Haka suka ci gaba da jinyarsa har zuwa lokacin da dungulmin ƙafarsa ya warke. Bayan shuɗewar wasu watanni shekaru biyun daya bata suka cika.
Ta tafi gare shi ƙirjinta na bugu akowane taku kasancewar watanni biyu kenan kakan nata na fama da zazzafar jinyar da sau tari bai iya ko tashi sai an tada shi.
Ita ta tashe shi ta jingina shi da bango ta dau mafici ta fara masa firfita ganin yana ta gumi duk da da asubar ranar ruwan sama ya ɗauke.
Ya dubeta fuskarsa yalwace da murmushi. “Tun shekaran jiya na gama haɗa aikinki. Kamar yadda na faɗa miki, idan har kina so ki haifi ɗiya Mace, sai kin yanko hantsar mace mai tsohon ciki da gashin kanta, da shi za a yi miki siddabarun da za ki haifeta. Idan har kina son Bawa ya warke, sai an yi masa wanka da ruwan farko da aka wanke wannan jaririyar, a take zai warke…”
“Sai dai ki sani wanda ya rasa ƙafa ya rasa kenan har abada tunda an riga da anyi kuskuren yankewa, zai dai warke da ga nannaɗewar da ya yi, zai kuma buɗe baki har ki ji ya ce miki “Ina ƙaunarki Zawwa!”
“Yar da kika haifa ita ce za ta rama miki dukkan abinda kika rage, ita ce za ta juya miki Hameedu Siddiqu da dukkan Ahalinsa a tafin hannunta yadda kika kasa har kuwa zuwa kushewarsa. Dan haka ki je a daren yau ki haƙe kabarin da yake na farko daga ɓangaren hannun damarki, ki tone shi za ki tarda mace mai ciki a cike. Idan kika wuce yau, kin wuce burin rayuwarki kenan har abada ba ki ƙara samun wannan damar. Shekara biyun da muka yi muna jiran wannan ranar ta tashi a tutar banza da wofi, kar ki tsaya, ki tafi, ko da mahaifinki ne zai mutu a yau, kar ki tsaya, ki tafi! Har kuma ki je ki dawo kar ki juya, idan kika juya kar ki yi kuka da ni, ki yi da kanki, na gama taimakonki Zawwa! Na gaji!!Sosai na gaji!!!”
Ta sadda kanta ƙasa hawaye na jiƙa gaban rigarta, duhun daya lulluɓe zuciyarta na yayewa, sai take ji kamar shi ke nan duk wata damuwarta ta duniya ta ƙare a yau. Ta miƙe tana kallonsa cikin ido tana tuno duk wata ƙuruciyarta da ta yi tare da shi, sai take jin tamkar bankwana take yi da shi, tamkar gajiyarsa na nuni da kusantowar mutuwarsa. Ta juya ta fara taku sai kuma ta tsaya tana waiwayowa.
“Amma ta ya ya zan gane kabarin mace mai ciki a cikin jerin kaburburan?”
“Wai kin manta na ce miki na farko? Kin manta yau shekara biyu kenan da na ce miki ki dawo zan baki rana? Ki tafi kawai, ki je ga kabarin da na wassafa miki.” Ta sake juyawa har ta kai bakin ƙofa ta ji wani zancensa mai wahalar fahimta ya shiga kunnuwanta.
_”Kin ga, kome kika tarar cikin kabarin ki yi amfani da shi naki ne, halalinki ne Zawwa!_”
Ta waigo ta kalle shi yana cije baki yana mata murmushi, ta ji tabbas akwai wani abu da yake damunsa ya ɓoye mata. Ta ci gaba da kallonsa yana mata murmushi har ya sake buɗe bakinsa.
“Kina ta gaggawa baki ji maganar da nake so ki kiyayeta ba har mutuwarki, ko da rayuwa za ta tsaya mini iya nan da ba zan samu ganin abinda za ki haifa ba. Ina umartarki da ki sakawa yarinyar suna *Haƙabiyya!…”*
Ya yi shiru ganin yadda take motsa laɓɓanta sai dai mamaki ya hanata furtawar.
“Eh ki saka mata wannan sunan, shi ne sunanta, idan baki saka mata shi ba tabbas Bawa zai warke amma ba za ta haɗaki da Hameedu ba, ba za ki ƙara ganin Hameedu ba! Sai dai, idan wani ya tambaye ki koda kuwa maigidanki ne, kar ki faɗa masa ni ne na ce miki kisa sunan, ce masa matata Habi da ke kushewarta ke son sunan ke kuma kika mata alƙawarin sakawa duk ɗiyar da za ki haifa! Ungo wannan!”…
Ya furta yana miƙa hannunsa da ke rawa can gefensa ya zaro wani shantu ya miƙa mata ta taho ta amsa a sanyaye.
“Ko da wani zai ganki a yayin da kike aikinki a maƙabartar, wanin da kike tunanin zai iya cutar da ke ko ya fallasa ki, akwai wasu kwayoyi guda biyu a cikin shantun, ki bashi wacce ke da launin baƙi ya haɗiye. Idan duka duniya za ta taru babu wanda ya isa ya buɗe masa baki dan ya bada labarinki sai ni, sai kuma farar kwayar da ke cikin shantun. Dan haka ki masa kyakkyawar ajiya!”.
Ta juya tamkar waccar kunkuru ya shigewa ƙafa ta fice daga gurin. Shi kuma ya jawo hular kabarsa ya lulluɓe rabin fuskarsa da ita!.
****
Hameedu…
Shi Hameedu ko da ya sake shafa zoben ya ɓace tare da Huzaif da dukkan sauran kayan, a tsakiyarsu Alhaji Hashim ya bayyana.
Oga Tunjim ya murtuke fuska ganin yadda ya yi wuri-wuri tamkar ƙadangare cikin tukunya yana ƙara ƙanƙame yaron jikinsa, sai kawai ya miƙa masa hannu alamun ya bashi, kafin ya motsa bakinsa ne Hameedun ya yi wani irin yin baya a birkice ya ci karo da shirgin kayansa sai gashi ya hantsila kansa ya bugu da wata kujera kafin kuma ya yi zaman daɓaro a ƙasan, Huzaif da ke kafadarsa ya ɓingile gefe tamkar wanda baya numfashi, hakan ne yasa ya manta da nashi zafin ya hau girgiza yaron cikin fidda tsammani.
“Zoben da ke hannunka nake umartarka da ka ba ni ba yaron ba. Babu abinda zan yi da yaron da bai shekara goma ba balle naka da nasan ko shayi ba a kai ga yi masa ba, kar kuma ka damu da rashin farkawarsa ba zai farka ba har sai ya fita daga nan, haka sirrin gurin nan yake, ban kuma yarda yaron da ya haura shekaru biyar ba zai iya tuna wani abu na yarintarsa ba a bayan girmansa. Ka kwantar da hankalinka, in dai za ka cika dukkan alƙawarinmu na rantse maka da farcen mai girma Jiji babu wani mahaluƙin cikinmu ko a waje da zai cutar da kai, ka manta kome na rayuwarka ta baya ka kalli gabanka, za mu baka kyakkyawar rayuwa da za ka yi ta Babu sirkin talauci balle wayyo duniya, za ka rayu da mahaifiyarka cikin jindadi da walwala, kai idan ma baka son dukiya irin tamu ni da kaina zansa Hashimu ya baka wani kaso daga cikin dukiyar Aminin naka, kai dai ka zamo mai biyayya ka kuma kiyayi cin amanarmu, cin amanarmu daidai take da raba kan yaron nan da gangar jikinsa da kuma keta alfarmar mahaifiyarka da zan yi…” Ya yi shiru yana ƙara takunsa gaban gadonta ya miƙa siririn hannunsa mai zanen tafka-tafkan jijiyoyin girma ya shafo haɓar Inna zuwa kuncinta zuwa kwantaccen gashin gaban goshinta da furfura ta fara ratsawa, ya waigo ya kalli Hameedu da ya runtse idanuwansa jikinsa na wani irin kakkarwa.
“Hameedu…Na daɗe rabona da aure!..”
Ya furta masa wani bushasshen murmushi na bayyana saman fuskarsa.
“Na kuma daɗe rabona da mace…”
“…Ba ni zoben.”
Ya ƙarasa yana mai sake miƙa masa hannun.
Hameedun ya jijjiga kai bayan ya haɗiye wani kakkauran yawu da ya tarar masa, sai ya zare zoben a hankali ya miƙa masa idanuwansa na rau-rau, ga mamakinsa sai sannan ya ji mugun ciwon da inda ya ƙume a kansa yake masa.
Yana gani Tunjim ya buɗe bakinsa ya jefa zoben, bayan wasu sakanni ya fiddo zoben ya sake miƙawa Hameedu shi. “Maida shi hannunka, yanzu ba za ka sake ɓacewa da shi ba, sai dai dashi ne za ka dinga jin duk kiran da za mu yi maka, sai ka yi amfani da wannan sulallan domin isowa gare mu…”
Jin wani ihu yasa suka waiwaiya da sauri suna kallon yadda yake ɗaga tarin zinarin cikin akwatin yana watsawa sama yana ihu. ‘Dama ya sani babu tashin hankalin da zai sa mutumin ƙauye faɗar ya ga dukiya alhalin bai ganta ba. Ya sake watsa sulallan sama tamkar taɓaɓɓe, duk matsiyatan kuɗin da yake da su na zallar tsafi da yaga waɗannan ji yake tamkar bai taɓa mallakar kome ba, ya sani ba dan Jiji da ke buƙatar ganin an baƙantawa abinda Hameedu ke so ba da bai taɓa ganinsu ba, sai dai ba za su gane amfanin dukiyar gare shi ba, babu ma mai taɓa fahimtarsa koda ya furta, lissafinsa daban yake, irin na mutanen da suka isa sha tara ne ashirin ɗin tagagara, duk zunubi zunubi ne, sai dai fa a mizaninsa da dai ya ɗau dukiyarsa da ya assassa da wata gaɓa ta halittar ɗan Adam (rai), ya fidda Zakkar da ake takura shi ya yi, da sadaka ga ‘yan maular da ke cika ƙofar gidansa da ginin masallacin da ya sha kai linta yana dawowa ya zube, gwara ya yi da dukiyar da ya kwata ta karfin tsiya ba tare da ya fitar da wani rai ba ko jini! Haka, da ya dawwama da dukiyar da ya sameta yana daga bisa gadonsa a bayan ya salwantar da jariri mafi soyuwa a ransa da amaryarsa ta fara haifa masa, gwara ace yana da wata dukiyar da yake juyawa a can gefe, wadda babu ɗigon jinin kowa a cikinta!’ Ya buɗe bakinsa a zahiri ya ce, “Tunjim, ba za ku fahimta ba, ba za ku taɓa fahimtar lissafina ba, amma ku kira ni da kome a kan dukiyar nan na ji na amsa, ba za ku fahimta ba ne ko da kwakwalwarku zan buɗe na zuba muku abinda ke tare da ni.” Sai kuma ya bushe da dariya yana jijjiga kai, Tunjim ya murmusa kawai ya shige wani siririn ɗaki. Shi kuma ya kai kallonsa ga Hameedu fuskarsa cike da fara’a. “Na gama magana da Amintaccen likitana da yaro na da ke harƙallar visa, za ai mana kome na tafiya can Indian nan da sati biyu masu zuwa. Dan haka yanzu mu tafi ka ga gidan da za ka zauna.”
Hameedun ya waiwaya a sanyaye yana kallon Innarsa.
Hashim ya bishi da kallo yana murmushi.
“Da ita za mu tafi, ba zan barwa mayunwacin Dattijan nan Innarka ba, likitan shi zai ci gaba da kula da ita har a tafin. Kai dai mu tafi, yadda baka san yadda ta zo nan ba haka ba za ka san yadda za ta tafi gidan ba.”
Daga haka ya juya ya fita, Hameedun ya tallafo yaronsa da buhun kayansu ya bi bayansa. Shi dai yaga sun bi wata ƙofa, sun ɗaga wani farin labule sai ya ganshi a wani jeji mai yawan fili da duwatsu manya, ya ga sun ci gaba da tafiya, can sai ga wani ya faka a wata ƙatuwar baƙar mota, ya ga Alhajin ya shige cikinta, shi ma ya bishi, daga haka suka ci gaba da tafiya, ya ga suna ta wuce wasu gonaki har suka shiga wani gari mai yawan benaye da tituna miƙaƙƙu, suka shiga wata unguwa mai ɗaiɗaikun gidaje suka faka a wani gida da yafi duk gidajen unguwar tsaruwa. Suka shige cikin gidan zuciyar Hameedu tamfatse da tsoro, shi fa ko a labari bai san da Aljanna irin wannan ba a duniya bare ya kwatanta ganinsa a zahiri, ya bi manyan ɗakunan da ke luntsume da gadaje da Alhajin ke ta nuna masa da kallo, a maimakon ya ji nutsuwa sai yake ji zuciyarsa na daɗa karyewa da lamarin nasu, ya tuna Bawa, ya tuna yadda a kullum duniya rana ke ƙarewa saman kansu ba tare da sun tsinana kome, sai ya ji dama yana tare da shi a yanzun, dama zai iya roƙar Alhajin ya kawo masa Bawa, Bawa bai hana shi dukkan abinda suka saka shi, sai kuma ya tuna hatsarinsu, ya tuna duk wannan daɗin da suka bashin shi Bawan yafi shi kwanciyar hankali, shi fa kamar yana ƙarshen wani dogon dutse ne da aka dasa shi a tsakiyar teku, taku guda tal! Da zai yi zai afka ciki ya rabu da rayuwarsa a manta da babinsa har abada. Sai ya ji kome na gurin ya koma masa baƙiƙirin, sai dai mamakin mutanensa bai gama kashe shi ya rufe masa baki ruf ba sai da Alhajin ya fito da wani mukulli mai tarin ‘ya’ya ya ce masa, “Wannan gidan naka ne, mallakinka ne ko da aikinka bai yiwu ba ina burin ka mutu a cikinsa. Nan ne garin Abuja, nasan kana ji a labari.” Sai kuma ya masa murmushi, murmushin da har ya rabu da shi rabuwa ta har abada bai sake ganin ya masa shi ba!
Abin ka da naira, cikin lokaci ƙanƙani aka gama hada-hadar tafiyarsu suka tashi zuwa ƙasar India. Kasancewar likitan Alhaji Hashim ya gama kome na asibitin yasa nan da nan aka karbi Inna, anan likitocin suka duƙufa kanta dan ganin sun ceto zuciyarta daga halin ha’ulin da take ciki.
A ɗan zaman da suka yi na watanni biyu a ƙasar Hameedu ya fara naƙaltar rayuwar, dan kuwa Alhajin kafin ya baro su ba haka ya bar shi ba sai da ya shiga ya fita ya samo masa wani Albino mai kafirar kwanya ya fara koya masa rubutu da wasu daga kalmomin turanci, abin da ya koya haka zai zauna ya koyawa yaronsa. Abinka kuma da mutumin da dama ya iya rubutun allo da karatu, nan da nan sai gashi ya fara gogewa ya fara fahimtar abubuwa da yawa na rayuwar kanta.