Jiri na ji yana neman kada ni, dafa bango na yi, ba na ganin abin da ke gaba na, tuƙuƙin baƙin ciki ne kawai ke taso mini, cikin murya da ba zan ce kuka nake ba ba zan ce ba kuka nake ba na ce,
“Ya Habib me na yi maka da na cancanci wannan sakamakon?” Ido rufe na yi masa wannna tambayar.
“Ni ba ki min komai ba, kawai dai abin da yake tsakaninmu ne ba zai yiwu ba, saboda na fi samun kulawar da nake buƙata a wurin ƙawarki, sannan ba zan samu nutsuwar da nake so a wurinki ba, kin ga kuwa ba zan kai kaina prison ba, idan kuma kina ganin kina so na, kuma za ki iya to ki yi ƙoƙari ki kwato ni daga inda na karkata a yanzu, idan kuwa ba za ki iya ba to kin gaza a matsayinki na ƴa mace.”
Kalamansa na yanzu sun fi dafi cutarwa a gare ni, kuka na ringa yi har da majina, wata tsanar Habib ce ta cika mini zuciya, cikin kukan na dube shi na ce,
“Wallahi kai Musa ne a fuska fir’auna a zuciya, da sannu sai Allah ya saka min yaudarar da ka yi min, da yardar Allah sai an yi maka abin da ka yi min, ita kuwa SA’ADIYYA na bar ta da Allahn da ba ya bacci, in sha Allah sai an ci amanarta kamar yadda ta ci min tawa.”
Ban jira jin ta bakinsa ba na tafi da sauri, duk kuwa da cewa ba na ganin gaba na, shigewa na yi ciki tare da banko ƙofar na haye sama, ina shiga ɗakin su Nana suna kallo a wayata, faɗawa na yi kan katifa ina kuka mai tsuma zuciya.
Kaina suka yo da tambaya,
“Yaya me ya same ki? Me aka yi miki?”
Hankali tashe suke tambaya ta don ba su taɓa gani na a haka ba, ban ba su amsa ba na tashi zaune, kukan da nake ya hana ni yin magana, na rasa wane irin raɗaɗi nake ji a kirjina, ƙwaƙwalwa ta ta toshe, ba tunanin komai a ciki.
Anty ce ta shigo ɗakin tana tambayar mu,
“Hayaniyar me nake ji haka?”
Abdul ya tashi tare da nufar inda Anty take a tsaye ya ce,
“Mama kuka ya Halima take yi.”
Anty ta ƙarasa shigowa dakin tana faɗin,
“Subhanallah! Halima me ya same ki?”
Sai sannna na ji na samu ƙarfin guiwar yin magana na ce,
“Anty ya Habib ne ya ce min wai ba ya so na, Sa’adiyya zai aura.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wace ce Sa’adiyya kuma?” Ta tambaye ni a kiɗime,
“Sa’adiyya ƙawata, ta gidan malam Shehu?”
Jimami ta shiga yi bayan ta zauna kan gado,
“Sa’adiyya kuma.”
Na gyaɗa kai na alamar “Eh!”
“Ina zuwa.” Ta faɗa, da sauri ta fice daga ɗakin, nan da nan sai ga ta tare da daddy, kan kujera ɗaya suka zauna, tambayar dai ɗaya ce daddy ya maimaita min,
“Me ya haɗa ki da Habib ?”
Kwashe komai na yi na faɗa masa tun daga lokacin da na fara zargin su har kawo wannan baƙar ranar.
Ddady ya ce, “Haba ba da gaske yake ba, sai dai ko wasa yake yi.”
Cikin fusata Anty ta ce, “Ni abin da nake son sani shi ne, meye matsayin ƴata a yanzu?”
Daddy ya ce “Wannan duk shirme ne, aure kuma babu fashi tsakaninsa da Halima, domin shi ya ce yana son ta, ba kuma wata hujja da ya isa ya kawo mana mu karɓa.”
Juyowa ya yi gare ni yace,
“Ki kwantar da hankalinki kin ji Halima, ba abin da zai raba ku da Habib in dai na isa da shi.”
“To.”
Na ce masa still Ina kuka, sai da suka lallashe ni sosai sannan suka fita, sai da safe muka yi musu don ba wanda ya yi bacci a cikinmu, Sameer kuwa bai san ma wainar da ake toyawa ba a gidan, shi dai bar shi da kallo da kuma chatting, dama shi ba mai yawan magana ba ne, da yawan halayensa irin na Anty ne.
Ni kuwa kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, dama tun kafin su Anty su fice daga ɗakin na fara jin sanyi, bargo na jawo na rufe jikina ruf da shi har kaina, kuka nake son yi amma hawaye ya ƙi fitowa, yadda na ga rana haka na ga dare, babu bacci ko misƙala zarratin a ido na.
Duk yadda muka ɗauki matsala ta da ya Habib abin ya huce haka, don a washe garin ranar kowa da wuri ya tashi, ƙarfe tara na safe muka sakko kasa kasancewa duk ba mu tashi da daɗin rai ba, wanka na yi, na shirya ba kamar yadda na saba, hijab na saka zumbulele har ƙasa, ba ni da nutsuwa sai dai ban fita hayyacina kamar daren jiya ba, Lipton kawia na iya sha, wanda a takaice ma ba na iya gane ɗanɗanonsa, ina cikin sha ne daddy ya turo Abdul ya ce ya kirawo ni, na san kwanan zancen, kuma dama so nake yi a yi ta ta ƙare.
Cewa na yi “Je ka ce gani nan.”
Cikin Abdul ya koma da gudu, ni kuma na ajiye kofin kan dirowar kicin na ce da Atine “Bari na je ana kira na.”
Ta ce, “To yar kirki.”
Ita kanta ta lura da yanayin da nake ciki, saboda tun fitowa ta take kallo na, daga baya kuma ta tambaye ni, “Hali dubu yau lafiyarki kuwa?” Shiru na yi mata a lokacin saboda da zarar na buɗe baki zan yi magana, to kuka ne yake taho min, ganin na yi shiru sai ba ta matsa min ba.
Duk wanda ya Sanni a tsakanin jiya da yau zai iya gane ramar da na yi, ga uban kumburin da idanuwana suka yi, cikin farin idanun ya yi ja jawur.
Ina shiga na samu wuri na zauna kan carpet, kiran Habib Daddy ya tura a yi, amma sai ya ce a ce bacci yake.
“Bacci yake?” Daddy ya maimaita maganar, tashi ya yi da kansa ya tafi ɗakin Habib, kusan minti goma sannan ya dawo, ko da ga yanayin da fuskarsa take ciki ya isa ya tabbatar maka da cewa ba su ƙare da daɗin rai ba, shigowa cikin parlon ya yi, ya dube ni ya ce,
“Abin da nake so da ke Halima, ki yi haƙuri, ki ƙara hakuri, ki kuma cire Habib daga zuciyarki, amma ba ke ya yi wa wannna rashin mutuncin ba ni ya yi wa, in sha Allah Allah zai saka miki.”
Daddy na kaiwa nan ya miƙe zai fita, Anty ma ta miƙe ta ce,
“Dady ina son mayar da Halima gida.”
“Ba yanzu ba.”
Ya faɗa a gajarce, ficewa ya yi daga parlon.
Na so tafiya a ranar, amma Anty ta ce na zauna har daddy ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Yini na yi kamar wata mara lafiya, zuciyata cunkushe da baƙin ciki, lokaci zuwa lokaci sai na ce, “Mutum!”
Anty da ke gefena sai ta ce “Halinsa sai Allah.”
Ba daɗi haka muka kai dare, Atine kanta ta girgiza da jin rashin arziƙin da Habib ya yi, haƙuri dai ita ma ta ba ni, har labarin jikarta Binta ta ba ni, ita ma haka saurayi ya yi mata, bayan an kawo kuɗi da sa rana, sai ya koma wurin ƙawar Binta, ƙawar tata ya aura, yanzu haka ma yaransu biyu, ita kuma Binta ta samu wani, saura wata biyu ma bikinta.
Na jinjina lamarin Binta duk da ban santa ba, amma lamarin ya ban tsoro, koda yake nima ai ga shi ya faru a kaina.
Sai daf da wurin biyar na yamma Daddy ya dawo gidan, Anty ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta tashi ta bi shi ɗakinsa, abinci ta dawo ta ɗaukar masa, bayan sun kammala suka dawo parlo, kirana dai ya sa aka kuma yi, bayan na shiga na zauna, gaishe da shi na yi, ya amsa ba kuzari.
“Halima ki hakura da Habib.”
Wata irin faɗuwar gaba na ji, kukan da nake dannewa ya fito fili, ba wanda ya hana ni, sai da na yi mai isa ta. Anty kuwa idan ranta ya yi dubu ya gama ɓaci, lallashi na ta shiga yi har na yi shiru.
“Daddy ina so Halima ta koma gida.” Anty ta yi maganar rai ɓace.
Ɗaga idanunsa da suka yi ja ya yi ya fara magana da ɗaga murya,
“Na faɗa miki ba yanzu ba! Wai so kike ki maida ni ƙaramin mutum ne? Na yi wa mahaifin yarinya alƙawarin aurar da ita, akan me zan canja? Akan me zan mayar da ita gida yanzu? Halima ta dawo nan gidan da zama gabaɗaya.”
Shiru ya yi, can kuma ya cigaba da magana, “Shi Habib shi ne zai fice ya bar min gida, tunda ba shi ya gina mini ba, ba kuma da kuɗinsa muka haɗa na siya ba.”
Anty ta ce, “Ba za a yi haka ba, ita dai ya kamata ta tafi, bana so a zo ana zarginmu da wani mugun abin kuma.”
Katse ta daddy ya kuma yi a fusace, tare da cewa,
“Kin san cin zarafin da mahaifiyarsa ta yi min akan wannan maganar? Ki kyale ni da batun tafiyar yarinyar nan Sa’adatu, bar ni da maganganun nan haka, ya isa!”
Anty ba ta ƙara cewa komai ba, ta san idan daddy ya yi fushi to ba ya buƙatar komai, ya fi so a ba shi sarari har ya huce don kansa.
“Shi da ya yi mugun abin ba’a zarge shi ba sai ita yarinya da ya cuta? Ki daina kawo mini maganganun mutune marasa tushe da makama, duk abin da za’a ce a ce, ni ba na gudun abin faɗa, kowa yana da aibu, sai dai na wani ya fi na wani.”
Dubata yi cikin tausasa murya ya ce,
“Halima nan za ki ci gaba da zama kin ji, mun gama magana ma da mahaifinki, makaranta za ki fara ke da Sameer, in sha Allah sai na cikawa mahaifinki alƙawarin da na ɗauka, na aurar da ke, sannan za ki bar gidan nan.” Yana kaiwa nan ya tashi ya fice daga parlon.
A wannna lokacin ba na iya fahimtar komai, so da haushin Habib sun hana ƙwaƙwalwa ta yin tunani akan komai, da Habib yasan irin matsayinsa a zuciyata da bai yaudare ni ba, da ace takwara ta san irin son da nake wa Habib da ba ta shiga tsakanina da shi ba, amma ba komai na bar su da Allah wanda ba ya bacci, da sannu za su ga abin da suka yi.
Wani mugun son ya Habib ne ya shiga taso min, “Yanzu shi kenan na rasa ya Habib?”
Kuka na yi shi kamar ba zan daina ba, inda Allah ya taimake ni ma wani abu bai taba shiga tsakanina da ya Habib ba, tun ranar da ya yi rashin lafiya ne, kuma shi ma na fuskanci ciwon ƙarya ne don na yi abin yake so ne ya sa ya ɓullo da zancen ciwon, “Alhamdulillah.”
Na yi ta nanata wa, take na soma sauke ajiyar zuciya, wata nutsuwa ce ta zo min.
Na sha nasiha wurin Anty, da taimakon shawarwarinta na samu na sassauta damuwata, gefe guda kuma ina ta addu’a.
Cikin sati na biyu da faruwar lamarin na warware sosai, amma da ɗan sauran damuwa, wayata da ke a kashe tun lokacin da muka rabu da ya Habib na ɗakko, don na ma mance da ita, kunna ta na yi, ganin hoton da ke kan screen ɗin ya sa na yi saurin kifata kan hannun kujerar da nake kai a zaune, hoton ya Habib ne da ya ɗauka ana saura sati ɗaya mu fara rikicin, sanye yake da ƙananan kaya, farar riga ce mai ratsin ash color sai Blue black ɗin wando, ya yi kyau sosai, hoton ya shiga raina, shi ya saka min shi kan screen ɗin wayar.
Hawaye ne ya shiga silalowa ta saman kumatu na, son Habib ya zame min wani miki da ba shi da maganin da zai iya warkar da shi, ban taɓa son wani ba idan ba shi ba, Habib ya yi wa jini da tsokar jikina ginin da ban san ranar rushewar sa ba.
Ba na taɓa manta wasu ranakunmu, lokacin muna kan ganiyar soyayya, ranar asabar ce da safe, wankin mota yake yi da kansa, sannu a hankali na ƙara sa inda yake, sanye nake da riga da wando na Pakistan milk color, sun min kyau sosai, tsayawa ya yi yana ƙare min kallo, juyawa na yi ya ce,
“Za ki kashe ni da kyawunki My Leemat.”
Dariya na yi haɗe da kashe masa ido ɗaya, ƙarasawa na yi daf da shi na ce,
“Sai ma mun yi aure.”
Dariyar shi ma yake ya ce, “Allah ko?”
Na gyaɗa masa kai, ce wa ya yi, “Mu je ɗakina ki ɗan sammin mana tun yanzu.”
Haɗe rai na yi na ce masa, “Allah zan daina yi maka kwalliya indai haka za ka ringa ce mini.”
Dariya ya yi yana cewa, “Ke ƴar kauye ce wallahi, kin san kuwa me zamani yake ciki yanzu?”
Na ce masa, “Ba ruwana da zamani.”
A hankali na juya wayar sai sannan na dawo cikin hankalina.
Ajiyar zuciya na sauke, take kuma wani tunanin ya faɗo mini, shi kuma ranar da takwara ta fara zuwa ganin ya Habib, tun shigowarta gidan ta hange shi zaune kan farar kujera, da yake ya san da zuwanta da kansa ya gane ta, da fara’a ta ƙaraso in da yake daidai lokacin ni kuma na fito hannuna ɗauke da plate da na yanka masa lemo da abarba a kai, yana matuƙar son kayan fruit, dariya na saki ina cewa, “Barka da zuwa, kin sha hanya.”
Dariya kawai ta yi muka samu wuri muka zauna a tare.
“Ina yini.” Ya Habib ya kalle ta, kallo yake mata irin na ƴan duniya, ya ce “Lafiya lau takwararmu, fatan kina lafiya.”
Cewa ta yi “Lafiya lau.”
Hira muka shiga yi, ganin tana ɗararewa ya sa ce mata, “Malama ki saki jiki don Allah, mijin naki ba ruwansa.”
Habib ya ce, “Faɗa mata dai.”
Sai sannan ta saki jiki muka yi ta hira, muna nan zaune Anty ta dawo, dama ita za ta ɗakko su Fatima daga makaranta.
Shigowa suka yi muka yi musu sannu da zuwa bayan sun fito daga mota, har ciki muka raka su, takwara ta tsuguna har ƙasa ta gaishe da Anty, na ji daɗin haka.
Ashe ban sani ba wannan rana ita ce silar rushewar katangar da ta ginu tsakanina da ya Habib, wannan rana ita ce masomin komai.
Ban aune ba sai jin shigowar su Nana na yi sun dawo daga makaranta, mamaki na shiga yi, na sani lokacin da na zauna kan kujerar da tunanin Habib ya ɗauke ni karfe sha daya na safe da minti arba’in, idan haka ne kuwa kenan na shafe awannin a zaune ban sani ba, don a lokacin karfe biyu na rana ta wuce har da mintuna bakwai.
Tashi na yi na shige toilet don ba na so su ganni cikin damuwa saboda Anty ta hana ni yawan tunani, sannan kuma da zarar yaran sun ganni cikin damuwa take su ma tasu walwalar take ɗauke wa.
Alwala na yi na fito, ina haɗa ido da Abdul uban yan surutu ya ce, “Ya Halima kuka kika yi ko?” Matsawa na yi jikin dirowar kayana na ce masa, “A’a. Ya makaranta.”
Mayar da hankali ya yi ga ƙarasa cire Uniform ɗinsa yana cewa “Kuka kika yi, ga idanunki nan sun yi ja.”
Ban kuma cewa da shi komai ba, illa ciro doguwar riga ta shadda light blue na saka, ɗan ƙaramin mayafi na ɗora a kai baƙi na fice daga ɗakin, a parlo na tarar su Fatima sun baje suna cin abinci, Anty da ke kan kujera kusa da bakin ƙofa ta ce, “Har kin tashi kenan?”
Na ji daɗi da ta yi zaton bacci nake yi, sai dai Abdul ya tona min asiri da cewa “Mama ba ta daina kuka ba, yanzu na ga idanunta sun yi ja.”
Ƴar dariya na ƙaƙalo duk don na kubutar da kaina daga tonon asirin da Abdul yake shirin yi min na ce, “Anty ba fa kuka na yi ba, bacci na tashi, sai kuma na ji kaina yana ciwo.”
“Ayya Allah ya sawaƙa, amma dai ki daina yawan tunanin nan, don ba ya da kyau ga lafiya.”
Na ce “To na daina Anty.”
Wuri na samu gefen Fatima na zauna ina kallonsu na ce, “Cin abinci ba ku jira ni ba?”
Dariya suka yi Fatima ta ce, “Yau wace rana kin nemi abinci da kanki.”
Dariyar nima nake yi na ce, “Sai ki zubo min ai.”
“An gama.” Ta ce, ta fice daga parlon.
Kafin ta dawo na ce wa Anty, “Dama daddy da ya Habib ba mamansu daya ba?”
Dan murmushi Anty ta yi, hankalinta na kan wayarta ta ce, “Uba suka haɗa.” Bayan ta ajiye wayar hannunta ta ci gaba da cewa, “Kowa zato yake yi uwa daya uba ɗaya suke, saboda shaƙuwar da ke tsakaninsu, iya zamana da Daddy ban taɓa ganin sun yi saɓani da Habib ba sai wannan lokacin, ina matuƙar mamaki yadda aka yi Habib ya aikata wannan wulaƙancin, ke in takaita miki Habib ba matar yayansa ya ɗauke ni ba, kallon uwa yake yi mini.”
Shigowar Fatima ɗakin ya sa ta ɗan dakata da maganar, amma ya za ta yi, dole ta faɗi gaskiya ai. Ci gaba ta yi da maganar,
“Sa’adiyya ta matuƙar ba ni mamaki da ta iya janye hankalin Habib daga kanmu baki ɗaya, har yau zuciyata ta ki yadda haka kawai abin nan ya faru, kawai dai na zubawa sarautar Allah ido mu ga abin da hali zai yi, na tabbata wata rana sai Habib ya yi nadamar abin da ya aikata.”
Tana kaiwa nan ta tashi ta fita.
Daga wannan rana na ƙudurce cire yaya Habib daga cikin zuciyata, na kuma sa a raina na daina kuka akan abin nan, na shirya fuskantar rayuwata ta gaba, duk da dai kasan zuciyata yana son kunyata ni saboda haka na mike na hau sama, ɗakinmu na shige a lokacin Fatima ta fito daga wanka, na ce mata ta ban littafi da biro.
Miƙa min ta yi na zauna kan darduma na fara rubutu, a wannan rana na tsara duk wasu sabbin abubuwa da nake son farawa Wanda a da baya bn yi su ba.
Na farko shine, goge duk wani sako da na samu daga ya Habib, duk wasu text message ya taba tura min sai da na goge, daga ƙarshe na goge number sa gabaɗaya daga wayar.
Na sauke kayana kaf na sake gyarawa na mayar, sannan nafara gyara ɗakin na share shi tas don sai da na kwashe komai sannan share na mayar.
Kan magriba na gama gyara saman baki daya, na sakko na gyara kasan na saka turaren wuta, Anty ta fito daga ɗakin daddy fuskarta cike da fara’a ta ce, “Lallai, na ji daɗin wannna canjin da na gani a tare da ke, Allah ya miki albarka.”
Su Fatima ta je ta koro daga ɗakin Sameer tana ta motar Ba sa aiki sai son kallo, ita da take shirin exam ba ta karatu.
Tare suka fito har Abdul, suka zo muka dora jellop din shinkafa tare, Atine ma murnar canjin da ta gani a tare da ni take yi.
*****
Haka kwanaki suka cigaba da tafiya, har zuwa ranar da aka saka mana za mu yi jamb, alhamdulillah mun yi, bayan kwanaki sakamako ya fito duk mun samu makin da ake buƙata don haka Daddy ya fara shirin nema mana makaranta, gefe guda kuma Anty na ta mana sayayyar abubuwan buƙata, kama daga sutura sawa zuwa mayafi da hijabai da takalma duk wani tarkace dai da sabon dalibn jami’a yake bukata Anty ta tanadar min. Daga nan ta min nasihohi sosai, daddy ma ya yi mana akan mu kula da karantunmu, shi ne abin da ya kaimu makaranta ba wasa ba, kada mu yadda ya kama mu da wani laifi. Cikin nasara kuwa muka samu admission a BUK, ni na samu B.Sc Health education, shi kuma Sameer B.Sc Geography. Haka muka gama registration komai ya kammalu, a daren ranar na je gida, da yaya Muttaƙa na fara haɗuwa, ya yi min murna tare da fatan alheri, Abba kam har kuɗi ya ban na karɓa ina ta godiya.
Mama ta karɓe ni, da zan tafi ta yi min nasiha, abin da ba ta taɓa yi min ba a rayuwa, na ji daɗi na kuma gode mata. Tuni su Ummee suka fara lecture a School of hygiene, tana karantar Environmental Health Assistance.
Nan da nan cikin ikon Allah sai ga mu a makaranta, sai na ji sanyi ya ratsa ni, hamdala na yi lokacin da muka kutsa kai ciki, sosai na yi farin ciki sai dai duk wannan abin alherin ba mahaifiyata, ba don ba ta raye ba sai don wani dalili na Abba.
Education aka sauke ni su kuma suka wuce da Sameer Faculty of Earth and Environmental Science.
Dayake tuni na san department dina sai na wuce theater da za mu fara lacture a ciki, ba mutane sosai da yake ranar farko ce, na shiga na zauna daga gaba, malamin bai shigo ba don haka da time ya cika muka fito kowa ya kama gabansa, sai kuma 2-4pm za mu koma.
Rest Area na nufa dama duk Aunty ta gama yi min bayanin komai kasancewarta lecturer a cikin makarantar. Nan na zauna ba wanda na sani don haka na ciro wayata cikin jaka na fara danne-danne WhatsApp na shiga a cikin group ɗin gida na ga an sanar da rasuwa, shiga na yi da sauri don na ga waye ya rasu sai na ga ashe ya Usman ne ɗan gidan Aunty Indo, “Innalillahi.” Na faɗa ashe ciwon nasa ba na tashi ba ne, Allah ya jikansa ya sa ya huta.
Kiran Aunty na yi, ta kashe ta kirani na ɗaga da sallama ta ce, “Yanzu nake shirin kiran ki, ki fito bakin faculty mu wuce tare.”Na ce, “To Anty.”