“Ka kula da wannan zoben da shi za ka kawo ta ɗakinmu na tarbar baƙi irinta, idan kuma yana jikinta ba za ta iya fita daga gurin ba sai da izininka. Sannan kuma duk wanda…” Sai kuma ya yi shiru yana ɗaga sandarsa ya sake nuna shi, a take kome nasa ya dawo daidai.
“Kodayake ba sai na gaya ma ba tunda nasan za ka kiyaye duk abinda zan faɗa.” Ya furta yana masa murmushin da har yau bai san fassarar shi ba.
“Sai dai kawai ka kiyaye saka shi a yatsanka, kar kuma ka bari Maɗaci ya gani ko da wasa.”
Daga haka ya juya zuwa mazauninsa, Huzaif ya bishi da kallo yana jin kamar yasa ƙafa ya masa duka guda a motsattsan jikinsa da tsabar rama ana hango ƙasusuwan ƙirjinsa. Sai kuma ya kauda tunaninsa yana mai azamar barin gurin.
Koda ya koma gida jujjuya zoben ya ringa yi zuciyarsa cunkushe da mamakin hana shi sawa da ya yi, can dai daya gaji da tunani sai ya buɗe wata locker ɗinsa ya jefa zoben ciki.
Haka ya zauna tsawon watanni biyu cikin tunani da fargabar da ya rasa dalilinta, wannan yasa ya yi rama sosai tamkar wanda ya kwanta ciwo.
Bayan cikar lokacin ne ya tafi kadunan zuwa unguwar da suka faɗa masa, nan ya bibiyeta a ɓoye ya gama naƙaltar halin da take ciki kafin ya bayyana gare ta, ya mata ƙaryar da yasan za ta ji tausayinsa ta sake bashi dama kanta, a nan ya sake samun yardarta a bayan ya kaita gidan ya yi mata pretending rantsuwa da alƙur’ani wanda yasan ko haukan duniya ne kansa ba zai iya wasa da Alƙur’ani ba, haka idan har tana ƙaunarsa da gaske ba za ta barshi ya rantse ba. Hakan ne kuwa ta faru, ta hana shi rantsewar, shi kuma ya samu damar da ya saka mata kwayar nan cikin cup ɗinta na ruwa, tasha ya haiƙe mata ba cikin hayyacinta ba. Tunjim ya yi surkullensa aka maida ta gida, aka kuma juya tunanin Iya.
Daga nan ya shiga rayuwar Iya har ta fara ƙaunarsa, har zuwa lokacin da ta haɗa su tafiya tare, a rannan ya saka zoben Tunjim a hannunsa a halin mantuwa, sai da ya yi nisa da shi ya tuna, ya yi kamar zai zare zoben sai ya fasa yaja dogon tsaki daya tuna ƙila ma iyayi ne kawai na tsafi za a wani ce masa kar ya saka a hannunsa, har zuwa sa’adda suka ƙona motar nan dan ma kar wani kuskure ya faru ko a gane tana da rai, a nufinsa ta bar gaban ahalinta ta tafi can wani gurin ta yi rayuwarta, anan ya saka mata zoben suka ɓace, har zuwa sa’adda aka ce masa tana da ciki, yaso a zubar ta ƙi yarda, Tunjim ma ya hana shi, har dai zuwa rayuwar da suka gabatar tare da ita zuwa ranar da aka fitar ta cikin idonsa aka tafi da ita aka binne. Daga rannan jin daɗin rayuwar duniya ya tsaya masa cak!
*** *** ***
Shi Maɗaci lokacin da ya tafi da Hamdiyya cikin baƙar motar da Alhaji Hashimu ya bashi, sai ya tsaya a wata gonarsa da ke gabas da jejin da suke, ya gama harkokinsa har zuwa sa’adda dare ya raba tukunna ya ɗau hanya zuwa maƙabartar da aka bashi umarnin binne ta wacce take yamma da jejin nasu.
Adaidai marabar hanyar da Hashimu ya taɓa kaɗe Hameedu ya aje motar ƙasan wata bishiyar mai yawan duhuwa.
Daga nan ya buɗe boot ya zaro Hamdiyya da ke kwance tamkar matacciya, har sannan jini na fita daga hannun da suka tsarga mata.
Saɓata ya yi a kafaɗarsa ya zaro ƙaramar cocinsa da massasbi da manjagara ya fara keta dajin da ita.
Sassanyar iskar da ke kaɗawa mai gauraye da danshin ruwan da ke kafe a ganyayyakin bishiyu, su suka haɗu suka farkar da ita ta zabura tana sakin azababben ihun da ya firgita maɗaci ya yi watsi da ita nan gefe, a take gefen maƙogwaronta ya caki wani ice da ke kafe a gun, gurin ya fashe jini ya fara kwarara tamkar wadda aka sokawa wuƙa.
A fusace ya haske ta da cociin hannunsa ya daga ƙafa zai daki ɗayan hannunta da take ta ƙoƙarin ɗagawa ta dafe maƙogwaron anan ya yi arba da zoben hannunta ya yi wata irin wujijjiga yana komawa baya. Ya ma za a yi ya manta shi? Zoben da ya yi sanadin kashe yaron cikinsa saboda ya tsince shi a ƙasa ya ɗauka ya zurawa ɗan ƙaramin yatsansa. Ya tuna daga rannan su Tunjim suka fara hajijiya da rayuwarsa, sai kuma ya buɗe idanuwansa sosai da ya tuna Haameedu, idan har ya saka shi a yatsansa to tabbas idan shi bai mutu ba wani nasa zai mutu, a karon farko tun shigowarsa bariki da ya ji yana marmarin roƙan Allah kada ace Haameedu ya saka zoben nan. Ya tsinewa Tunjim ya tsinewa muguntar da ya saka ya bashi zoben duk biyayyar da yaga Hameedun na musa, sai kuma ya dubi Hamdiyya, anan ya gane dalili, kenan Tunjim ya ce a saka mata zoben ne saboda yana so tasha wahalar duka duniya kafin ta mutu, ya jijjiga kai yana mai sunkuyawa ya sake surarta ya saɓa ta a kafaɗa, yaji taja numfashi alamun bata suma ba, sai dai fa idanuwanta a rufe suke ruf, sai sannan ya buɗe baki ya mata magana.
“Yar budurwa idan har kina so wahala ta ƙare miki to ki san dabarar da za ki yi ki cisge zoben hannunki kafin na binneki, idan yana hannunki za ki ta shan wahale ne marar amfani tunda dai a bayanta mutuwa ne za ki yi, ni kuma bazan iya cire miki ba saboda ban shirya ganin mutuwar Yetunde masoyiyata ba.”
Yana ji ta yi wani sharaf alamun ta idasa sumewa.
Daga nan ya ƙarasa cikin maƙabartar zuwa wani ɗan fili, ya shimfiɗe ta a gefe, ya kashe tocilan ɗinsa ya hau tona rami, sai da ya tona daidai tsayinta ya jawo ta ya watsa ta ciki, ya fara maida mata ƙasa kenan ya hango hasken fitilar ƙwai ko na aci bal-bal na yi sashin da yake, ya tuttura ƙasar da sauri-sauri ya yi ƙundumbula cikin wata duhuwa da ke bayan kabarin Hamdiyya ya ɓoye.
Yana nan laɓe Zawwa ta zo ta fara haƙa kabarin, da fari yasha ko Hameedu ya turo ayi hakan, sai kuma can ya fahimci irin matan nan ne masu cire sassan mamata. Ya yi matuƙar kaɗuwa sa’adda yaga Hamdiyya nada rai har tana nuni da a cire cikin ɗanta, duk yawonsa da ya yi cikin duniya yana ta’addanci bai taɓa cin karo da taurin rai irin na Hamdiyya ba, ya jinjina girman ƙudirar Allah sai yake jinsa tamkar sabo cikin addinin masulunci. Yana nan yana tunani har Zawwa ta cire mata zoben bai kula ba, Sai zuwan Haadiru ne ya dawo da shi hayyacinsa, har dai zuwa sa’adda suka fito da jajiriyar ya ji jikinsa ya yi wata irin mutuwar da ba zai iya fitowa ya murɗe kan ɗiyar ba, har zuwa sa’adda aka fara ruwa bayan ya ɗauke Haadir ya maidata kabarinta, har zuwa sanda ya ga duhunsa shi kuma ya ƙara lafewa, zuwa sanda suka tafi ya bisu a baya har gidansu bai san da tarko ba ya faɗa, har dai zuwa inda Zawwa ta rufe bakinsa ruf da wannan kwayar!
Daga rannan ya yi-ya yi ya buɗe baki ya bawa Hameedu labarin ‘yar sa na raye sai dai da ya yi niyya sai harshensa ya sarƙe da wasu zantuttukan, tun yana gwadawa har ya haƙura. Har zuwa bayan shekaru biyu da Hameedun ya nemo shi ya bashi kuɗi cikin wata jaka wadda ke daidai da Miliyan biyu ya kwatanta masa ƙauyensu ya kaiwa Amininsa Bawa, amma kar ya faɗa masa in ji Shi ne yasan dai ƙaryar da zai musu su karɓa.
Ya tafi ƙauyen ya tarar sun bar ƙaryar ba a san ma inda suka tafi ba, ya taka har gidan Maigari ya nemi sanin makarantar da Haadiru yake ya faɗa masa tun dai ɗiban da aka yi har yaron A.B.U aka kai su, zai iya dubawa ko yana can har sannan. Haka ya taka har Zaria ya kuwa fara ganinsa tun a ƙofar farko ta makarantar, anan yake shekararsa ta ƙarshe a degree na biyu, ya nemi wani yaro ya bashi jakar ya ce masa ya kaiwa Haadiru ya faɗa masa Maigarin Tanɗau ne ya ce a bawa Babansa Bawa, agaji aka kawo ƙauyensu shi ya sa aka raba har shi.
Daga nan bai komawa Hameedu da sakon ya kai ko bai kai ba, kasancewar shi ma akwai kyautar da ya masa kawai sai ya kama gabansa zuwa legos, bai sake waiwayar Hameedun!