“Ka ji zance na ko? Dama na faɗa maka sai Zawwa ta haifi ɗiya har ta girma sannan ka auri ɗiyar, ai shi kenan, alƙawari na na biyan sadakinka da sisin gwal na nan fa. Ni Allah yasa shi Huzaif ɗin bai yi auren ya barka ba, ina kake ne Huzaifu matso mu gaisa mana..”
Hameedun ya yi wata irin dariya yana juyawa ya kalli Huzaif da ke ƙoƙarin ficewa daga falon, “Bawa bari zancen nan, idan na ce maka kunyarka nake ji ba za ka yarda ba, bari dai na tafi zuwa gobe, dan Allah a bawa Zawwa da ɗiyarta haƙuri sosai dan Allah su yafe mini su ma, ina jin kunyar da har bansan ya zan yi na kalli idanuwan Zawwa ba, ga jarabtar da na faɗa ta kamuwa da son ɗiyarta, ƙaunar da bansan yawanta ba, dan Allah Bawa kar ka hukuntani ta hanyar hanani ɗiyarku, ba zan iya ba, da zan iya da tun da na fahimci taka ce wallahi da na barta yadda annabi ya bar duniya, wallahi summa tallahi da haka zan barta, amma ban ma ji zan iya balle na gwada iyawar, ban ma ji zan iya haƙura ba balle na gwada haƙurin.”
Jikin Bawan ya daɗa sanyi, sai kawai ya jijjiga kai yana daɗa girma ƙudurar ubangiji mai fidda rayayye a jikin matacce. Duk da yasan ɓata lokaci ne tsayawa yiwa Zawwa maganar ta yafewa Hameedu sai dai yana fatar Allah ya ganarta aƙidarta kuskure ce ta hanyar da za ta gane.
Shi ya turo Bawan zuwa farfajiyar filin gidan, suka yi tsaye anan suna tattaunawa kan wasu abubuwan nasu. Zawwa da ke can sama jikin window tana kallon filin gurin, idanuwanta suka ɗauko mata Hameedu na tura Bawa a keken guragu suna magana cikin farin ciki tana kula da yadda yake kyakyata dariya yana waige-waige. Ranta ya daɗa ɓaci da zallar mamakinsa har sai da idanuwanta suka fidda kwallar baƙin ciki, ta juya fuu ta yi ɗakin Haƙabiyya da ita ma shigarta ke nan ɗakin.
“Ke kina jina!”
Ta juyo a ɗan tsorace tana kallon idanuwan mahaifiyar tata.
“Duk randa kika shiga gidan wancan abokin Baban naki, ina so ki turo min shi tun daga saman bene zuwa ƙasa, ko kuma ki saka guduma ki yi ta bubbuge mini ƙafafuwansa shi kaɗaine abinda zai sanyaya ruhina.”
Sai kuma ta rufe fuskarta tana hawaye ta samu gefen gadon ɗakin ta zauna tana haɗiye wani ɗaci da ya tattare mata maƙoshi.
Jikin Haƙabiyya ya yi sanyi, ƙafafuwan ta suka kama rawa da ganin yanayin Mamin nata, take ita ma ta fara hawayen ta matsa kusa da ita.
“Mami dan Allah ki yi hakuri ki yafe masa, a kunnene na ji Baba ya ce ya yafe masa.”
“Tashi ki je yanzu zai tafi, ki buɗe masa motar idan zai shiga!”
Haƙabiyyar ta yi sororo tana kallonta.
“Ki tashi na ce! Ki kuma shafawa fuskarnan taki hoda kafin ki fita gabansa!!”
Ta furta mata da tsawar da ya sakata isa gaban mirror da sauri ta fara zizara kwalli cikin idanuwanta.
Daga bakin ƙofar falon da za ta sadata da parking space ta tsaya tana hango Huzaif da ke waya fuskar nan tasa a tamke, sai ta samu kanta da ƙurawa fuskar ido hawaye na cikowa cikin idanuwanta.
A jikinsa ya ji ana kallonsa, ya ɗan waigo saitin da yake ji, fes! Idanuwansa suka sauka cikin nata, muryarsa ta ɗan sarƙe ya kama tari, sai kuma ya sauke wayar daga kunnensa ya buɗe mota ya shiga.
Hawayen da take riƙewa suka gangaro bisa kuncinta, ta ɗaga ƙafarta da dukkan kuzarinta ta isa gurin motar, ganin yana ƙoƙarin zuge tagar motar da take tint ya saka ta saurin saka hannunta a gurin tana duban gefen fuskarsa da yaƙi juyo da ita ya dube ta. Suka yi shiru na ‘yan sakanni kafin ya ɗago da fuskarsa saitinta, sai ya mata murmushi yana cuno bakinsa gaba ya ce.
“Look at his face…”
Ta kai kallonta saitin da ya mata nuni da bakin, taga mai zubin ghost da babanta suna magana harda dukan kafaɗun juna, ta tsurawa fuskarsa ido tana jin bugun zuciyarta na canjawa da wani irin tsoro, sai ta waigo saitin Huzaif tana tsuke baki.
“Kinsan adadin shekarun da na kwasa ina fatar ganinsa yana dariya irin haka?…Kinsan adadin hawayen da na zubar ina fatar ganinsa cikin farin ciki ko na yini guda ne.”
Ya furta yana mata wani irin kallo na ƙiyasi.
“Ina ganin tun ba ki zo duniya ba, tun ban haɗa cikakken hankali ba, ba sai na roƙe ƙi ki cika masa burinsa ba dan na kula shi ɗin ne mijin da kike ikirarin an miki a gida, na kuma yi farin ciki da ke ɗin kika zama wani ɓari na jinina, ‘yar Aminin mahaifina, duk da haka ba zan fasa roƙar kiyi iyakar ƙoƙarin ganin baki ɓata ma abokin Babanki ba, ki tabbatar kin bashi farinciki da duk wani abu da kika san zai taimaka masa kan hakan, ki kuma ƙaunace shi fiye da kome da kike ƙauna, kinji Matar Babana?”
Ta haɗiye wani ɗaci tana maka masa harara cikin hawaye, sai kuma ta ja hanci tana sa hannunta ta share fuskarta.
“Kai nake so…”
“Ba zan taɓa ƙaunarsa ba ko da shi kaɗaine namijin da zai saura cikin duniya…”
Ta furta tana janye jikinta daga jikin motar, ta yi taku biyu ta baya ta tsaya.
“Na tsane shi! Na faɗa maka na tsani Babanka!”
Ta ƙarasa a hankalin da tasan shi kaɗai ne zai ji.
Bin bayanta da kallo ya yi zuciyarsa na tafarfasa da kibiyar maganar da ta daɓa masa, yana gani ta isa ga Babansa ta tsaya gefensa fuskar nan tata a yatsine yawa taga kashi, ya kai kallonsa ga baban yaga yadda yake washe baki yana tsokanarta sam bai ma kula da yadda take harararsa a kaikaice ba, kai zai iya rantsewa da Allah jikinsa har rawa yake yi, sai kawai ya ja siririn tsaki yana zuge tagar motar, ya kuma cusa earpiece a duka kunnuwansa.
Sun ɗan daɗe tsaye suna ta hira da tsoho Bawa kamar ba a rabu ba, kafin kuma ta rako shi har jikin motar saitin mai zaman banza ta buɗe masa ya shiga ya zauna kamar yadda Zawwa ta bata umarni. Daɗi ya kashe shi kamar ya ce kada duniyar ta ƙare, ya bi bayanta da kallo yana jin dama ya fisgota ya tsaga ƙirjinsa ya jefata ciki ya ɗinke. Har ta ƙule bai sani ba sai da ya ji Huzaif na sallama da maigadi, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana daɗa nutsa jikinsa cikin kujera, ya rufe idanuwansa ruf! Yana neman tsari da abinda zai katse masa tunanin mallakarta!!
Har cikin ɗaki takai babanta ta taimaka masa ya kishingiɗa saman gadonsa, ya yi hamdala fuskarsa fal fara’a ya dube ta, “idan kin shiga ciki turon Maminki. Yauwa ashe ma kinsan abokin nawa? To kuma kina sonsa? To shi ke nan dai Allah ya haɗa kanku, ki yi kome da kyakkyawar manufa kinji?”
Ta gyaɗa kai kawai tana miƙa hannunta bisa wani tangaran, ta ɗauko dabino ta buɗe tsakiyarsa ta cire kwallon, ta miƙa masa ya karɓa ya watsa a baki ya taune.
“Allah Ya miki albarka, yasa naga ‘ya’yanki, na yi farin ciki da dalilinki na samu Aminina, Allah ya baki masu sanyaki farin ciki kema, ya cika miki dukkan buri, ya kare ki daga sharrin mai sharri.
Sai ta yi dariya tana saka hannayenta ta rufe fuskarta jin wata irin kunya na shigarta.
“Kai Baba dan Allah ka yi shiru.”
“Ungo nan”.
Ya mata daƙuwar da ta sakata ficewa da gudu tana dariya, abin mamaki har ta fara imagine ga ‘ya’yanta da Huzaif sun haye jikin Baba Bawa suna ta tsalle-tsallensu. Da wannan farin cikin ta faɗa ɗakin Zawwa tana furta “Allah Yasa haka” a zahiri, sai kuma ta yi diri-diri ganin Mamin ta zuba mata ido, “Baba ya ce na kira ki.”
Ta furta kamar uwar gulma taga abin gulma. Mamin ta mele baki tana aje mata littafi gefen mirror ɗinta, “ɗauki wannan ki mini solving wani equation da aka ba mu.” Ta ratsa ta gefenta ta fice, ita kuma ta ƙarasa ga littafin ta buɗe tana mamakin son boko irin na Maminta da bata mai da hankali kan lissafi, nan ta zauna ta fara yi mata aikin ganin tun tana Jss3 ta gama da shi.
“Uwargidan Bawa Ɗan Malle, kin tare gaba kin tare baya, kin dunƙule zuciyar Bawa kin jefa a rijiyar da batta ido.”
Ta yi wani irin murmushi kanta na fasuwa da kirarin, ƙuncin da ke tattare a ranta na shigewa wani saƙo, ta daɗe bata gansa cikin murna irin haka ba, sai ta ji ganinsa hakan ma ya mata daɗi ta ko’ina, duk da acikin ranta tana jin duk domin Hameedu ne. Ta zauna a gefen gadon ta ɗauko gudar ƙafarsa da ke miƙ ta ɗora ta bisa cibiyoyinta ta hau matsa masa. Sai ya lumshe ido daɗin hakan na ratsa shi, can ya buɗe yana leƙen fuskarta yana jinjina rigimarta cikin zuciyarsa.
“Yau dai buri ya cika ko? Hameedun ‘yar ki ce ta kawo shi nan, ya ganta a waje ya ji yana sonta, sai ya bibiyeta har ya zo nan ya tadda mune iyayenta. Ya kuma nemi da ke ma ki yafe masa, ki kuma yarje masa ya nemi auren ɗiyarki.”
Ta dakata da abinda take yi tana kokawa da bugun da maganar ta mata, duk da hakan take so, hakan ne burinta na shekaru, amma a yanzun sai ta ji lamarin ya mata wani girma, ta wani ɓangaren kuma sai ta ji zafin Hameedun na daɗa mamayeta, taga zahirin fitsararsa da rashin kunyarsa takai intaha. Sai kawai ta ci gaba da matsa ƙafar bayan taja wani siririn tsaki. “Allah ya wadaran soyayya.”
Tsoho Bawa ya buɗe baki yana kallonta.
“Wai ba haka kike so ba?”
“Hakan nake so, kuma na yi murna, kawai naga rawar kansa ya yi yawa ne, waya faɗa masa zan basa ‘yata da manufar alkhairi, ai sai ta sharrin da zai gagara numfashi wallahi, ba zan yafe ba, kar kuma ya sake ya ce zai mini magana, zan iya baku mamaki Bawa.”
Ta kira sunan Bawan gatsal, sunan da ta daɗe bata kira ba.
“Allah ya sanyaya zuciyarki, ya ganar da ke Hameedu mutumin kwarai ne. Ni dai na faɗa miki ba da yawuna ba ki ruguza rayuwar yarinya, haka ko zan bada Haƙabiyya ga Hameedu to fa da zuciyata guda zan bashi, shi ɗin jinsa nake kamar jinina, idan kika masa abinda ba daidai ba to Ni kika yiwa. Na kuma hane ki da wannan mummunan ƙudirin naki, ki aje makamanki tunda da kansa ya taso ya nemi gafararki, wai me kuma kike so da shi?”
“Rayuwarsa! Duk abinda zai tarwatsa rayuwarsa nake so. Sai na raba shi da duk abinda ya mallaka, ciki har Haƙabiyyar da yake so a bayan na mallaka masa ita na kwana uku kacal! Yanzu kai baka ga saboda mace ya zo nan ba, kenan da ba itan ba ce haka zai yi aurensa ba abinda ya shafe shi da nemanmu, ba abinda ya dame shi da hakkinmu da ke kansa, kana ganin mutum ya zama hamshaƙi baya da damuwa ko ta sisin kwabo, amma kai sai wani daɗi kake ji kana wani bin bayansa, Allah kaɗai yasan karairayin da ya maka ka hau kai ka zauna.”
Da ke a wuya take dama sai kawai ta rushe masa da kuka tana tuna abubuwa da yawa da suka faru ciki harda kumburar da kafar bawa ta yi suna ihu yanayi, da jelen da ta dingayi da shi a gadon bayanta. Amma shi ne yanzu duk ya manta har ma ƙoƙarin ɓata mata yake yi saboda maƙiyinta Hameedu.
Bawan ya yi shiru yana jin kukan nata na ratsa shi, bai taɓa ganin abinda ke saurin saka Zawwa kuka ba irin batun Hameedu, ya rasa irin ƙiyayyar da take masa, sai kawai ya ja numfashi ya hau rarrashinta.
“Ni ba kuka na ce ki yi mini ba, Allah Ya baki haƙuri, kawai gaskiya ce na faɗa miki, amma shi ke nan, kamar yadda na faɗa in sha Allah zan tabbatar, ba na sake shiga lamirinki da Hameedu, na sani da sannu watarana za ki gane.”
“Ya dai fi.”
Ta furta tana karkata baki tana sharce hancinta da ke yoyo.
Daga haka suka shiga hirar da ta shafe su.
Sai da tasa haƙarƙarinta bisa gado tunanin abubuwan da suka faru ranar ke ta dawo mata, abin kamar almara, wai Baban Huzaif ne Abokin Babanta da suke nema su aura mata, wai kuma tun kafin su ganshi har ya ganta ya kuma fara ƙaunarta kamar yadda Mami ke buri, sai taji tsoron Allah na cika zuciyarta, dan tabbas idan ba shi ba babu mai iya juya lamarin haka. Ta juya ɓarin damarta tana jin kewar Huzaif na mamayeta, sai ta tuna lokacin da yake roƙarta ta haƙa rami ta binne soyayyarsa, ko ina taga ramin da zai ɗau ƙaunar da take masa, ai babu wannan hole ɗin, babu shi cikin duniyarta. Sai ta miƙa hannu ta jawo wayarta ta fara daddanna lambarsa, duk da bata ji zai ɗauka ba hakan bai sa ta fasa kiran ba, ga mamakinta wayar na shiga ya ɗaga tamkar wanda dama kiran nata yake jira.
Sururul Qalby…tunanina ya hanaka barci ko?”
Ta furta da salon da tasan zai ratsa jikinsa ko da shi ɗin dutse ne.
“Haramun ne nema cikin nema, ki daina nemana dan Allah, kinga an bada ke.
Tsarin yayi kyau