Wani abu mai ɗaure kai shi ne, tunda Inna ta fara warkewa sau ɗaya ta tambaye shi ina ne nan, ina goggonta da wasu daga jama’arta ya gagara amsa mata sai sannu da ya mata ya tashi ya fita ƙirjinsa na bugu bata ƙara yi masa ba, har suka gama zaman jinya suka dawo gidan da aka bashi bata sake maganar garinsu ba, sai ma da taga gidan ne ta dinga shiwa Alhaji Hashim albarka, da ke a tahowawarsu ya mata bayanin shi ya kadesu a mota sanda ɗanta zai kai ta asibiti, ganin ba su da hali gashi ance sai an kawota waje za ta warke yasa shi ya ji tausayinsu ya kawo su, nan ya dinga bata haƙurin kadesun da ya yi. Innar hadda hawaye tana ta sheka masa addu’ar gamawa da duniya lafiya. To fa daga wannan lokacin ko sunan ƙaryarsu ba ta tuna ba bare ta tuntuɓa. Tun abin na ɗaure masa kai har ya daina ya gama fahimtar lamuran mutanen nasa ya shallake dukkan tunanin mai tunani.
Haka ya taho Kano a bayan sunyi magana da Alhajin za a saka Huzaif makaranta da alfarmar ba da kudin jinin wani ba. Alhajin ya yarda ya masa alƙawarin hatta abincin da za su dinga ci ba zai siya da kudinsa na tsafi ba, haka Innar ma zai kawo mata tsohuwa daga ƙauyensu dan karta zauna ita ɗaya. Shi dai kawai ya cika masa burinsa idan har yana son samun duk abinda yake so gurinsa.
Nan aka haɗa shi da Ado Maɗaci, tsohon ɗan ta’addan da ya faɗa komarsu Tunjim, yanayin ƙarfinsa da baƙar zuciyarsa yasa basu kashe shi ba, suka bar shi suna amfani da shi a dukkan wani babban kamu ko wani mummunan kisa da za su yi.
Yana da tarin gaskiya da riƙon amana gare su, wannan yasa lamarinsu da Hameedu ma shi suka danƙawa amanarsa, suka kuma umarce shi da ya masa biyayya a kome da zai saka shi banda cin amanarsu.
Shi ya nemawa Hameedun gurin da zai zauna ya aje masa kome na buƙata harda yar tv marar kala da bidiyo da tarin fina-finan turawa da indiyawa, ya ce masa ya yi ta kalla ta haka kansa zai ƙara buɗewa ya fahimci yadda ake yiwa matan birni magana, ya kuma nemo kwararren malamin da zai koya masa karatu da rubutu ya wayarsa kan lammuran rayuwar.
A ranar da malamin ya zo, ya tambaye shi sunansa, kafin Maɗacin ya yi magana ya riga shi da Huzaif sunansa. A ransa yake jin gwara ya yi amfani da sunan ɗansa mafi soyuwa cikin ransa akan ya yi amfani da sunan Siraj da Alhaji Hashim ya ce masa.
Bayan tafiyarsa ne ya dubi maɗacin ya ce masa daga ranar ya manta da sunansa Hameedu, ya ringa ambatonsa da Huzaif har ya zauna a bakinsa. Maɗacin ya yi ta mamaki ganin cikin lokaci ƙanƙani ɗan ƙauye ya fara fita daga duhun kai.
Haka ya ci gaba da rayuwarsa yana karatunsa yana kuma yawo cikin kwaryar Kano yana kalle yanayin yan matansu, yana bibiyarsu sosai da kalle yadda suke mu’amalantar samari, kafin cikar watanni shida ya yi wata irin gogewa kwakwalwarsa ta buɗe da duk wani abu da aka zuba masa, fatar jikinsa kanta ta canja, farinsa ya daɗa haskawa kome nasa ya daɗa kyau hatta kuwa muryarsa canjawa take yi. Idan kuwa ka ji suna ɗan yarawa da malaminsa yadda harshensa ya karye sai ka rantse da Allah ba da zallar hatsi ya rayu ba, ba kuma a cikin shekarar ya koyi hakan ba.
A haka wasu watannin suka shuɗe har sannan bai ga macen da yake nema ba, Maɗaci har ya fara gajiya da bincika makarantun mata haka Alhaji Hashim har ya fara karaya yana ma ƙoƙarin canjawa Hameedun fuska. Gani yake tamkar Hameedun bai son gano masa yarinyar. Kuma haka ne, akwai abubuwa da yawa cikin ransa da bai kai ga bayyana su ba, sai dai fa har a ƙasan ran nasa yana fatar kowacece zai ganin to karta bayyana gare shi.
Ana hakan watarana ya shiga kasuwa shagon wani ɗankoli da suka fara sabawa ya hangeta tsaye da ƙawarta tana ta yatsine fuska tana masifar da baya iya ji sai da ya isa gare ta ya ji abinda ya ɗauke yawun bakinsa.
“Haba Hadiyya, ke ɗin furfura nawa kika cisge rannan da kike mini oiling? Wai ni duka ma Yaushe na fara ƙirgar da…”
Wacce aka kira Hadiyyar ta rufe mata baki tana dariya,”Ba fa kida magani, baiwace yarinya, oh! Su o’o an zama gwaggo..” Ta ƙara sheƙewa da dariya tana dafata.
Ta fusge kafaɗarta da ta dafa ta matsawa
“Ni ki ƙyaleni, da dariyarki zan ji ko da baƙin cikin ɗan kolin nan! Yau fa sati da nake zuwa gurinsa neman Dying Yana cewa zai kawo, wai Ni so kake furfurar ta cika gashina? Na fa faɗa maka yau guda biyar aka cire mini, Allah ban barin gurin nan sai ka bani abinda zan sakawa kaina ko’ina ya zama iri ɗaya!”
Ta yi walwal za ta yi kuka.
Shi kuma da isowarsa kenan ya dakata yana kokawa da bugun zuciyarta yana kuma ƙiyasta adadin shekarunta!
Ya yi nisa cikin tunani da ƙiyasce-ƙiyascen har suka gama ɓaɓatunsu suka wuce bai ankara ba sai da suka yi nisa ya hangi ƙarshen hijabinsu.
Ya waiwaiga yana dube-dube da kallon mutanen da ke wucewa tamkar mai son gane wani da ke bibiyarsa. Sai kuma ya matsa kusa da ɗankolin ya masa sallama suka cafke ya zauna a wani dutse da ke gefensa. Ya buɗe bakinsa duk da yadda ƙirjinsa ke bugawa hakan bai hana shi fasa tambayar da ya yi niyya ba, sai dai a ƙasan zuciyarsa yana fatar ya samu amsa ba daidai da zatonsa ba.
“Kasan ‘yan matan da suka tafi daga nan yanzu? Ya sunan ‘yar farar doguwar mai manyan kyan?”Sai kuma ya sosa ƙeyarsa ganin yadda ya buɗe baki yana masa dariya.
“Ah Abokina ka ce kaima ka hango ganimar da nake hanga a jikinsu a duk sadda za su zo. Kwastomi nane suna yawan zuwa nan, sai dai Allah bai sa nasan sunansu ba dan sun fi kiran kansu da ‘yar fara ko ‘yar baka, gajerar ce dai yanzun naji farar ta kira ta da Hadiyya.”
Ya dube shi ganin ya yi shiru yana duban ƙasa kamar da damuwa. Sai ya aje jar hodar hannunsa ya ɗan daki kafaɗarsa.
“Aboki kar ka wani damu naga har ka rufta da yawa, nasan makarantar da suke yi ina ji suna hirarta anan, G.G.S.S KWA suke, za ka iya zuwa can ko ita Hadiyyar ka fara nema.”
Ya dube shi ya jijjiga kai yana jin sunan makarantar na zauna masa a kai, sai kuma ya tsurawa zoben hannunsa ido, can ya ɗago ya masa murmushi ganin ya riƙe ƙugu ɗaya yana kallonsa, daga haka suka ci gaba da hirar da ta shafe su har lokacin tafiyarsa ya yi ya tashi ya tafi.
Da tunanin fuskarta ya isa gida, har kuma ya gama ɗabi’unsa ya kwanta maganarta nata wulga masa cikin rai. Tausayinta da ƙarancin shekarunta na damun zuciyarsa, sai yanzu ya fara hango wautar da ya yi, idan wannan kyakkyawar budurwar ce Hamdiyya ya zai yi ya yaudareta ya basu rayuwarrta?A cikin zuciyarsa ya ji yana addu’ar Allah Yasa idan ma itance to karta saurare shi. Yasan wannan hanyar ne tsiran duk wacce zai tara da sunan soyayya.
Tashi ya yi ya zauna a tsakiyar gadon yana tunanin ko ya nemi Maɗaci ya bashi labarin yau, sai kuma ya ji ƙofar falon na motsi, ya miƙe da azaba da ‘yar cocilansa ya fito ya isa ga ƙofar, kafin ma ya tambayi wanene ƙofar ta buɗe sai ga Alhaji Hashim saɓe da babbar rigarsa, ya ratsa ta gefensa ya shiga tsakiyar falo ya zauna bisa doguwar kujerar da take kwalli ɗaya tal a gurin.
“Ance ka bibiyi yarinyar da ka gani yau a kasuwa, akwai yiwuwar ita ce.”
Bai yi mamaki ba, ya sani suna biye da kome da yake gudanarwa a rayuwarsa, ta yiwu har buƙatunsa da yake yi a bayan gida suna gani.
“Ban fa ji sunanta ba, hirar gashin nata kawai na ji, ban kuma san wani abu bayan wannan ba ko gidansu ban sani ba. Sannan…”
“Ya yi shiru yana tauna maganar da ke cinsa a tun sa’adda ya gantan.
“….Ta yi yarinya da yawa, bari a samu wacce ta ɗan fita, za a samu ni na san za a samu cikin shekarar nan.”
“Ba kada hankali, har ka manta zarewar da na fara yi ganin an ci rabin shekara ba a same ta ba? To umarni aka baka, ba kuma wanda zai wahalar da kansa bincikenta, nan da cikar mako uku ka je asibitin nasarawa za ka sameta acan, ka yi duk yadda za ka yi ta faɗa mata sunanta da bakinta. Koma da dai ba ita ba ce anan ne za ka samu mai sunan da muke buƙatar, abinda ya bayyana gare shi kenan!”
Ya miƙe tsaye ya isa ga ƙofar sai kuma ya waiwayo yana kallonsa.
“Ka rage gaddama, Tunjim baya sonta, ka kuma rage wannan jindadin da kake yi kana ƙyalli kana zuba kiba, ka ringa tuna ko da take hannuna banda ikon hana Tunjim ita a yayin da za ka yi masa kuskuren da zai neme ta! Kar ka manta alƙawarinka, ba zan ƙara tunatar da kai kome ba”.
Ya fice yana buga masa ƙofar saman manyan idanuwansa da suka fara kaɗawa.
Ya lulubi kujerar ya zauna ya riƙe kansa yana ambaton sunan Allah cikin zuciyarsa. Sai kuma wasu kalamansa suka saka shi murmusawa ya shiga bin jikinsa da kallo. ‘Wai ya rage jin daɗin da yake yi, ko ya bawa zai hana kansa jin daɗi? Da kuma ace baya gyara kan nasa Alhajin shi zai fi kowa tada masa hankali, haka zuciyar da yawan mutane take, baƙin ciki ƙiri-ƙiri kan abinda ba kai ka bawa kanka shi ba.’
Ya jira har cikar mako ukun, da wuri ya shirya ya tafi Asibitin da suka ce masa zai samu mai sunan da suke son, ya haɗa ido da mutane da yawa kafin ya hango fitowarta daga wani ward, ya yi azamar fiddo kuɗi daga aljihunsa ya hau lissafi, ya ɗago kai yaga tana ta waiwaye-waiwaye har ta waigo suka haɗa ido ya ɗauke kansa da sauri jin zuciyarsa ta yi wata irin rigirgiza, haka ya cigaba da lissafin da baya ganewa, a cikin jikinsa yake jin motsin takunta na zuwa gurinsa, har ta iso ta lalace a kallonsa kafin ta tambaye shi ko ya ga mai goro ya girgiza kai, ta fara jansa da hirar masu talla cikin asibiti har ya ɗan sake yana tayata cikin rashin walwala, a cikin zuciyarsa yake jin kuskure ne ya tsaya tambayar sunanta, bai so ko kaɗan wannan kyakkawar yarinyar ta shiga komarsu, har ta wuce sai kuma ta dawo tana masa murmushi ta faɗa masa sunanta Hamdiyya, anan na’urorin da ke sarrafa kwakwalwarsa suka tsaya na sakanni kafin ya yi azamar daidaita kansa ya faɗa mata nasa sunan Huzaif.
“Kana da kyau Allah!”
Ta furta masa tana rufe fuskarta alamun kunya, sai kuma ta juya da sauri tana masa rangwaɗa har ta ɓacewa idanuwansa. Ya sharce gumin da ya jiƙe sajensa da bai hanata ganin kyawun ba, a sanyaye ya juya ya bar asibitin.
To fa har ya dawo gida zuciyarsa babu nutsuwa ko kaɗan, ba abinda ke sake narkar da tunaninsa sai daddaɗar muryarta, da kuma yanayinta da ya gani irin na mahaifiyarsa har kuwa yanayin tsayinta da dogon wuyanta duk irin na Innarsa, ba dan Ƙaryarsu da nisa ba, kuma Innarsu ba ta taɓa takawa birni ko na garinsu ba, da sai ya rantse da Allah ita ɗin jininsu ce.
Ya tuna yadda take ta zuba masa murmushi tana kashe ido sai abin ma ya saka shi murmusawa, sai kuma ya tsuke fuska tuna shashancin mata na haɗamar mazaje masu kyau a ɗan fahimtar da yawa matan birni, ji dai wannan yarinya ƙarama da ita amma rawar kanta da kome ya nuna ɗan wannan kyan nasa da yake rainawa, su Alhaji Hamshim ke baƙin ciki da shi ya fusgeta zuwa gare shin.
Buɗe ƙofar da aka yi ne ya katse masa tunaninsa sai ga Maɗaci ya shigo. Ya bishi da kallo kawai har ya zo ya zauna kusa da shi. Ya yi saurin kauda kansa jin wani warin burkutu da yake yi.