Bawa ya ce mata ya tsinta a jeji ashe Hameedu ya bawa ajiya, shi kuma saboda mugunta ya ɗauke duka ya gudu ya kuma nakasta shi dan kar ma ya tafi nemansa, ta tsinewa Hameedu ta la’anci dukkan ahalinsa, ta furta ta sake nanatawa da babbar murya kafin ta bar duniya sai Hameedu ya yi mutuwar da ko kare ba zai kusanci gawarsa ba, ta dubi Haadiru ta maida kallonta ga Bawa da wasu hawaye suka kwaranyo masa ta gefen idonsa, ai sai ta ɗora hannu aka ta fasa wani irin ihu da ya jawo hankalin jama’ar da ke can waje, cikin ihun kuka take faɗin Hameedu ne ya yiwa Bawa sata ya nakasta rayuwar shi ya gudu, tun mutane basu fahimci kome har suka fara fahimtar abinda ke faruwa. Nan fa gari ya ɗauka da wannan labarin har zuwa ake ana kallon Bawan ana jajanta masa.
Bayan Kaka ya gama rarrashinsu ne ya ce mata a maida Bawa gida ta ci gaba da kula da shi, shi kam ya gama nasa. Hankalinta ya daɗa tashi ta fara roƙarsa da ya warkar da Bawa ya kuma duba mata shi Hameedun tana son gigita tasa rayuwar da hannunta.
Kakan ya nisa cike da alhinin abinda zai faɗa mata yana dubanta.
“Ku tafi kawai babu wani abu da za a iya yi yanzu, na faɗa miki wasu irin miyagu ne da duk daɗewata cikin duniyar nan ban taɓa ji ko ganin irin aikin su ba. To amma akwai wani abu… Yanzu ku tafi karki ƙara batun neman magani ko a guri nane har sai wata irin wannan na tsakiyar zafi ya zagayo. Ki dawo nan zan ga abinda ke yiwuwa.”
Ta yi shiru tana miƙewa ta isa ga Bawa ta ɗago shi tana ƙoƙarin goya shi Haadiru ya yi saurin matsowa ya duƙa dan ta saka masa shi, sai dai bata ko dube shi ba haka ta samu ta goya Bawan ta ja kallabinta ta ɗaure shi.
Zuciyar tsoho ta karye, ya yi tsai yana kallon jikar tasa yana ƙissima ƙananun shekarunta da yadda za ta ƙarar da ƙuruciyarta cikin jinya. Tausayinta ya cika zuciyarsa, ya tuna jikar sa ce fa mafi soyuwa gare shi cikin wannan halin, sai ya matsa gareta yana mai sanya busassun hannayensa ya riƙo nata hannun.
“Zai warke, na miki alƙawari zai warke ta kowane hali, ke dai ki yi dukkan abinda zan umarce ki da yi. Da sannu za ki ga bakinsa ya buɗe har ya ce miki “Zawwa! Ƙaunarki ta cika dukkan ruhin.”
Murmushi ya suɓuce mata ta ja lullubinta ta rufe fuskarta. Sai kuma ta cakuɗa fuskar tana daɗa saɓa yankwanan nan Bawan da ke bayanta. Akwai wani abu da take tunanin faruwarsa har a yanzun da take gabansa ba ta cire tsamannin ba zai faru ba musamman idan ta yi duba da tarin furfurar da ke saman kansa da bushassun hannayensa.
Tamkar yana karantar abinda ke ranta ya ce mata.
“Da saurana, da sauran lokaci, ko dan alƙawarin da na miki ba zan kusanci mutuwa ba sai na cika shi. Kar ki manta ko sanda aka haifeki mutumin da ya haifi Babana yana nan da ransa.”
Ta sunkwi da kanta tana ƙoƙarin zura takalmanta ta fice, sai take jin kashi sittin cikin ɗari na damuwarta na dulmiyewa a wani guri da zai wahala ya dameta.
Makwanni suka shuɗe watanni suka girgije har zuwa watan da ya ƙididdige mata, a tsakiyarsa a wata farar safiya ta masa sakamako goye da Bawa da ya fara kyan gani sai dai fa kome nasa na nan ba wani cigaba.
Ya dubeta yana girgiza kai bayan ya zana ƙasa ya shafe ya daɗa zanawa ya shafe, ya miƙe ya fita ita ma ta miƙa ta biyo bayansa jikinta na bari. “Ni na san ba za ki haihu ba, Maigidanki ya san ba za ki haihu ba duk da nasan bai yarda da zance na ba game da rashin haihuwarki, amma a yanzu lamarin warkewarsa ya nuna abinda za ki haifa shi ne maganin Bawa shi ne maganin Maha’inci Hameedu!”
Zawwa ta gigice tana jin sabuwar karaya na mamaye ta. Ta hangi Bawa da ke can ɗaki da a kullum kwanan duniya sai ta zubar masa da hawaye ai sai ta rushe wani irin kuka, idan ba zina ake so ta yi ba ayi mata tambarin dan mijinta ba lafiya ta nemi maza ta ina Bawa zai mata ciki? Kome nasa aka lalata har kuwa halittarsa ta ɗa namiji.
“Kar ki karaya mana, kome zai iya faruwa a duniyar nan tamu har abinda baka tunanin zai faru sai ki ga ya faru. Tabbas maganin Bawa na cikin haihuwar da za ki masa ta ɗiya mace. Bansan yaushe ba, ban kuma san ta ya ya ba, amma ki tafi ki ƙara jiran wani watan da zai zagawo irin wannan ki dawo da shi, na miki alƙawari a sannan za mu ga yadda za ki haihun, ta yiwu wani ilimi ya zo mini ki ga ya samu ya take ki ko a dare ɗaya ne.”
Ta tashi ta tafi, ta sake jira har wannan shekarar, wannan karon sai da watan ya tasarma ƙarewa a wani yammaci ta nufi gidansa.
Da sassauci a fuskarsa ya dube ta bayan ya tashi ya ja asabari ya rufe ƙofar ɗakin nasa, “Na ga yadda za a yi ki samu haihuwa, amma akwai haɗari kaɗan sai dai idan za ki kiyaye babu kome…” Ya nisa yana sa tsinke ya sakace mataccen goron da ya maƙale cikin haƙoransa.
“Idan har kina so ki haifi ɗiya mace, sai kin yanko hantsar mace mai tsohon ciki da gashin kanta, da shi za a yi miki siddabarun da za ki haifeta. Idan har kina son Bawa ya warke, sai an yi masa wanka da ruwan farko da aka wanke wannan jaririyar, a take zai warke…”
Ta miƙe jikinta na mazari, “na san inda za a samu hantsar, yau kwana uku wata mai ciki ta mutu a can ƙasan rafi, bari na je na nemi danginta su nuna mini kabarinta! Wallahi ka ga dai da wuƙata jikina, idan ma babu kaifi ka ara mini taka, ni kuwa yanzu zan tafi in yanko maka duk abinda kake so, na sani zuwa dare Bawa ya warke, gobe da safe mu tafi gona tare.”
“Ke!…” Ya mata tsawa ganin kamar ta fara zaucewa.
“Da yammacin nan da maza ke dawowa daga gona za ki tasamma shiga maƙabarta dan baki da hankali? Sannan dama shi cikin a daƙiƙu uku ake yinsa ya girma sa’a guda ki haihu a sakanni uku ko? To kuskure ne idan kika je kika buɗe kabarin da ba na mace mai ciki ba, kuskure ne kuma idan kika bari wani ya ganki a yayin da za ki shiga cikin maƙarbartar, babu lefi idan kika haɗu da wani cikin maƙarbartar, babu kuma lefi idan za ki aje rawar kanki ki jira zuwa lokacin da zai bayyana gare mu na baki rana, nan da shekaru biyu masu zuwa ki dawo.”
Ta koma daɓas ta zauna tana jin zuciyarta na narkewa, ko’ina na halittar jikinta na girgiza.
“Ba zan taɓa yafewa Hameedu ba! Wallahi ba zan yafe ba!!”
Ya ja hular kabarsa ya rufe fuskar yana ci gaba da sakacensa.
“Ni ma bance ki yafe masa ba, bance ba jikata!”
Haka ta ci gaba da jira har zuwa shuɗewar shekara, a wata safiya suka wayi gari shanyaryar kafar Bawa guda ta kumbura suntum ta tsattsage wani irin ruwa mai wari na fita daga jikinta, tun yana ihu yana kiran wayyo Allah har sai da ya yi shiru sai ruwan hawaye kawai dan azabar raɗaɗi, hankalin da yawan mutanen ƙaryar ya tashi, mata masu karyayyar zuciya haka suke biyo layin zuwa ganinsa suna zubar masa da hawaye suna tirr! Da halin Hameedu da ake ta ƙishin-ƙishin yana ƙasar turawa shi da ahalinsa. Ganin ciwo nata ƙaruwa dan wasu tsutsotsi murtaka-murtaka suka fara fitowa yasa maigari tada yaronsa da mota da kudin magani aka ɗauki Bawa zuwa garin Bauchi wani asibitin ƙashi.
Sai dai fa likitan kallo guda ya yiwa ƙafar ya girgiza kai yana tur da halinsu da suka bar ƙafar ta ruɓe, sai da Zawwa ta ce masa duka ciwon kwana guda ne tukunna ya yi shiru, ya gama aune-aunensa ya faɗa mata babu wani hal dole sai dai a yanke ƙafar.
Ta haɗiye abinda ya riƙe mata maƙogwaro, ta dubi Bawa da jijiyoyin kansa suka fito burɗa-burɗa tsabar azaba, ta juya busassun idanuwanta da babu ko ɗigon hawaye ta ce masa a yanke.
Sai bayan an yanke da sa’a guda sai ga Haadiru ya zo mata da saƙon Kakanta, ya ce ko da ance a yanke ƙafar karta bari, zai warke a wasu ƙididdugun lokuta, ta karbo masa abinda zai rage masa zugi kawai.
Ta girgiza kanta wata kwalla guda ɗaya na sauko mata. ” Bakin alƙalami ya bushe Haadiru, bazan iya ba, ba zan iya ganinsa cikin wannan azabar ba, babu wani abu da zai hana masa jin raɗaɗi idan ba yankewar ba.”