Skip to content
Part 30 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

A bakin falon ya tsaya yana kallon tvn da aka kunna ga kuma bowl an aje cike da inab, ya waiwaiga yana jin ƙamshinta na cika hancinsa, sai kawai ya jijjiga kai ya gane ita ce ta ɗaukar masa mukulli ta saka shi shan wahala yau, ‘ko uwar me take so da ni?’ ya yi kwafa yana ƙarasawa tsakiyar falon ya zube bisa kujera yana kiran sunan Allah.

“I swear idan baka ce kana so na ba sai na kashe kaina.”

Ya yi firgigit ya miƙe ya waiga, can ya ganota a lungu ta yi wuƙi-wuƙi da ido hannunta riƙe da wuka ta saita a kan ɗaya hannun. Abin ma sai ya bashi haushi ya bashi dariya.

“Aww wai kashe kan ki za ki yi?”

Ta kaɗa ido alamun i.

“To bari muga irin kakarin da za ki yi a yayin da za ki mutun.”

Ya furta yana dosarta har ya isa daf da ita ta yadda take jin hucin numfashinsa a saman fuskarta. Bata yi aune ba ta ji  ya fisge wuƙar, “shashasha kawai, ni fice mini daga gida kafin na karya hannayen naki masu kama da ƙafar ‘yan tsaki.”

Ta zumɓuri baki ta zagaye shi ta wuce, maimakon ta tafi yadda ya ce sai kawai ta yi gurin dining ta dauko cup ta zuba ruwa ta miƙa masa. Yabi hannunta da kallo yana mamakin taurin kanta. “Wai ke me gareki cikin gidana da har za ki satar mini mukulli ki dinga shigo mini Kai tsaye ko kunyar hakan baki ji, ko baki ga ni namiji ba ne? Hala dai dama haka kike bin gidajen samarinki?”

“Sururul Qalby kasha ruwan pls, ka gaji ko? Sannu.” Ya gyaɗa kai kawai ya karɓi ruwan ya sha ya ishe shi, ya waiga gefensa yaga jakarta ya jawo ya hau zazzageta ya duba bai ga mukullinsa ba, ya dago ya kalleta yaga dariya ma take masa, “yana inda ba za ka iya gani ba, in kuma za ka gani zo ka duba.”

Sarai ya gane mai take nufi, dan haka ya fisgo ta ita da gyalenta da jakar ya jawo ta har farfajiyar gidan.

“Ki fita idona, Allah kika ƙara gigin dawo mini nan zagewa zan yi na miki dukan tsiya, na tattara ki na kaiwa Babanki na faɗa masa iskancin da kike yi mine.” Maimakon ta ji haushi sai ta hau tafi tana dariya. “Sir Allah indai za ka kaiwa Baba wannan maganar ni kuwa gidanka yanzu na fara zuwa, ai abinda nake so kenan.” Ganin ya zaburo Yasa ta kwasa da gudu ta yi ƙofa, ta buɗe shi ma ya buɗe suka kusa gware, sai ta yi baya da sauri tana ɓalla masa harara da jin haushin bai sameta rungume da ɗansa ba. Sai kawai ta fice da sauri tana cika da batsewa, shi kuma ya ƙarasa inda Huzaif ke tsaye, “wai lafiya? Jiya na ganta anan yau ma na ganta me kake yi mata ne?”

Ya sauke ajiyar zuciya ransa ɓace da ganin Alhajinsa ya sake ganinta a gidansa.

“Allah ka ƙyale yarinyar nan sam bata da ce da zama uwa ba, bata da mutunci gata daƙiƙiya, wai fa dan ta faɗi jarrabawata shi ne take ta bibiyata sai na gyara mata ta ci. Alhajina dan Allah ka bar neman yarinyar nan.” 

Ya rufe bakinsa da ya fara washewa, sai kuma ya juya zai koma inda ya fito, sai da yaje jikin gate ya waigo yana kallonsa. “Sai ka dinga mini addu’ar Allah Ya dasa mata so na cikin zuciyarta ya rabata da shashashan da ta ce tana so. Kuma tunda ka ce mata daƙiƙiya idan muka yi auren kai kaɗai za mu bari anan na tafi da ita ƙasar da za ta yi karatu har ta fika ilimi, jarrabawa kuma dan Allah kar ka saka mata ta cin kaga ta inda zan hukuntaka”. Ya yi ƙwafa, ‘ɗan gwafar uba kai, ji ko kunyar duban idona ya kira matata daƙiƙiya bai yi ba. Ya buɗe ƙofar ya yi ficewarsa dama miƙe ƙafa ya fito yi ya ƙara so gun yaron nasa su ɗan tattauna tunda dai yanzu ya gane yana shigar masa gida. 

Huzaif ya rufe bakinsa da ke buɗe jin ƙuda na shirin faɗa masa, sai kuma ya hau ƙarewa kansa kallo daga sama zuwa ƙasa.

‘Ke nan ni ne shashashan?’ Ya furta cikin ransa yana jin haushin Haƙabiyya na isowa har maƙogwaronsa.

*****

Kafin cikar sati biyu ta je gidan Huzaif sau kusan shida suna kwashewa ba daɗi, ƙarshe ma ya bar daga kiranta ya kuma daina mata magana a duk inda ya ganta, wannan matakin da ya ɗauka ya daga hankalinta, da ƙyar ta shawo kansa da alƙawarin ta daina zuwa gidan tunda bai so, daga nan suka ci gaba da gaisawa sama-sama, duk da ita hakan ma daɗinsa take ji. Ta ɓangaren mai zubin ghost kuwa a duk sanda ta ji labarin zai zo za ta nemi waya ta tura masa sakon kar yazo idan yana son ganinta cikin farin ciki, ganin da yake mata cikin makaranta ai ya ishe shi, hakan zai biye mata ya ƙi zuwan gudun karya ɓata mata rai. Idan kuwa ya kira ta a waya shi zai ta surutunsa tana ta uhm har ya gaji ya kashe.  Zawwa na ankare da ita sai dai bata taɓa nuna mata ba, tara ta take tana jiran lokaci.

Yau, tunda ta tashi take jin kanta na yawan sara mata, haka ta duƙunƙune kan gadonta kafin kiran Mami ya iso kunnenta ta tashi ta tafi.

“Gani Mami.”

“Yau ba lecture ne?”

“Eh babu, ban ma jin daɗi.”

“Ok,” Mamin ta furta cikin halin ko’in kula, sai ta jawo wasu kaya masu shegen kyau a gefenta ta turasu gabanta.

“Ki je kiyi wanka ki saka su a jikinki, yanzu Abokin Babanki zai iso.”

Ta karɓa a sanyaye tana turo baki gaba.

“Ba ni wayarki.”

“Me?”

Ta furta jin kamar kunnenta ne.

“Ba ni wayarki na ce, idan kina buƙatar faɗa masa kar ya zo yadda kika saba sai ki nemi ta babanki.”

Ta zaro ido jin an kamata.

Mamin ta harareta ta miƙe.

“Idan kin gama shiryawar akwai yari da sarka da na daɗe da sai miki cikin waccar locker, ki ɗauka ki saka, ban kuma san taɓe-taɓe, ni zan leƙa Hajiya Zuwai da ta kwan biyu ba lafiya, ke nake jira.”

Ta tafi da sauri ta kawo wayar ta bata tana kumbura. Ita kuma ta kasheta ta jefa cikin jakarta ta miƙe, “in kuma dawo na tarar ba ɗan kunne ko sarka a wuyanki.” Ta yi ƙwafa, ta fice daga ɗakin.

Anan ɗakin Mamin ta shirya, ta shafa manta mai gurguwa da aka kwaɓa shi da tube na pure skin, ta hakimce kan stool na mirror tana hararar locker. Ita ta rasa  irin Mami, idan ta yi wani abun sai ka ce bafulatanar daji, yanzu meye na cewa tasa sarka dan za ta zance sai ka ce ana suna ko biki, ta zumbura baki ta miƙe ta isa ga locker ta buɗe ta hau dubawa, ba daɗewa ta gano sarkar mai kyau da ita a cikin gidanta, ta ɗauko tana murmushin jin dadi, sai kuma idanuwanta suka sauka kan wata ‘yar ƙaramar battar silver mai sheƙi, a hankali ta kai hannunta ta ɗauka tana jin sha’awarta na cika ranta, ta girgizata ta ji da abu a ciki,sai ta ji tana son ganin menene, ta buɗe battar ta zazzage sai taga zobe mai kyau ya faɗo, ta ɗauko ta jujjuya taga na zinari ne sai dai ba sabon design ba ne, kai bata ma taɓa ganin irin design ɗin ba. Sheƙinsa ya cika idanuwanta, sai taji tana sha’awar gwadawa a yatsanta. A hankali ta zura shi a hannunta na hagu, ta kalli hannun taga ya mata wani irin kyau, ta yi murmushi ta kai hannunta ta shafo goshinta jin kamar abu na tafiya a gun, ta kalli hannun taga gumi take yi, sai ta ɗaga kai cikin mamaki ta kalli A.C da ke ta aiki a ɗakin. ‘To gumin me nake?’ Ta furta a ranta tana sake maida kallonta kan zoben, gabanta ya faɗi da taga kamar gizau idanuwanta ke mata, kamar sanda ta ɗauko zoben golden ne mai tsananin sheƙi. Yanzu kuma taga ya koma launin silver mai tsananin haske. ‘Koyaushe aka yi dynamic zobe?”

“Anty Biyya, Anty Biyya?”

Muryar yaro ta katse mata tunanin, sai ta ruga da gudu zuwa wajen ɗakin, ta hangoshi shi da Babansa suna hawowa benen, sai ta tafi da sauri ta ɗaga yaron sama ta shilla shi suna dariya. Sai kuma ta sauke ta ta kalli baban da ya tsaya yana ƙare mata kallo, kunya ta kamata ta sadda kai ƙasa tana murmushi.

“I lalle ana son Abokin Baba, wannan kwalliya haka?”

“Kai Yaya Dr, Allah Mami ta sakani yinta.”

“Ai bance lefi ne ba, na ganshi ma a ƙasa mun gaisa sosai, bai wani tsufa ba, sai ki dage gurin ganin baki yi wani abu marar daɗi ba, na san shi tun ina karami mutum ne mai kirki da alheri. Yanzu da na shiga gun Baba ya ce mini in tsaida ranar bikin, Mami dai ta ce nan da sati biyu, ni ma na ce hakan ya yi, inyeee! ‘Yar ƙanwata an girma.”

Ta zoɓari baki tana kwaɓe fuska hawaye har sun fara sauka, tana jin tashin hankulan duniya na kusanto mata, sati biyu fa? Sai ka ce kaza ko bazawara? Sati biyu har yaushe ta kori mai zubin ghost? Wa za ta tunkara? Ga Yayanta ma ya goyi bayan Mami, shi ya sa ko sau ɗaya bata taɓa faɗa masa damuwarta kan auren ba, ta san shi sarai duk abinda Mami take shi yake so. Amma ba za ta bari ba, ba za ta taɓa yarda Huzaif ya haramta gare ta ba, za ta yi ko menene gurin ganin ya ƙyaleta dan kansa!

“Ga Hanif zai kwan miki biyu ya tayaki hirar, ita ba ta jin daɗi ne, yauwa, kan ki wuce dan canja masa pampers ɗin, Ina jin tun safe ya yi bahaya ta kasa wankewa.” Ya furta yana miƙa mata jakar yaron ta karɓa ta riƙe hannun yaron suka yi toilet tana Mita cikin ranta. Tsabar ƙazanta yaro ɗan shekara biyu ita bata ga abin sawa pampers ba, gwara a nuna masa poo ya ringa hawa da kansa. Ta yi kwafa tana tuna wai saura sati biyu bikinta, sai kuma ta kunna ruwa ta wanke masa jikinsa ta fiddo shi waje ta koma, ta kula gefen wandonsa har ya fara ɓaci, sai ta ɗauka ta zazzaga Klin a ‘yar roba ta hau dirzawa har ya fita, ta dauraye wandon jikin famfoo ta sakale shi gefe, ta juyo ta ɗau robar da ke cike da ruwan wankin ta buɗe gun bahaya ta juye, sai ta ji ƙara kamar na ƙarfe a ciki, wani abu ya dunƙule mata a gefen ciki ya tamke tsam, ta kalli hannunta da azama taga babu zoben nan da ta ɗauka ɗakin Mami, wani gumi ya karyo mata ta leƙa ba abinda take gani sai kumfa. Tana hawaye tana kome haka ta danna gun flushin ruwan ya wuce ya zama garai-garai, ta fito a sanyaye tana tsinewa karambanin da ya kaita taɓa zoben, yanzu me za ta cewa Mami idan ta neme shi?

A can wani katafaren gida da ke da nisan tafiyar jirgi ta awa guda, wasu mutane biyu ne zaune a tsakiyar falon gidan, sun tasa wani kwamin wanka da ke girke a gurin a gaba suna kallo, cikinsa babu kome sai wata ‘yar ƙaramar Mujiya an ɗaura mata jan zare a wuyanta. A sannu suka ga mujiyar ta fara hayaƙi, suka miƙe a razane suna kallo har ta idasa ƙonewa ƙurmuss.

Ɗayan da yake tsoho tukuf ya dubi gudan yana maƙyarƙyata.”B-ba-ba’a binne wannan yarinyar da zoben nan ba, ina zobena Hashimu, ina yake, m-m-munn salwanta, ban s-so-so na mutu?”

Gudan da yake tsakanin shekaru sittin zuwa da biyar ya dube shi cikin rashin fahimta ya ce, “wacce yarinya wai, wane zoben? Ni fa Tunjim matsatalata da kai gigin tsufa, haka wai ake tsufan? Na fa kawo ka nan ne dan ka gama aikin yarona Hisen ya ture tsohon can shi ya hau mulkin ya yi yadda na yi hankalina kwance, amma tunda muka zo nan ba abinda kake yi sai zunguɗe-zunk…Wayyo!”

Ya furta da ƙarfi yana yin gefe ganin wani yanki na ginin gidan ya zabtaro ya faɗo, kan ya gama fahimta wani ya sake zabtarowa ya danne tsohoTunjim ta yadda ko yatsansa bai ragu ba, ya juya da wata irin firgita ya yi ƙofar fita daga falon, kawai sai yaga ta kama da wuta, ya zube anan yana ihu yana kiran kafatanin danginsa har matatttun sai dai ba wanda ya jjiyo shi, haka yana ji yana gani wuta ta cinye shi, ginin ya idasa rufe shi ruf!

*****

A karo na uku ta sake yaye labulan tagar tana leƙensa daga can sama, har yanzu yana nan yadda ta barshi a tsakiyar zazzafar ranar da ta kwalle a ilahirin garin na Kano. Tun ɗazun ta fita ta jawo shi filin gidan, ta haɗe rai duk maganar da ya yi taƙi amsawa, tana jin Dr. ya fita ta koma ciki da sauri a tsammaninta idan ya gaji ya tafi.

Taja tsaki mai ƙarfi ta ɗaga kai ta kalli agogon da ke kafe a bangon ɗakin Mamin. Idan lissafinta daidai ne awansa biyu da minti goma kenan a tsaye a gun, a kowane lokaci kuma daga sannan Mami za ta iya dawowa gidan taga kunun da ta dama wanda shi ne babban tashin hankalinta. Yatsunta biyu ta zura a bakinta tana tunanin abinyi tana ƙara leƙensa. Dole ne ta samu hanyar da zai tafi, amma ta yaya? Mutum ne da baya jin masifa baya tsoron aci mutuncinshi, kai ko sunan iyayensa ta kira ta zaga ba ta tunanin zai saurareta, ƙarshen abinda ta sani shi ne ya mata murmushi ya ce “Yarinta mai daɗi, ina son ki a kome da za ki yi.”

Anty Biyya na gama.”

Muryar Haneef ta katse mata tunani, ta waigo ta maka masa harara cike da takaicin uwarsu da ba tada aiki sai turo yara hutu ana sakata yi musu tsarki, yanzun fa daga zuwan kashinsa na biyu kenan gashi ta rantse bata saka masa pampers. Miƙewa ta yi ta finciki hannunsa suka koma toilet ɗin ta wanke masa. Ta ɗaga foo ɗin za ta juye ta yi flushing wani tunani ya shige ta, da sauri ta rufe ta fito da shi a hannunta zuwa jikin tagar ɗakinta ta zuge ta yadda take iya hango farfajiyar gidan gabaɗaya, ba ta tsaya wani dogon tunani ba sanin abu guda zuciyarta ta sani lokaci ya zo da za ta yiwa Abokin Baba abinda ba zai ƙara shiga lamarinta ba balle har ta zama mallakinsa nan da mako biyu, dan haka ta watso tutun gabaɗaya tun daga can sama haka ya sauka a jikinsa da saman motarsa tamkar ana ruwan tutu, ya ɗago kansa sama ya dubeta, ta kuwa kashe shi da murmushin da yake so ta ɗaga masa hannu irin sai ƙaƙa? A daidai sannan gate ɗin gidan ya hangame motar mutumin da bata taɓa tunanin wanzuwarsa a cikin gidansu ba ta kunno kai ciki. Ya yi paking ya fito yana sauke kallonsa kan mutumin da ke tsaye yana yarari cikin milk ɗin tsadadden yadinsa ya zarce da su kan nata da ke sama. Ita ma kallonsa take, idanuwanta cike da tsantsar firgici, tana jin yadda gumi ke saukowa tun daga ƙarshen gashinta yana zarcewa can cikin jikinta, kanta take girgizawa, tana takawa a hankali tana komawa baya, yaraf! Ta zube saman gadonta ta dafe saitin zuciyarta da take ji na barazanar tsarwatsewa.

Maida kallonsa ya yi kansa, idanuwansa sun kaɗa jajur dan azabar ɓacin rai. A hankali ya ƙarasa gabansa bayan ya sanya hannu ya zare rigar dake jikinsa. Ɓalle masa botiran tasa rigar ya yi ya zare masa ita ya sanya masa tasa. Hannuwansa ya riƙo zai yi magana sai dai ya gaza ji yake yana buɗe baki zai zubar da duk wani ƙwanji nasa na ɗa namiji a gidan da baya fatar ya sake tozali da ko me irin fentinsa. Runtse idanuwansa ya yi yana jin yadda ƙirjinsa ya yi nauyi da wani abu da bai san menene ba. Jansa ya yi ya tura cikin motar shi ma ya shiga ya yi wani irin ribos da wani azababben horn, Maigadin da ya bude masa gate din ya yi tsalle gefe, ya fige ta da gudun bala’I suka bar gidan.

Sai da suka yi tafiya mai nisa ba wanda ya ce uffan sai can ya ja wani numfashi ya fesar yana sanya hannu ya daki satiyarin motar da ƙarfi.

“Hankali dai…”

Alhaji Hameed ya furta.

“Ka rabu da ita! Dan ALLAH ka rabu da ita ko dan mutuncinmu!!”

Murmushi ya masa mai kyau yana sanya hannu ya dafa cinyarsa.

Abin Ya ƙara ƙular da shi ya maida kansa kan titi yana kiran sunan Allah a zuciyarsa. Shiru na ɗan lokaci ya ratsa a ilahirin motar, sai can ya ji kalamansa a hankali na zarcewa can cikin kunnuwansa suna aje kansu a inda ba za su taɓa gogewa ba.

“Da zan iya da tun a ranar farko da na ganta ba zan bibiyeta ba. Da zan iya da tun a lokacin da na gane alaƙar da ke tsakanina da ita nada girman da nemanta zai sakani jin kunya na barta. Da zan iya da na barta saboda kai Huzaif, saboda kar na ja maka zagi da aibanci da girmanka da kome a garin nan, ka yi hakuri ka ji, wannan ita ce ƙaddarar da aka yi mini fatan samunta a can wani lokaci, ina sonta a haka, ina sonta ko da ita ce silar kaini ga kushewata! Kar ka manta abu guda, duk abinda za ta yi ko zai faru ba zai taɓa kai kwatar abinda ni na yi a gare su ba!!”

“Amma na faɗa maka yarinyar nan ‘yar iska ce marar kunya ko?”

Ya furta muryarsa a dishashe.

“Tsaya na sauka!”

Ya furta yana ɗauke kallonsa daga kansa.

Wani wawan burki ya ja har sai da motar ta girgiza kafin ta tsaya.

“Idan ka isa Jami’a ka cewa Alhaji Bilya ina nemansa.”

Daga haka ya buɗe motar ya fice.

<< Hakabiyya 29Hakabiyya 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×