Sai ta ji maganar bambarakwai, wato shi ya zama mace ita namijin, shi ne yake faɗa mata abinda maza ake faɗawa, sai kawai ta taɓe baki kamar tana gabansa.
“Ba zan iya ba, da zan iya da ban kira ka cikin daren nan ba.”
“Ni kuwa kinga na iya, dan daga shekaranjiya zuwa yau kallon yar ƙaramar ƙanwata nake miki, kuma matar Babana.”
“Aww da wane kallo kake mini?”
Ya yi murmushi yana gyara kwanciyarsa jin ya kusa bambarama. Sai ya ji duk wani haushinta na ɗazu na yayewa, shi kaɗai yasan daɗin da ya. . .