A karo na uku ya ƙara duba agogon hannunsa yana jan tsaki cikin zuciyarsa. Tattara takardun gabansa ya yi gefe, ya miƙe ya doshi bishiyar da yasan tana zama ita da abokan karatunta. Tun daga nesa ya san bata cikinsu dan haka yaja ya tsaya kansa na daɗa zafi. _To wai ta zo makarantar ɓoye masa take yi ne ko me?_. Ya ƙara ɗaga idonsa saitin bishiyar yana hango 'Yar baƙar ƙawarta Hanifa kamar ya tambayeta ina take amma tuna girmansa da ajinsa yasa ya fasa. Bai san tana da muhimmanci har haka a rayuwarsa ba. . .