Skip to content
Part 4 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Gyalen ta fara zamewa kafin tasa hannu ta cisge ɗankwalin kanta, ta zube ƙasan bishiyar tana sauke numfarfashi kamar wacce ta yi gudun famfalaƙi. Hannunta ta duba sai kuma ta yi jifa da ƙyallen a tsoroce tana binsa da idanuwa kamar wacce ke zaton yana dira a ƙasa zai ɓacewa ganinta. Dafe ƙirjinta ta yi tana matse cinyoyinta jin mararta na daɗa ɗaurewa a kowane lokaci za ta iya sakin fitsarin.

Ta ƙara bin ƙyallen da kallo tana jin nadama na baibaiyeta, kome ya hanata nuna masa tsoronta? So mana wata zuciyar ta nusar da ita. Amma kuma ta furta masa abinda ba za ta taɓa iyawa ba, ita fa har yanzu da ta yi jifa da ƙyallen ji take kamar an zuba ruwan dalma a tafin hannunta. Allah kaɗai shaidarta ba za ta taɓa iya aikata abinda ta furta za ta yin ba. Sai dai kuma a kowane motsi idanuwanta na hasko mata hawayensa, na hasko mata girman tashin hankalin da yake ciki, anya ta cika masoyiyar gaskiya idan ta yi shakulatin ɓangaro da larurarsa? Shin ba ta yi butulci ba? To menene mafita, me za ta yi ta nuna masa girman soyayyarsa a rayuwarta? Ko ta bazama ta nemo masa kuɗaɗen?

Hamdiyya ko duka ƙauyenmu zan siyar ba za su dawo mini da abinda ke cikin jakar ba…. Wasu zantukansa na kusan ƙarshe a jerin bayanansa suka yi sururu zuwa cikin kunnuwanta. Ai sai ta cije baki tana jawo dankwalinta ta fara goge gumin daya jiƙa dokin wuyanta.

Cikin rashin sanin abin yi ta miƙe ta fara tafiya a hankali tana daɗa dukunkune ƙyallen a hannunta, a sannan ne sunan wata ƙawarta guda ɗaya tal! Ya faɗo mata a zuciya, ta ja ta tsaya tuna tabbas Hadiyya na da kaifin tunanin da za ta iya bata shawarar abin yi, sai dai kuma sun yi faɗa watanni uku da suka gabata a ranar da za su bar makarantarsu ta kwana. Tun daga ranar kuwa ko a hanya suka haɗu harara ke gama su. Amma kuma ta san duk wannan abin jiranta take yi ta mata magana su shirya, dan haka ta juya ta bi hanyar da za ta sadata da gidansu Hadiyyar.
*

Tunda ta fara bata labarin har ta kai ƙarshe bakinta ke hangame, ganin har ta ƙare amma tana ƙame kamar wacce aka zarewa laka ya sakata saka hannu ta haɗe mata labban nata guri guda. A lokacin ne ta yi firgigit ta ja baya zuwa can ƙuryar katifarta tana leƙen cikin hannunwan Hamdiyya.

“Wai menene haka kike yi mini kamar kin ga wata dodo.”

Da ƙyar ta buɗe bakinta ta ce da ita.

“Ina nuna miki ne da ki tsaya can inda kike mu yi duk maganar da za mu yi ba tare da hannunki ya zo jikina ba, wai ma kika ce mini saboda kina son sa kika karɓi ƙyallen dan ki zuba masa jinin al’adarki majnuniya?”

Ta kafeta kawai da idanuwanta tana gyaɗa mata kai.

“To wawiya shashasha wacce aka yi rabon tunani babu ita, ba ki da labarin a cikin shekarar nan babu labarin da ake yi sai na shigowar ‘yan mafiya? Har ta kai ko a hanya kika ga Mai Yalo kika tsaya siya sai dai ki ga kan ki a Injin ‘Yan Yankan Kai a maidake kuɗin America. Yanzu da kina karɓar Ƙyallen kika zama kuɗi wa gari ya waya, da kin tafi kenan ba tare da mu muna da labarin abinda ya faru ba.”

Ta bi ta da kallo a tsorace sai kuma ta miƙe tana matse mararta..


“Wallahi banda labarin nan, ke bari na yi fitsari…”Ta furta tana ficewa da sauri daga ɗakin.

“To yanzu ya kike ganin za a yi, me zance masa, amma fa Hadiyya na yarda da Huzaif idan da abin cutarwa ba zai taɓa kusantata da shi ba, ke kanki shaida ce, naga kin yaba da halinsa tun lokacin da yake zuwar mana makaranta.”

“Idan kuma shi ma yaudararsa suka yi suka ba shi fa, bai san mene ba? Ke wai ma tambayata kike yi ya za a yi da shi, ai kinfi kowa sanin Ashana zan ɗauko mu ƙyasta masa ya ƙone ke ko tokar a ruwa za a zubata yadda ba mai ganin ɓurɓushinta.”

“Hadiyya ba zan iya ba, kin sani abin nan daga hannun Huzaif ya fito, idan na kona shi in ce masa me?”

“Ki ce masa ya ɓace, kin neme shi kin rasa, ƙila matar Kawu ta share.”

“To shi kuma ya kike so ya yi da rayuwarsa? Ya sha ce mini saboda aikin nan ya baro garinsu mai nisa ya taho nan ya yi yaƙi da jahilci ya koyi Ingilishi dan kawai ya yi aiki, ya sha ce mini Idan ciwon mahaifiyarsa ya tashi sai ya zagaye kaf ƙauyensu ba mai taimaka masa da kwabon da zai sai mata magungunanta masu tsada. Ya kike so ya yi idan ya rasa aikin nan a dalilin wani abu ƙarami da ni zan iya sama masa?Ni kam zan tafi, dama zuciya ta ce ta kasa nutsuwa da lamarin shi ya sa na zo gurinki ko kina da wata dabarar.”

Ganin ta juya ya sakata saurin riƙota tana girgiza mata kai, gani take yi tana tafiya shi ke nan har abada ba ta ƙara tozali da ita. Ita kam da hakan ta faru gwara su dawwama suna faɗa da hararar juna, ko banza tasan dai tana rayuwa kusa da ita. Dan haka ta jawo ta suka dawo bakin katifar suka zauna.

Shiru ta yi tana nazarin abin yi, sai can ta ɗago da sauri fuskarta a sake.

“Kinsan me za a yi? Mu fara gwada ƙyallen, ba dai jini ake so ba? To ko jinin kaza mu zaba masa idan muka ga ba abinda ya faru, sai ki yi ƙunzugun da shi.”

“Kina ganin hakan ba zai lalata laƙanin dawowar jakar ba?”

“Ke ba zai lalata ba, ƙila ma muna zuba jinin kazar ki ga jakar ta dawo, kika sani ma malamin ko kawai shi jini yake so kowanne iri ne.”

“Kai Allah har na ji daɗi, Dan Allah Hadiyya mu daina faɗa mana.”

Ta furta fuskarta a washe.

Zungirinta ta yi tana harararta, “tashi ki bar mana gida, ban huce ba fa.”

A tare suka ƙyalkyale da dariya. Sai kuma ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana dubanta.

“Ke kamar fa jiya Lauratu ta can bayan layi ta haihu, bari ranar sunan idan aka yanka rago sai mu dangwali jininsa mu gani.”

“Shi ke nan kuwa ta zo gidan sauƙi, dama ina ta tunanin inda za mu yanka kaza ba tare da an sani ba, to mu haɗu ranar sunan kawai.”
Hadiyya ta furta tana miƙewa.

*****

“Kin ga dan baƙar rowa a rariyar tsakar gidan za su yanka ragon.”

“Mu shiga kawai ai duk yan unguwa na ciki.”

Hamdiyya ta ba ta amsa.

Suka kutsa kai zuwa tsakar gidan daidai lokacin da aka kayar da ragon aka zizara masa wuƙa.

Zungurarta Hadiyya ta yi dan ta ƙarasa gurin, ta dube ta idonta na kwal-kwal da kwalla, “ke Allah tsoro fa nake ji…”

“Ke dillah ba gwadawa za mu yi ba, Allah ya gama yankawa ya kwararawa  jinin ruwa ya bi rariya kin huta, ki ƙarasa kawai ki yi kamar za ki ɗauki buta ki jefa ƙyallen kan jinin mu gani.”

Ta saki hannunta ta fara takawa a hankali zuwa gurbin da mahaucin yake.

Ita ma ta ɗan ja baya tana leƙenta ƙirjinta na matsanancin bugu. A lokacin ne ƙyallen da ta saki daga tsaye ya dira jikin jinin da ke malale a bakin rariyar, ta ja baya tana ganin lokacin da jinin ya yi wata irin kumfa yana tattare kansa guri guda ya dunƙule kamar curarriyar fura ya saita kansa zuwa saitin inda aka yanka wuyan ragon! Tamkar an saka gam an haɗe wuyan ragon haka ragon ya zabura ya yi fatali da mahaucin da ke duƙe kansa ya miƙe tsaye ya yi wata irin girgiza yana kallon saitin da Hamdiyya take, idanuwansu suka haɗu guri guda, kafin kuma shi da ƙyallen su ɓace ɓat! Tamkar ɗaukewar ruwan sama a tsakiyar sahara. Wuƙar hannun mahaucin ta silale daga hannunsa ta iso dandaryar ƙasar, daga bisani shi ma ya kife kanta a sume. Hamdiyya da Hadiyya suka runtuma ɗaki a guje suna sakin ihun kuka da kururuwa.

“Rago ya ɓace!”

“Rago ya miƙe ya haɗe kansa!!”

Shi ne ɗaukacin abinda mutunen gidan sunan ke furtawa suna sheƙawa a guje da rige-rigen ficewa daga gidan.

KANO 2018

Idan har wannan duhun shi ne duhun kabarin da ya ji ana bada labarinsa a can wata duniya da ya gaza tuna ko da sunanta, to tabbas zai dawwama yana kiran a maido shi cikin duniyarsa shi kuma zai tafi ga wani tudu ko da na saman dutse ne ya yi ɗaki a bisansa ya shiga ya fara bautawa mahalliccinsa har I zuwa ranar kushewarsa! 

Ga dai bakinsa na motsi yana kira da dukkan ƙarfinsa a maida shi cikin rayuwarsa zai gyara gabaɗaya lefukansa sai dai fa a cikin kunnuwansa baya jin sautin muryarsa haka baya jin danshin hawayensa da yake jin saukarsu a dukkan wata gaɓa ta jikinsa. Bai san adadin daƙiƙun da ya kwashe a wannan yanayin ba ya dai ga sa’adda wani haske daga can wata kusurwa cikin kusurwowin da bai san yawansu ba ya bayyana tamkar ratsowar hasken rana a jikin hujjajjen labule. A cikin hasken ya hangi ƙafa, ƙafar ma irin ta mutum, sai dai an datseta daga jikin cinyarta da gangar jikinta. A jikin ƙafar akwai wani rufaffen takalmin danƙo irin wanda ya taɓa sani a wani wurin da tunaninsa ya gaza hasko masa. Tsoro da firgicinsa bai yawaita ba sai da ya hangi ƙafar na tahowa gare shi da wani irin taku mai ƙarfin da ke fita da sautin kukan mutum. Bai san ya juya cikin matsananin duhun yana zabga gudun bala’I ba sai da ya waiwaya ya hangi cinyar ta biyo shi ita da wannan hasken jini na bulbula daga gaɓar da aka rabata da gangar jikinta. Bai fahimci jinin shi ne hawayenta ba sai sa’adda ya ji wata murya da ta taho daga inda take na kiransa da ya maidata jikin cinyarta da gangar jikinta.  Cikin wani irin matsanancin firgici ya ƙara ƙaimin gudunsa a yayin da a kowane takunsa da zai ɗauke ƙafar ce ke sauke tata akai. A sa’adda ta cimma shi ne ta daka tsalle ta dake shi a baya ya faɗi tim! Ta gabansa haƙoransa na haɗuwa da ƙasan wurin suka yi nasu guri. Yana gani ƙafar ta tako ta jikinsa ta tsaya a tsakiyar ƙirjinsa tana tsiyayar jini, zugi da azabar raɗaɗin da yake ji a bakinsa ya hana shi taɓuka kome.

“Kai maidani jikin cinyata jikin gangar jikina kafin ka mutu!”

Ya ƙara jin sautin muryar ya fito daga saitin da ƙafar take. Runtse idanuwansa ya yi da ƙarfi ganin ƙafar ta sake daka wani tsalle za ta faɗo a jikinsa. Firgigit ya yi ya buɗe idanuwansa yana tashi zaune a matuƙar tsorace kan tafkeken gadon nasa  mamakin abinda ya saka shi komawa barci bayan sallar asuba na baibaye shi. Jikinsa na rawa ya kai hannunsa ya shafo bakinsa ya ji babu kome sai dai fa zai iya rantsewa da Allah kan ya ji ƙasa-ƙasa a tafin hannunsa, da sauri ya kunna fitilar gefen gadonsa yana ƙarewa jikinsa kallo, sai kuma ya miƙe ya shige cikin toilet ya tsaya gaban madubi yana kallon fuskarsa. 

A sannu ya dawo gefen gadon ya zauna yana riƙe kansa da hannu biyu jin kamar zai dare dan azabar damuwa. Ya daɗe yana ganin abubuwan tsoro da jin labarinsu sai dai fa bai taɓa cin karo da irin wannan ba ko a cikin tsatsunoyoyin mutanen farko. Abu ne muraran da ya gama sanin toshensa ake sake nuna masa har a cikin mafarkinsa. Shin me zai kira haka rahma ko baiwa? Ke nan ba ƙaramar baiwa ba ce ga mutumin da zai na ganin waɗanda ya zalunta a cikin mafarki? Ba kuma ƙaramar rahma ba ce ga mutumin da zai farka daga mafarkinsa ya dinga jin nadamar abinda ya aikata har ya janyo masa yin mummunan mafarkin na cukurkuɗa ruhinsa da gangar jikinsa. A cikin kansa yake jin girman haƙƙin mutumin da ya zalunta na masa gingiringim! A kuma kullum safiya a sa’adda hantsi ya dubi ludayi wani ƙunci da azabar ɓacin rai ke sabunta kansu cikin zuciyarsa har ya gagara kurɓar ruwa domin sanyaya ruhinsa, har kuma ya gagara yin mu’amala mai kyau da jama’arsa, har a dalilin haka baya iya fitowa daga gidansa sai bayan 12:00 na rana. Duk mene dalili? Saboda a irin wannan lokacin ne mutumin da ya zalunta ya rasa wani abu mai muhimmanci a halittarsa duk ta silarsa, silar son zuciyarsa, silar ƙaunarsa ga halittar da ta kawo shi cikin duniya. Halittar da duk abinda ya aikata dominta bai amfane shi da kome ba. Bai kuma ji kwanciyar hankalin da ya bazama cikin duniya domin dawwamar da shi a cikin rayuwarsu ta su uku kacal! Sama da shekaru ashirin(20) kenan. 

Shin wai ta yaya zai iya tsayuwa a gaban mutumin da ke amsa sunan Bawa Ɗan Malle domin neman gafararsa?Ba Bawa kaɗai ba, baya jin kafatanin zuri’ar Bawa za su dube shi da rahma. Sai dai fa ba zai gaji ba, yanzu ya fara nemansa da dukkan zuri’arsu, da taimakon ubangijinsa zai nemoshi ko da kuwa yana binne ne a ƙasan ƙasa dan ya nemi gafararsa, dan haka ya jawo wayar da ke gefensa ya latso number mutumin daya bawa  haƙƙin kula da masu shige da fice a can tsohon ƙauyensu domin kawai ya ji zuwan Bawa cikin garin duk da kuwa an tabbatar masa shekaru ashirin kenan ba a ƙara jin ɗoriyarsa ba tunda ya kwashi iyalinsa suka tafi. A cikin zuciyarsa yake jin wannan kiran da zai yi shi ne na ƙarshen da zai sada shi ga muradinsa!

<< Hakabiyya 3Hakabiyya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×