Skip to content
Part 12 of 12 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Fitowa na yi muka wuce, a hanya zuciyata ke ta wasi-wasi tare da zulumin Allah dai ya sa mu wanye lafiya, ko da yake ai rasuwa ce ba lallai ne ta min abin da ta saba yi ba.

Nan da nan muka isa Nassarawa, a Sokoto Road suke da zama, muka isa bakin wangamemen gate din su da yake kullum a kulle, saboda yawan tafiye-tafiye da suke yi, yau kam an buɗe shi saboda rasuwar mutumin kirki, “Allah ya jikan ya Usman ya sa ya huta.” Na faɗa daidai lokacin da Anty Lami ta yi parking motar muka fito, gidan cike yake da mutane, to ɗan babban mutum ya mutu ai dole a cika, ga mulki ga sarauta.

Ciki muka shiga, Anty na ta sharɓar hawaye, ni kam fuska ta ƙamas, ba wai don ban damu da mutuwar ba a’a, tun bayan rabuwata da ya Habib sai nake jin zuciyata ta yi ƙarfi, ba komai nake wa kuka ba, cikin ma cike yake da mutane, muka shige can sashen Anty Indo muka zauna, ashe tuni su Fatima suna gidan, da daddy ya ɗakko s daga school nan ya kawo su.

Tuni aka yi jana’iza aka kaishi makwancin sa, gida ya rage sai yan makoki da masu cin abinci da masu gulma kowa na bajekolin sa.

Bayan la’asar na cewa Anty yunwa nake ji ta ce min, “Kin wa yaya gaisuwa kuwa?”

Na yi shiru, ta ce “Tashi da Allah can mara kunya ki je ki mata gaisuwa, mutum abu ba ya wucewa a wurinsa ne.”

Ni kadai nake jin faɗan da take min don ƙasa-ƙasa take magana, haka ban so ba na miƙe na fice daga ɗakin, duk na duba ban ganta ba na tambayi masu aikin gidan suka ce tana ɓangaren Fu’ad rasss! Gabana ya faɗi, haka na nufi sashen jikina na a sanyaye, wuri ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba, take komai da ya faru ya soma dawo min kamar yanzu yake faruwa, ko a lahira ba na fatan sake haɗuwa da mutumin nan, a duniya ban ga wanda ya takura min tare da nuna min tsana ba irin yaya Fu’ad, ba ya so na, ba ya son ganina cikin kwanciyar hankali, kyama ta ma yake kamar ba jininsa ba.

Kamar ƙwai ya fashe min a ciki na tura ƙofar tare da yin sallama, katon parlo ne na alfarma da ya ƙawatu da kayan ado ya gaji da haɗuwa, ba shirgi sosai, daga kujeru sai labulaye komai ash color ne hatta painti ruwan toka ne mai haske, sai Tv da sauran kayan kallo baƙaƙe.

Suna can tsakiyar parlon a zaune, shi yana kan kujera ita kuma tana ƙasa, a raina na ce, “Ba girmamawa.”

Da alamu magana suke mai mahimmanci don ba su ji ma shigowata ba, na ƙarasa na yi sallama sannan Maman ta ɗago ta kalle ni, na tsuguna gabanta na gaishe ta, na mata gaisuwa, sanyin Ac na ratsa ko ina, shi kuwa gogan tunda ya ji an yi sallama bai ko waiwayi inda nake ba kawai dai ya kau da kai gefe guda, ya tara gemu da kasimba sosai ya zama cikakken mutum, kyawunsa yana nan sai ma karuwa da ya yi, ya ɗan yi kauri ba kamar da ba da yake siriri, idanuwansa sanye cikin farin glass, azuciya na ce, “Likita bokan turai.” Cikin mintinan da ba su fi biyu ba na gama nazartarsa, har yanzu izgilancin nan da girman kai suna nan, dama boko ya hadu da kuɗi, ga mulki ai sai ta Allah kuma.

Na miƙe zan fita Anty ta ce, “Ban gane ki ba fa.”

Da mamaki na juya ina kallonta, sai na ce, “Halimatu ce, yar gidan Jibril, ƙaninki.”

Baki sake take kallo na, ko ba a faɗa ba na ji rakiyar idanun ya Fu’ad a baya na don da na juyo zan saka takalma na tare na ga suna kallo na shi da uwarsa har na fice ba wanda ya kuma magana a cikin su.

Ina komawa sashen Anty Indo na tad da Anty ta shiga toilet a lokacin mutane sun ragu a ɗakin, tana fitowa nima na shiga, bayan mun idar da Sallah Anty Indo ta shigo ɗakin, kafin ta yi magana kuma su Abban mu suka shigo shi da ya Muttaƙa da uncle Abubakar da Abba Ibrahim, da Abba Malam, da uncle Kamal, duk suka zauna aka sake gaisuwa Anty Lami na gefe, Anty Indo na tsakiya, ta ga kowa ya zo, sannan kowa ba irinta ba ne, da alamu ma kunya take ji sai faman cewa take, “Na gode, Allah saka da alheri ya kara zumunci.”

Uncle Abubakar ne kaɗai ya ce, “Amin.”

Suka ce za su tafi, dama saboda Usman ne ya rasu yasa ma aka zo mata haka, ita da ba ruwanta da dangi, gani take don Allah ya ba su dukiya sai ta taka kowa son ranta, ba haka mutane suke ba, idan mutum yana da zuciya ba ya jure wulaƙanci, na gode Allah da ya kasance Abba na yake da zuciya, ba ya son raini, sam ba ya shiga sabgar kowa bare kuma Anty Indo da ta zazzaga masa ruwan rashin mutunci a rayuwa, ita ce sanadiyyar tarwatsewar gidansa a farko, ita ce sanadiyyar da ya sa mahaifiyarsa ta fita a harkarsa har sai da ta kusa mutuwa sannan suka samu daidaito don haka ba ya jin za ta sake samun gurbin yan uwantaka a wurinsa don ya yi fushi da ita sosai, yanzu ma saboda mutuwa ce, kuma Uncle ne ya je har gida suka taho tare, amma ban da haka da ba zai zo ba.

Suka fita na bi su a baya, Uncle yana ta tambaya ta makaranta na ce masa ai yau na fara zuwa, ya ce, “Allah ya taimaka, kamar yau za ku gama ai.”

Na ce, “Amin uncle, Ina su Najma?”

Ya ce, “Suna Abuja, sai gobe za su zo.”

Na ji daɗi, don ina son ya’yansa, su ma suna so na. ƴaƴan sa biyu, Hannatu ita ce babba, ana kiranta Najma sai Aliyu suna kiransa Nabil, suna da kirki, mummynsu Amina ta so Abba ya ba su ni ya ƙi, ina son matar ta yi a rayuwa.

Da dare muka tafi gida, ban da ya Fu’ad ba wanda na gani a ya’yan Anty Indo, sai da muka je gida nake tambayar Anty ina suke ta ce, ai matan biyu suna Canada, sai Ibrahim yana India shi ma medics ne, Huzaifa kuma yana Italy, shi daman dan kwallo ne tun yana yaro, ga shi burinsa ya cika.

Wanka na yi bayan mun ci abinci na haye sama, yau garin an dan fara zafi kaɗan, na haye gado ina tunanin rayuwa, daga wannan sai wancen a haka har bawa ya wayi gari babu shi. “Allah sa mu cika da imani.”

*****
Cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala level 1 muka yi hutu, na sha karatu don haka sai da na yi ramuwar bacci sosai, bayan kwana biyu na tsefe kaina, aka min kalba ƙanana, muka je kunshi, baƙi aka min ya yi kyau sosai, abin ka da farar fata kowa ya gani sai ya yabi ƙunshin.

A wannan lokacin gabadaya na canja, na ƙara girma da wayewar rayuwa, sam na daina jan abubuwa cikin raina bare su dame ni, ban ƙara yin ƙawa ba, sai wata yarinya Yasmin da ta nace min, ita ma don ta faɗan garinsu ne ya sa nake ɗan sauraren ta, kuma yarinyar tana da wauta sosai nake ba ta shawara idan na ga za ta yi kuskure.

Ƴar Dambatta ce, ta zo karatu nan shi ne take zaune a hostel, ita kadai nake kulawa, sai wani ɗan ajinmu shi ma Yusuf sunan sa, shi ma dai shi ne yake shige min har muka saba, yana kulawa da al’amura na, shi ya sa ba zan manta da shi ba a rayuwa.

Ranar wata Laraba muna zaune a farfajiyar gidan Anty, dukkan mu, Fatima na ta karatu don sun fara waec har sun yi guda biyu ma, a gobe Alhamis za su yi biology, ni kuma Ina gefenta ina manicure, Anty na zaune kan farar kujera tana shigar da wasu rubuce rubuce cikin system, Nana na assignment a gefe muka ji horn a kofar gida, megadi Ya buɗe gate, motar gidan Ambassador Rayyan ce ta shigo, Anty ta miƙe baki washe tana dariya, yaran ma suka mike suna ta murna ganin Anty Indo, ni kam baya na ja na tsaya, ni ba fushi ba ni ba murna ba, haka kawai idan na ga matar sai na ji duk na takura, walwala ta ta ɗauke, sai da suka gama gaisawa na matsa kusa da ita na gaishe ta, ta amsa ba yabo ba fallasa, sannan suka shige ciki, duk zato na direba ne ya kawo ta ashe ba haka ba ne, ɗan gaban goshinta ne zaune a driver seat, ni dai na ci gaba da abin da nake yi, sai bayan sun shiga ya fito ya ɗan jingina da motar, dagowar da zan yi idanunmu suka sarƙe da na juna, tuni na ji wani shock ba shiri na haɗa komai nawa na bi su ciki, a kitchen na tsaya, ya yi kyau kananun kaya ya saka sun fito da asalin kyawunsa, idanunsa sanye da farin glass medical ne amma, a raina na ce, “Makahon banza.”

Ban san me suka tattauna ba suka fito tare da Anty, na dai ji Anty Indon na cewa, “Ki dai bi a hankali, amma sam wannan ba mafita ba ce.”

Ni dai na haye sama abina, yadda ba ta ja na a jiki haka ba na cusa kai inda take, ita da bakinta ta faɗa a gabana ba ta so na ba ta don mahaifiyata, ni kuwa ta ya zan so ta, ai ba zai yiwu ba.

*****

Mun koma hutu, su Fatima sun gama ssce dinsu, Nana an zama ƴan mata, tana ss1 Abdul js1 sosai yaran sun girma, ni kaina na ƙara girma, ga wata kiba da nake yi ba mai muni ba ce, illa ma sake fitowa da kyawun halitta ta da take yi, kowa ya ganni sai ya tanka, ba shiri na koma saka hijab da nikaf, muna daf da fara exams aka tafi strike na sati biyu, na roki Anty ta bar ni na je gida na kwana biyu, ai kuwa ta bar ni, washegari na haɗa kaya sai gida, ina ta nishaɗi, ko ba komai dai yau zan kwana gidan Abba.

Murna gun su Ummee don ban faɗa musu zan zo ba sai kawai ganina suka yi, ai kuwa kamar sa karya ni don murna, mama dai sai dariya take mana, a ɗakinta na sauka, kan gadon ta na kwana, Abba ya ji daɗi, da safe ta bayar aka sayo min wainar shinkafa mai daɗi da taushi, ai ina tashi na yi brushing na dawo daki na fara ci, na ji daɗin ta sosai, ina son masa kamar me.

Ya Muttaƙa ya ji daɗin zuwa na, kowa ya ganmu a dakin Mama sai ya yi murna, a ranar Anty Mariya ta zo da su Faruk, kannenmu ne su biyu, ‘ya’yan Abba ne, sai dai su tunda suka rabu da Abba Anty Mariya ta tafi da su, don ta ce ba za ta bar masa ƴaƴanta ba, don ta san wuyar da na sha a baya, ta ma yi mamaki da ta ga mama na nan nan da ni a yanzu.

<< Halimatus Sa’adiya 9

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.