Skip to content
Part 32 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Karshen Tuka-Tuki

Koda ta hau saman wayarta ta lalubo ta latsa lambobinsa da kullum sune na farko a layin da kira ke shigowa. Rinni biyu ta ji ya ɗaga.

“Ka yi hakuri, domin Allah..”

Kalmomin suka fita tamkar an fisgo su.

A can ɓangarensa runtse idanuwansa ya yi da ƙarfi yana tasbihi ga ubangijin talikai a sa’ilin da sautin muryarta ya shiga cikin kunnuwansa. Sai ya ji sak Hamdiyya a wani dare da take furta irin wannan kalmomin gare shi. “_Ka yi haƙuri, domin Allah Huzaif kar ka ce baka taɓa so na ba._”

“Ina sonki da gaske Hamdiyya, me ya sa kike ba ni hak…”

“Haƙabiyya ke magana, ka dai manta sunan nan.”

Bai san a fili ya yi maganar ba sai da ya ji muryarta.

“Baby Sarauniya me ya samu muryarki ne?”

Ya furta a gaggauce yana jin kamar ya yi tsuntsuwa ya ganshi a gabanta, zuciyarshi har wani bugawa take-take fat!fat!! Tsabar daɗi.

Shiru ta yi na ɗan lokaci har sai da ya ƙagara.

“Ka haƙura…?”

Ya numfasa yana jin yadda kome na halittar jikinsa ke girgiza.

“Ki daina ba ni haƙuri, ba za ki taɓa lefi a gare ni ba, amma na gode da haƙurin ma, Allah Ya miki albarka ya cika miki burikanki.”

“Amma da mamaki…”

Sai kuma ta yi shiru jin wata nadama na daɗa baibeyeta, wai shin dama an halicci irin wannan son? Wanda take wa Huzaif da wanda Abokin Baba ke mata, kai anya ita za ta ƙara tanka Huzaif a yayin da ya zuba mata irin najasar da ta zubawa mahaifinsa?

“Kin yi shiru?”

Sassanyar muryarsa mai cike da karasashi ta katse mata tunani.

Ta runtse ido ta buɗe tana jin kamar an watsa mata dalma a tsakiyar tafin hannunta. Ta ja a’uziyya ta tattofa a a gefe da gefenta wai ko abinda take ji game da shi zai ragu. A sannu ta ce…

“Dama ce maka zan yi na yarda da lamarinka, ka faɗawa Baba ayi auren sati mai zuwa.”

Daga haka ta kashe wayar.

Ya bi wayar da kallo sororo, kafin kuma hankalinsa ya dawo jikinsa ya sunkuya ya yi sujjadar godewa Allah mai girma da ɗaukaka.

Karshen Tuka-Tuki…

Baki buɗe ta bita da kallo ganin kamar ba cikin hayyacinta ta faɗi maganganun ba. Sai dai ga mamakinta a hawa na biyar da ta taka ta juyo ta mata murmushi wanda ke nuna abinda ta faɗa ya fito ne  daga zuciyarta.

Wani yawu ta haɗiya mai ɗaci jikinta na ƙara sanyi a yayin da wani ɓari na zuciyarta ke sanyata tunanin ranar nadama. Ɗiyarta da ke cikin shekarunta na 22 ne ta hana kanta farin cikinta saboda ta cika mata nata burin! Ƙara cira kanta sama ta yi tana kallon matattalar da ta bi. A ranta take jin ko a wuta za ta ga Hameedu da dukkan ahalinsa idan ba ta ƙara izata ba, ba za ta taɓa gigin ciro shi ba balle ta kai ga yayyafa mata ruwa!!.

Koda ta hau saman wayarta ta lalubo ta latsa lambobinsa da kullum sune na farko a layin da kira ke shigowa. Rinni biyu ta ji ya ɗaga.

“Ka yi hakuri, domin Allah..”

Kalmomin suka fita tamkar an fisgo su.

A can ɓangarensa runtse idanuwansa ya yi da ƙarfi yana tasbihi ga ubangijin talikai a sa’ilin da sautin muryarta ya shiga cikin kunnuwansa. Sai ya ji sak Hamdiyya a wani dare da take furta irin wannan kalmomin gare shi. “_Ka yi haƙuri, domin Allah Huzaif kar ka ce baka taɓa so na ba._”

“Ina sonki da gaske Hamdiyya, me ya sa kike ba ni hak…”

“Haƙabiyya ke magana, ka dai manta sunan nan.”

Bai san a fili ya yi maganar ba sai da ya ji muryarta.

“Baby Sarauniya me ya samu muryarki ne?”

Ya furta a gaggauce yana jin kamar ya yi tsuntsuwa ya ganshi a gabanta, zuciyarshi har wani bugawa take-take fat!fat!! Tsabar daɗi.

Shiru ta yi na ɗan lokaci har sai da ya ƙagara.

“Ka haƙura…?”

Ya numfasa yana jin yadda kome na halittar jikinsa ke girgiza.

“Ki daina ba ni haƙuri, ba za ki taɓa lefi a gare ni ba, amma na gode da haƙurin ma, Allah Ya miki albarka ya cika miki burikanki.”

“Amma da mamaki…”

Sai kuma ta yi shiru jin wata nadama na daɗa baibeyeta, wai shin dama an halicci irin wannan son? Wanda take wa Huzaif da wanda Abokin Baba ke mata, kai anya ita za ta ƙara tanka Huzaif a yayin da ya zuba mata irin najasar da ta zubawa mahaifinsa?

“Kin yi shiru?”

Sassanyar muryarsa mai cike da karasashi ta katse mata tunani.

Ta runtse ido ta buɗe tana jin kamar an watsa mata dalma a tsakiyar tafin hannunta. Ta ja a’uziyya ta tattofa a a gefe da gefenta wai ko abinda take ji game da shi zai ragu. A sannu ta ce…

“Dama ce maka zan yi na yarda da lamarinka, ka faɗawa Baba ayi auren sati mai zuwa.”

Daga haka ta kashe wayar.

Ya bi wayar da kallo sororo, kafin kuma hankalinsa ya dawo jikinsa ya sunkuya ya yi sujjadar godewa Allah mai girma da ɗaukaka.

ƘARSHEN TUKA-TUKI.

Ƙarfe Sha biyu da Arba’in da biyar 12:45am agogon wayarsa ya buga. Da sauri ya tattara kayan gwaje-gwajensa ya fito daga cikin ward ɗin ya doshi motarsa cikin duhun daren. Ya shiga cikin motar zai tada ta kenan ya ji an sako hannu ta bayansa an riƙe masa hannu. Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi! Sai dai bai razana ba ya ɗaga hannunsa alamun saranda yana miƙa mukullin. Yana jin sa’adda aka yi murmushi mai sauti kafin ya ji muryarsa na cewa “Na girmi wannan yanzu, juyo kaga bakon naka.”

A hankali ya sanya hannu ya kunna fitilar motar hasken ya haska masa fuskar mutumin da bai taɓa mantawa ba dan kuwa ba abinda ya canja na halittarsa sai ratsin farin gashi da yawan shekaru suka kawo.

“Shekara a shirin da biyu ko? Yaya ka ganni?”

Murmushi ya yi mai kama da yaƙe yana jin tsoronsa na gushewa.

“Kana nan yadda kake da alama ko a aiki baka canja ba tunda gashi ka buɗe motata a yayin da take rufe.”

Mutumin ya bushe da dariya yana shafa bajajjen hancinsa.

“Na sauya kome a tun ranar da na sha kulki a hannunka. Ka ga kuwa kai ka canja sosai, a da can na sanka mutum mai shegen tsoro, na za ta idan ka ganni a motar nan suma za ka dinga yi ina farfado da kai.”

“A haba habhabaa dai?”

Ya furta yana murmusawa.

“Yauwa Dr Haadiru ko?”

“Za ka fi ni sani tunda ga ka cikin Asibitina.

“To Ni sunana Ado Maɗaci”.

Ya furta yana miƙa masa hannu su gaisa.

“Ina saurararka da abinda ke tafe da kai a cikin talatainin daren nan.”

“Na zo ne na roƙe ka da ka bani maganin da ke cikin shantun nan na sha asirin jikina ya warware kafin ku yi kuskuren da ko ni ba zan taɓa yafe muku ba.”

Dr. Haadirr ya kafe shi da ido.

“Ban gane ba fa?”

“Kar kai mamaki idan na ce maka ina bibiye da rayuwarku a tun wancan lokacin…”

“Babu mamaki…”

“To mamakin na tafe a lokacin da za ka ba ni maganin nan. Dr. Ka taimaka mini na samu maganin nan kafin bakin Alƙalami Ya Bushe. Ka sani a yanzu girmana ya kai inda ba zan iya cutar da wani ba. Kalli nan.”

Sai a sannan ya yaye mayafin jikinsa sai ga dungulmin gwuwowinsa sun bayyana. Da sauri ya haska fitilar wayarsa waje ya hangi keken guragu can gefen motar. Jiki a sanyaye ya kallo shi. “Duk da bangane abinda kake nufi ba sai dai fa ba na tunanin za a samu shantun nan a halin yanzu. To kai banda abinka me za ta yi da shi a yanzu, ba ka ga yadda rayuwa ta sauya ba, ba na zaton ma idan ta ganka a yanzu za ta iya shaidaka balle har ta tuna lalurar da ta saka ma. Sannan ya za ai na yarda ba za ka cutar da wani ba? Alhali nasan burinka a tunda shi ne ka kasheta…”

“Tana sane da Ni, bata taɓa mantani ba daidai da kwayar zarra! Sannan, gwara kisa da abinda zai faru, ka taimaka mini, da gaske babu wanda zan cutar, bazan ma iya ba.”

Haadirr ya bishi da kallon mamaki.

“Ina nufin idan har za ta manta Haƙabiyya to tabbas za ta mantani.

Kai dai ka taimaka ka bincika mini tunda ba kada iyaka da gidan. Kar a wuce kwana bakwai dan Allah, kar ka yi kuskuren da gaba kai za ka yi nadamarsa.”

Numfashi ya ja ya fesar yana nazarin maganganunsa, wani ɓari na zuciyarsa na gargadinsa da kul ya yarda da shi.

“Shi kenan, in SHA Allah zan duba duk da ba na zaton za a samu, sai dai ina fata.”

“Yauwa, to taimaka mini na hau kekena.”

“Da yake ni na taimaka maka ka shigo nan ɗin nan ko.”

Ya yi murmushi.

“Kasan dabara tana ƙarewa kura ai.”

Attajirin da ake yiwa zaton wata mummunar lalurar ta hana shi aure a yau zai angonce tare da ɗiyar babban abokinsa. Wannan shi ne babban labarin da ya cika garin na Kano har a kafafen yaɗa labarai a safiyar ranar ta jumma’a har zuwa ƙarfe ɗayan ranar, lokacin da unguwar ta cika ta tumbatsa da mutane, ga tarin dandazon maroƙa a gefe guda. Hatta Huzaif ba a bar shi a baya ba ya ci ado cikin Milk din shaddar da suka yi anko da Baban nasa, sai dai ya saye idanuwansa cikin baƙin gilashi Allah kaɗai yasan abinda ke ɓoye cikinsu. A can gefe angwaye ne cikin attajiran abokansa da surukinsa ana ta cafkewa cikin farin ciki. 

Bayan an idar da sallar juma’ar ne aka fara hada-hadar ɗaurin auren, anja fatiha an shafa liman ya buƙaci sadaki a sannan ne Bawa ya karkace ya shafi aljihunsa ya ji babu alƙawarinsa a ciki, ya waiwaya ya kalli Huzaif, sai kuma ya bada umarni a ɗan dakata, ya yafito Huzaif ɗin ya tura shi cikin gidan dan ya karɓo masa sisinsa na gwal daya daɗe yana tsuminsa gurin Zawwa.

Yana fita daga masallacin Maɗaci na gunguro kekensa gurin, akai sa a mutane nata buɗa masa hanya har ya isa tsakiyar masallacin yana ta hanga kai ko zai ga Alhaji Hameedu sai dai bai ganshi ba, ganin lokaci na ƙurewa gashi bai gane abinda ake jira ba yasa ya buɗe muryarsa da ƙarfi ya ce, “ku dakata da ɗaurin auren nan, yarinyar da kuke ɗaurawa aure ɗiyar wanda zai aura ce, jininsa ce.” Gurin ya yi wani irin tsit! Sai a sannan ya hange shi acan gefensa. Faɗowa ya yi daga kujerar ya ja jikinsa har ya isa gabansa gabansa, ya kama hannuwansa biyu ya riƙe a yayin da wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa. A cikin kunnensa ya ƙara jaddada masa Haƙabiyya ɗiyar sa ce ta cikinsa, Hamdiyya ba ta mutu ba har ya binne ta duk da kuwa ya fasa maƙogwaronta. Zawwa, ita ta zo ta buɗe kabarin ta farke cikinta ta ɗauko ɗiyar, shi kuma ta masa asirin da ba zai taɓa iya bashi labarin nan ba har sai an ƙarya!Makarin kuma na hannu ita ɗaya tal!”

Alhaji Hameed ya cira kansa sama ya dubi tsakiyar idanuwan Bawa da labarin ya saka shi miƙewa tsaye, ya waiwaya ga liman da shi ma ke tsaye, ya buɗe bakinsa da wata irin dakiya ya ce “ɗaura auren da yarona Huzaif.” Hawaye suka sauko zuwa ƙunduƙuƙinsa, ya kai hannunsa guda ya dafe saitin zuciyarsa, sannu a hankali kuma sai fuskarshi ta faɗaɗa da wani irin murmushi mai taushi, ya sake kallon Bawa wani haske mai ƙarfi ya cika idanuwansa, sai ya hangi kamar Hamdiyya cikin hasken tana masa murmushi tana miƙa masa hannu, sai kawai ya ɗaga nasa ya miƙa mata. Bawa ya shiga girgiza masa kai da sauri yana ɗaga ƙafar katakonsa cikin sassarfa yana takawa zuwa gare shi, ya duƙa a gabansa ya ƙanƙame hannun da yake zaton shi ya miƙowa ya jashi cikin jikinsa ya rungume shi ba tare da yasan gangar jikin ya riƙa ba! Ruhinsa ya tafi ga mai shi a tun sa’adda ya masa murmushi! “Ban sani ba! Ba mu sani ba Hameedu!!Wallahi bansani ba!!!” Sakin da yaji jikinsa ya yi ya saka shi ɗago da fuskarsa a gigice yana kiran sunansa. Ga dai murmushi a fuskar Hameedu tamkar zai ce wani abu, sai dai fa idanuwansa a rufe suke ruf! Rufewar da har abada ba za su ƙara buɗewa ba!

A can cikin gida lokacin da Huzaif ya shiga ya tarda mata nata hayaniya kan Amarya tun jiya da ta shiga ɗakinta ta rufe kanta a ciki ba ci ba sha, shi dai tsaki ya yi a zuciyarsa ya shiga laluben Zawwa har ya gano ta a can madafi ya faɗi saƙon, ta tafi da sauri ta kawo masa. A sa’adda sisin ya shiga tafin hannunsa ne suka ji muryar wani maroƙi mai shegen karaɗi na jawabi. “Allah mai girma da ɗaukaka! Da tuni yau anyi auren ‘ya da uba cikin rashin sani, ashe dai amarya Haƙabiyya ɗiya ce ta jini gurin Alhaji Hameed Siddiq, kai! Allah ya taƙaitamu da jin kunya!!”

A tare suka dubi juna jikinsu na rawa ko ta ina kafin su maida hankalinsu kan matattakala jin an buɗe ƙofa da ƙarfi. Da sauri suka yi gun, ita ce ta zame take gangarowa daga matattalar benen bakinta har ya fashe yana jini, cikin wata irin gigita Huzaif ya yi kanta inda ta idasa faɗowa a tsakiyar ƙirjinsa a sume. Rungumeta tsam! Ya yi, cikin ihu ya hau kiran sunanta yana kiran a kawo masa ruwa.

Mami kam ƙamewa ta yi anan gun har zuwa sa’adda ta ji hannun Bawa ya danƙi nata yana janta zuwa cikin ɗaki. Tsura masa ido ta yi tana ganin yadda hawaye ke sintiri a fuskar tsoho Bawa.

Sai kuma ya fashe da dariya tamkar zautacce yana tari, yana nunata, yana girgiza kai hawayen na daɗa jiƙa gaban rigarsa, da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce da ita.

“Jinin Hameedun kika raina kika shayar da waɗannan gororin naki guda biyu Zawwa! Yanzu kuma sai me kike so? Ga dai Hameedu can ya koma ga mai shi ya bar miki duniyar a naɗeta tare da ke a dunƙule!! Ga dai Hameedu can ya tafi ba tare da ya furta abinda ya zo ransa ba a bayan jin labarin ba kuma tare da ya furtawa ɗiyarsa kalma guda irin ta ɗa da mahaifi ba. Hameedu ne kwance a tsakiyar masallaci yana yi mini murmushin tuhuma. Murmushin da har abada ba zai bar bayyana a saman fatun idanuwa ba. Kinsan dalili? Saboda ban kai ga furta masa ban sani ba, ban kai ga sanar masa ba zan taɓa aikata haram domin ɗaukar fansa ba ya tafi. Hameedu ya bar mini dafin da ba zan taɓa daina jin raɗaɗin sa ba, dafin da ya fi azabar da na ji a yayin da za a raba ni da ƙafata guda, dafin da ba zan bar tuna ya tafi yana kallona a azzalumi ba, har ya mini murmushi a saboda ya nuna mini ni ne silar ajalinsa, ni ne na bar shi zai auri ɗiyar cikinsa!!! Wannan shi ne sakamakon ƙiyayyarki, sakamakon dukkan mutum marar afuwa. Halittar da kika tsana tun kina ƙanƙanuwarki ita ce kika raini jininta kika shayar da jininta kika kafu da so da ƙaunar jininta! Shin akwai abinda zai fi wannan tsayawa a ruhi, ko kuwa akwai abinda zai fi wannan tsayawa cikin hankali? Kin sha cewa ko jinin Hameedu kika gani a wuta izata za ki yi ko? To gasu can su biyu tal! Suka rage jinin Hameedu a duniya, guda ɗan Yayansa ne daya raina da hannunsa, guda kuma jininsa ne na cikinsa, sai ki ɗauke su ki sanya a cikin akwatin al’amoudi ki jefasu tsakiyar tekun maliya ki ɗauki mukullin ki haɗiye shi a cikin cikinki! Wai ni yau bari na tambayeki Zawwa! Shin wai Hameedu ƙafar Habu Maharbi ya cire ko kuwa ta Bawa? Shin wai Hameedu dukiyar Ladi ya cinye ko kuwa ta Bawa? Shin shi Bawan me yake zame miki ne banda miji? Shin akwai wani jini guda ko da na halittar kaza ne da kika dasa a tsakaninki da Bawan? Kai! Ko kuwa akwai halittar mutum irin wacce uwar Haadiru ta bashi, shin ko kuwa banda abinda na sani akwai wani abu tsakaninki da shi Hameedun..!?”

Sai anan ta cira idanuwanta sama ta dube shi a yayin da wata kwalla guda ta sauko daga kurmin idonta.

“…I ZAWWA! Na ce akwai ne? To me ya sa za ki gina rayuwarki a ƙiyayyar mutum guda, wai ban ci gaba da rayuwa ba a bayan na rasa ƙafar? Ko kuwa ban rayu ba a bayan ya ɗauke dukiyar, shin yanzu ba cikin arziƙi nake ba me kika nema kika rasa? To bari ki ji wani abu da ba ki sani ba. A sa’adda ɗiyarki ta gane kina son ɗaukar fansa ne saboda ki maido dukkan dukiyarsa taki shi ya sa kika matsa da auren. Da kanta ta neme shi da ya maida kome nasa da sunanta ya danka mata a hannu idan yana so ta aure shi. Kinsan me ya yi? Take ya fara waya yana bada umarnin a fara tatttara masa kome nasa saboda ya bata. Ita da kanta ta ji tsoro ta ce masa gwada shi kawai ta yi. Wannan abin wancan satin ya faru, tun kuma a sannan na gane Hameedu babu kome a gabansa sai Haƙabiyya, ya kuma shirya zama faƙiri saboda ƙaunarta! To kuma kinsan labarin da na samu a yau gurin Aminin Maigarin Tanɗau da ya zo ɗaurin aure? Babu wani agaji daya taɓa zuwar musu balle har a kasabta mana miliyoyi a aiko mini da kasona. Da Jin wannan labari kaina ya shiga duhu, kinsan abinda ya warware mini duhun nan mintuna biyar da suka gabata a sa’adda aka fiddo da gawar Hameedu? To shi wannan gurgun da ya zo da labarin haihuwar Haƙabiyya, shi ya dube ni dan na yafewa Hameedun, ya kuma faɗa mini Hameedun ya taɓa aiko shi gurin Haadiru ya kai masa dukiya mai yawa ya faɗa masa saƙo ne daga maigarin Tanɗau! Zawwa!! Dukiyar dai da muka gina, kike ci kike sha, tana daga cikin kasona da kike jin ciwon Hameedu ya sace!!!

Ganin yadda ta zare ido tana dubansa da zallar mamaki ya saka shi jan tsaki ya juya kawai a sanyaye ya bar mata ɗakin.

Lalubar kujera ta yi ta zauna tana dafe ƙirjinta da take jin wani abu na lumewa cikinsa. Ba mutuwar Hameedu ba ce ta fi damunta, abinda ya fi damunta shi ne ta yadda za ta cewa Haƙabiyya ita ba mahaifiyarta ba ce ta nasaba, abin da ciwo sosai! Sai dai kuma ai nononta tasha, ta sani wannan soyayyar ta uwar na nan daram! A tsakaninsu. Ba kuma nadamar abin da ta yi ba ne yafi damunta, abinda ya fi damunta shi ne ta yaya za ta karkato da hankalin ɗan Hameedu kan Haƙabiyya ya aure ta ba tare da yana kallonta a makashiyar ubansa ba, ita kuma ta samu ta wanke kanta gurin yarinyar ta hanyar bata duk abinda take so, shin anya ma yarinyar za ta ƙara kallonta a cikakkiyar ‘yar Adam mai zuciyar tausayi da manta sharri? Anya yarinyar za ta yarda cewar bata san Hameedu ubanta ba ne duba da tsanar da take gwada masa a gabanta? Ta ji zuciyar tata na daɗa zama dutse maimakon gari, tabbas ta yarda da maganar kakanta da yake yawan ce mata a duk ranar da aka kawo masa ƙararta, Idan ba ki ji wasa da wannan dabi’ar za ta bi ki har ƙarshen rayuwarki! Akwai da yawa-yawan mutane da ba su taɓa canja halinsu kome zai faru!!

Ke nan ita tana cikinsu, halinta ya kafu inda bai taɓa barinta har abada!

A sannu ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana jin wani ƙulli da ta rasa gane in da yake sama da shekaru ashirin da biyar na warwarewa. Ga mamakinta sai ta ji ranta ya yi wani irin sanyi. A hankali ta sanya yatsanta ta ɗauke ‘yar kwallarta tana jin wata irin nutsuwa na ratsata. Lumshe idanuwanta ta yi tana tuna ranar da ta fara ganinsa a garinsu. A wani yammaci sun dawo daga farauta ta hange shi can yana haɗa karare, ta rugo da gudu gare shi tasha gabansa cikin rawar kanta da yarintarta ta shiga ƙare masa kallo tana washe masa haƙora sai kuma ta nuna shi da wata kibiyar iccenta tana karkaɗawa.

“Caɓ! Kana da kyau kamar balbelar da muka harba ɗazu, idan na girma za mu yi aure ko?”

Harara ya ɓalla mata ganinta duƙun-duƙun hancinta cike da majina, da yanayin suturarta ya gane ɗiyar maharbin garinsu ce.

“Tafi gida maza a miki wanka, ji ‘yar ƙarama da ke kina batun aure.”

Ya taɓe baki.

“Ni ko ana aure ba zan auri ɗiyar maharbi ba!”

Har ta je gida ta yi wankan tana kukan wannan maganar tasa. Shekara uku bayan haka aka ɗaura mata Bawa.

Shi Hameedu ya manta, ba zai ma taɓa tunawa ba saboda wasa ya yi da ita. Bai san sunanta ba, bai taɓa ganinta ba sai lokacin bai ma san ita ce ke auren Bawa ba tunda bai san adadin ‘ya’yan Habu Maharbi ba , kai bai ma tunata ba balle ya sani ɗin, bai kuma ƙarewa fuskarta kallo ba balle ya gane ta dan ta zama Amaryar Bawa. Ita kuma ba ta manta ba kai bata ma taɓa mantawa ba, asalima wannan na ɗaya daga cikin toshen tsanarsa!..

Ta tsura ma wani ado mai hoton sunan Allah ido tana harhaɗa abinda ta iya hange daga nan inda take zaune a cikin zuciyarta.

“God Is Great!”

Zahiri kalmomin suka bayyana a saman laɓɓanta!

A cikin zuciyarta kuma, a can wani loko da bata san da wanzuwarsa a dabi’arta ba, sai ta ji tana masa fatan samun rahma.

Ƙarshe!

ALLAH KA RABA MU DA MUMMUNAR ƘIYAYYA!

SAI MUN HAƊU A(FITILAR SHARRI!)*

NA GODE WA KAINA.

NA GODE MUKU MAKARANTA.

NA GODE WA FIKRA.

<< Hakabiyya 31

1 thought on “Hakabiyya 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×