Tafiya nake kaamar zan tankaɗa don sauri na nufi ƙofar shiga sashen cikin gidan, Allah ya taimake ni ba kowa a kasan, ɗakinmu na shige a hankali na mayar da kofar na rufe, zama na yi a bakin katifa, agogo na kalla sha biyu saura na dare a fili nake ta maimaita “Innalillahi wa inna alaihi raji’un, wallahi ba zan yadda da irin wannan soyayyar ba.” Kuka na saki, ashe Fatima ma ba ta yi bacci ba.
Tashi ta yi zaune ta fara tambaya ta,
“Yaya wace irin soyayya ce ba za ki yadda da ita ba? Kuka kuma?”
Rasa abin da zan faɗa mata na yi, can sai dabara ta faɗo min, don cikin kukan na ce mat,
“Wani abokin ya Habib ne yake wulaƙanta budurwasa, shi ne na ji suna waya yanzu da na kai masa shayi, shi ya sa ma na daɗe ban dawo ba.”
Ta ce,
“Ba daɗi gaskiya.”
Godiya na yi ga Allah da ya sa ba ta ɓaro jirgi na ba, cewa ta kuma yi,
“Ni ina son na fara soyayya, amma ina tunanin wa zan so? Ba na son yaudara, kuma na fuskanci samari mayaudara sun fi yawa, Salman ajinmu wani saurayi take so, amma ya yaudareta.”
“Innalillahi.” Na faɗa a zuciyata a fili kuwa cewa na yi, “Subhanallah, garin yaya ya yaudare ta.”
“Biye masa ta yi suka ringa fita yawo tare, dama ba ta da kamun kai, daga baya ya zo ya ce wai ta san maza da yawa shi ba zai aure ta ba.”
Kamar mazari haka jikina ya ɗauki rawa, kada dai Fatima ta gane abin da ya faru tsakanina da ya Habib yanzu, domin na tabbatar da zargin da nake sai na ce mata,
“Dama wa yake sakarwa saurayi jiki, ai da zarar ya gama gane wacece ke zai arce ya barki da sallallami.”
Fatima ta ce,
“Wallahi kuwa, kuma kin san abin haushin ma yaya?”
Na ce, “A’a.”
Ta ce, “Tun muna js2 suke tare, kusan 4yrs kenan sai yanzu ya zo da wannan shirmen, ba ki ga yanda ta rame ta yi baƙi ba, kullum ta zo school sai ta yi kuka. Mu ne ƴan ba ta haƙuri da rarrashi.”
Na tausayawa Salma, fatana Allah ya sa ba ta ba shi kanta ba.
“Allah ya sawaƙa, Fatima ki tsaya ki yi karatu, kada ki sake da namiji don wallahi sai ya kaiki ya baro sannan hankalinsa zai kwanta. Kin ganni nan, da ban haɗu da ya Habib ba, da wallahi har yanzu ba ni da saurayi, ina tsoron maza wallahi.”
Ta ce, “Ai dole, yanzu ko ina kika shiga dai zance maza ake yi.”
Na ce mata, “Haka ne wallahi.” Da haka muka kwanta muka yi bacci, amma dai gare ni baccin rabi da rabi ne, har mafarkin ya Habib na yi saboda tsoro.
*****
Sannu a hankali su Fatima suka fara exams ba jimawa kuma suka gama suka yi hutu, muka dawo zaman gida, islamiyya ma sun yi hutu, duk inda nake suna biye da ni, na koya musu wannan na koya musu wancen, Anty na matukar jin daɗin zamana da yaranta a tare.
Habib kuwa ya rage shige min tunda ina tare da su, idan za mu yi zance kuwa waje nake saka mana kujera don ba na son ma wani abu ya shiga tsakani na da shi, ya fuskanci hakan sai ya mayar da ni abar tsokana, wani zubin idan muna hira sai ya ce,
“Don Allah zo mu je ki rakani ɗakina.”
Ɓata fuska na yi na ce,
“Gaskiya ba za ni ba.”
Ya ce, “Me ya sa?”
Na ce masa, “Kawai.” Dariya ya yi wadda shi ya san ma’anar ta, ban damu da hakan ba, “Ki gama duk jan ajinki, kin san dai dole abin da kike ɓoyewa mallakina ne ko?”
Ni dariya ma yake ba ni wallahi, ban ce komai ba ya cigaba, “Allah ba zan saurara miki ba sai na kwashe komai, kuma nima sai na rama jan ajin da kike min.”
Dariyar dai nake yi, sai na ce,
“Kai ka sani kuma.”
Dariyar yake ya yi shi ma,
“Au haka kika ce, ai shi kenan, za ki gani.”
A zuciya na ce, “Allah ya sa na ga alheri.”
Daga wannan rana muka shirya, na rage sha masa ƙamshi, muna soyewa sosai, da zarar ya sauka daga layi zan ce ban san zancen ba.
A cikin satin ya saya min waya mai shegen kyau, ƙarshen satin kuma Sameer babban ɗan Anty Lami ya dawo daga Boarding school sun gama neco da waec, dama abin da ya sa da aka yi hutu bai dawo ba, jarabawa suka tsaya yi, kowa na gidan murna yake yi, muna ta masa fatan fitowar sakamako mai kyau, godia ya ringa yi, daga nan aka shirya masa abinci, yaci ya ƙoshi sannan ya shige ɗakinsa da ke ƙasan bene, hutawa ya yi bayan la’asar ya fito, aka yi ta hira yana ba mu labarin rayuwar boarding.
A bangare na kuwa sai santin wayar da ya Habib ya kawo min nake yi, kada ma Fatima ta ji labari, don ita ma ba ta da wayar, wai sai ta gama secondary, na ce mata,
“Ai kamar yau ne, ba ss2 kike ba yanzu?”
Ta ce, “Eh!”
Da taimakon ta da na Sameer na buɗe WhatsApp da facebook, take na soma ganin waɗanda na sani a kai, dama ina da layi na tun wata waya da ya Muttaka ya taɓa ba ni, to ta lalace, sai na adana layin, memeory kuwa ya Habib ne ya kawo min tare da wayar, sai komai ya tashi ɗas a wayar.
System ɗin Sameer Fatima ta ɗakko muka shiga loda finafinai masu kyau, ai kuwa mun sha kallo sosai.
Haka dai muka ci gaba da rayuwa, ya Muttaka yana zuwa gidan Anty Lami akai akai, takwara ma ta zo ta ga ya Habib sun sha hira shi da ita, ta dai yi min abin da ban ji dadi ba, zuwanta uku, sosai take shigewa Habib da farko ina ganin ba komai ba ne amma zuwanta na ƙarshe ya tabbatar min akwai matsala, don a gaba na take ce masa,
“Angon Leemat ga wayata ka saka min number ka ma ringa gaisawa.”
Duk dai na ji babbarakwai wai namiji da suna…, take na ji zuciyata ta fara tafasa, da kyar na danne ta, wata zuciyar tana bani shawara, “Wai bai kamata na ji kishi ba, ai takwara ce, ta yi min dukkan alheri a rayuwa.”
Duk yadda nake harararsa bai bi ta kaina ba, sai ma dariya da yake ta yi wa takwara ya sanya mata number ban ji daɗi ba, haka muka rabu duk raina ba daɗi, daren ranar haka na yi shi cur ba bacci, na yi kuka mai yawa, ga shi takwara ce ba yadda zan yi da ita.
Tun daga wannan rana sai na fara ganin canji a tare da ya Habib, lokaci zuwa lokaci idan muna hira da shi sai ya ce min twin ɗina na gaishe ni, idan na ce wace sai ya ce min,
“Sa’adiyya mana, ko kina da wata bayanta?”
Sai na ce “A’a.”
Abin ya soma damina matuƙa, to ganin watanni ya rage bikinmu ya sa na kawar musu da kai, na ce ko ma meye ai da zarar na aure shi za ta daina, ashe ban sani ba na tafka shirme.
Abin da ya fara ɗaga min hanakli shi ne, muna waya da shi da dare kawai sai ya ce min,
“My Leemat ɗan kashe zan ɗaga wata waya.”
Agogo na kalla sannan na ce, “Waye yake kiranka a wannan daren, ɗaya saura fa.”
Cewa ya yi “Twin ɗin ki ce.”
Kan bala’i, ai ban san sanda na jawo zagi na ƙunduma mata ba, “Wai me kuke nufi da ni ne ya Habib?”
Bai bani amsa ba kawai ya kashe kirana.”
Haushi, ƙunci, baƙin ciki ne suka zo min wuya, gabaɗaya yawun bakina ya ɗauke, har wata rawa jikina yake yi saboda tsabar damuwa, wane irin bala’i ne yake shirin tunkaro ni haka? Kiran number ya Habib na kuma yi amma ana sanar min waya yake, gabaɗaya na damu, layin takwara na shiga kira, abu daya ake faɗa min ita ma wayar take.
Ba ni na rintsa ba sai uku da minti ashirin, a lokacin na gaji da gwada kiran layikansu ana shaida min he’s on another call…, fushi na yi sosai na koma na kwanta, amma sam na gagara yin bacci.
Da safe da wuri ya fice daga gidan, su Nana a gidan wata cousin din Daddy Suka kwana, daga ni sai Sameer a gidan, hirar Boarding school ɗinsu yake min amma sam ba na fahimtarsa, ji na nake kamar wata mara lafiya, kirjina ya min nauyi, idanuna kuwa sun kunbura sun yi jawur, shi ma Sameer don ba mai bin kwakwaf ba ne da zai lura da yadda na canja.
Ba wanda ya kula da halin da nake ciki, wurin sallar azahar na kira ya Habib a waya amma bai ɗauka ba, daga ƙarshe ma idan na kira sai a ce min “User busy.”
Kuka kwai na fashe da shi a ɗakin, ina ganin shi ne mafita kawai, ɗaga hannu na yi sama na ce “Ya Allah idan Habib ba alheri ba ne cikin rayuwata ka gaggauta canja min shi, ya Allah ban cuci kowa ba kada ka bada iko wani mahaluƙi ya cutar da ni, Ya Allah ka fi ni sanin abin da yake sarari da ɓoye ya Allah idan har abin da nake fuskanta a yanzu kuɓuta ce zan samu daga sharri Allah ka bayyana min a yau ya Allah.”
Ina shafawa na ji na sauke wata nannuyar ajiyar zuciya, na ja numfashi da ƙarfi na sauke a hankali, take na ji raina ya yi sanyi, tashi na yi na kama abin da zai fissheni, duk wani abin buƙata ta na haɗa a jakar matafiya, haka kawai na ji ina so na koma gida a ranar, wani tunani na yi ya sai na fasa na maida komai inda yake na ajiye, fita na yi daga ɗakin, a ƙasan bene na tad da Atine na baza albasa kan yashi, sannu na yi mata na wuce falo, ganin Anty tana waya yasa na komo ɗakinmu, wayata na ɗakko na kunna data, WhatsApp na shiga, ba wani abin kirki daga groups har private chat, Facebook na koma, ashe mugun gani ne ya kaini can ɗin, group ɗin Mata masu gari na shiga, nan na iske takwara ta yi post bai fi minti ashirin da yi ba, abin post ɗin yake cewa shi ne,
“Ƴan uwa ku taya ni murna, na kusa kwace alawa a hannun kuturu.”
Sam ban fahimci inda zancen ta ya dosa ba, bin ta na yi inbox ba ta online mintuna biyar da suka wuce, ni kuma ba na son ajiye wa mutum message in dai ba online na gan shi ba, saboda ba ni da juriyar jira, sauka na yi na kashe data, ganin ana ta kiran la’asar ya sa na sakko daga katifar na shiga toilet, sosai ina cikin damuwa, alwala na yi na zo na yi sallah, bayan na idar na yi addu’a sosai, sannan na tashi, na so sanar da Anty halin da nake ciki, amma na bar shi zuwa anjima, tunda a irin ranar muke zance da ya Habib idan ya so zan roƙe shi ya faɗa min gaskiyar tsakaninsa da takwara.
Bai dawo gida ba sai tara da rabi na dare, duk da haka ban yi ƙasa a guiwa ba na tare shi, lokacin yana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinsa,
“Ya Habib!” Cikin sassanyar muryarta na kira sunan na sa.
“Na’am, ya aka yi?”
Tambayar ta min ciwo, amma na daure na ce,
“Magana nake so mu yi don Allah.”
“Umhumn ina jin ki.
Na ce, “Ko za mu ɗan zauna kan kujera.”
Haɗe rai ya yi sannan ya ce, “Ba buƙatar haka, ki faɗa min koma meye ina sauraro.”
“Dama kan batun takwara ne, na kasa gane me ke tsakaninku kai da ita, shi ne…”
Katse ni ya yi da cewa , “Shi ne me? Abin da kike zato dai shi ne tsakanina da ita, son ta nake kuma aurenta zan yi, bayan na aure ki da shekara uku, tuni muka kulla wannna alƙawarin ni da ita. Abin burgewa da na manta ban faɗa miki ba tuntuni, ta ce idan ba ki yadda ba to na fara aurenta ita ba ta da matsala da zuwanki a ta biyu, amma ki duba ki gani.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Hasbunallahu wa niimal wakil!! Lailaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin!!!” Su kaɗai nake iya furtawa.
Masu iya magana na cewa juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa, to ga tawa juma’ar da abin da ta zo min da shi, tuni idanuna suka lulluɓe da baƙin duhu, duhun da ya fi duhun dare duhu, duhu ne tafiyayye daga zuciya.