Skip to content
Part 6 of 12 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Bitar Al-ƙur’ani muka yi bayan mun idar da sallar asba, muka koma bacci, sai bakwai na safe na farka.

“Ya Salam!” Na faɗa bayan na duba agogon bangon ɗakin, na tashi zaune, hulata na saka, na miƙe tsaye tare da kiran sunan Fatima, Juyi ta yi ta ce,

“Na’am Yaya.”

Na ce mata “Ku tashi mun makara yau har bakwai ta yi.” Ina maganar ina buɗe window, hazo ne ma ya lulluɓe sararin samaniya.

Na juya kan Nana da ke ta juyi kan katifa na miƙar da ita tsaye ina faɗin,

“A tashi haka Nanaty mun makara.”

Ta ce,

“Yaya bacci bai isheni ba.”

Na yi dariya na ce,

“Ai ke da isasshen bacci sai kin gama karatu kin yi aure.”

Dariya Fatima ta yi, Nana kuwa cikin magagin bacci ta ce,

“Aure kuma yaya?”

Na ce mata,

“Eh!” Bayan ta tashi daga kan katifar, sannan na ce,

“Ku je ku yi wanka.”

Tuni Fatima ta shiga banɗaki, Nana da Abdul ficewa suka yi daga ɗakin, baɗakin falo Nana ta shiga wannan ƙa’ida ne kullum ta tashi a bacci sai ta yi Tutu.

Ni na yi wa Abdul wanka, na shirya ya shi, jakarsa ya miƙo mini ya ce,

“Yaya tuna min ƙarin da aka yi mana last week.”

Karɓa na yi na ce masa wace sura kuke?”

Ya ce, “Suratul mursalat muke, aya ta ashirin da ɗaya.”

Buɗe wa na yi na shiga biya masa, abin mamaki ya iya, makarijil huruf da tartili kamar wani ɗan larabawa, abin ya burge ni sosai.

A gaggauce suka fice ranar ko breakfast ba su yi ba, na dai saka musu abu cikin haka wanda za su ci, Fatima na ta tsokanar Nana wai acici ba ta ci abinci ba yau za su tafi, turo baki Nana ta yi ta ce, “Yaya kin ga ya Fatima ko?”

Dariya na yi na ce “Yi haƙuri ku tafi kin ji Nanaty kada ki jawo ku makara.”

Na juya ga Fatima na ce, “Don Allah ki daina tsokanar wannan a lallaɓa ɗin.” Suka fice, suna ta yi mini bye bye.

Gidan muka gyara ni da Atine, daga nan muka karya sannan muka fara haɗa kayan girki.

Da rana fried rice muka yi da farfesun kazar da ta yi ragowa, sai salad mai macaroni, haɗin ya ba ni sha’awa, na koye shi ne a catering school da na je, ban samu damar haɗawa ba sai yau a gidan Anty.

Shabiyu da mintuna kaɗan muka sauke tukunya, Atine ta ce,

“Gaskiya Hali dubu kin iya abinci, wai don Allah a ina kika koyi girki ne haka?”

Dariya na yi na ce,

“Zan ba ki labari, amma ya zu mu shirya kayan nan a dinning ba naso su Aunty Lami su iso ba mu hattama ba.”

Cewa Atine ta yi,

“Wannan gaskiya ne, ke dai mijinki ya huta wallahi.”

Ina ta dariya muka kwashe komai, sannan Atine ta gyara wurin, wanka na je na yi, na shirya cikin doguwar riga ta, ɗinkin straight grown, da yake atamfar na da duhun kala sai ta fito min da kyau da kuma hasken fata ta, sosai na ringa kallon kaina a mudubi, ƙasa zuciyata kam yana ta saƙa min halin da Habib yake ciki, ganin tunanin zai kashe min guiwa sai na tashi na sauka ƙasan bene.

Zaune na tadda Atine a ɗaki, tana shafa man kitso Apple a kanta, farar kujerar robar da na taho da ita a ɗakin na sa na zauna daga gefenta na ce,

“Wanke kai kika yi kenan”

Ta ce, “Eh wallahi, kitso nake so na je, amma sai Hajiya ta dawo.”

Cewa na yi da ita,

“Laaa! Ai na iya kitso, kawo na yi miki.”

Duba na ta yi da mamaki kwance saman fuskarta tace, “Alhamdulillah!”

Kibiya da comb ta miƙo min tana cewa,

“Allah ya sa ba ki da zafin hannu.” Dariya kawai na yi na ce,

“Idan na miki za ki ji ai.”

Kitso na shiga yi mata har guda shida, sosai kitso ya yi kyau, sai dai furfura ta yi yawa a kan nata, ina gamawa ta ce,

“Wai! Wallahi kamar ba ki taɓa kan ba, Allah ya taimake ni, aga yanzu idan da hali ke za ki ringa yi mini kitso.”

Ni dai murmushi kawai na yi tare da faɗin, “Idan na koma gida kuma fa.” Sai sannan ta ce,

“Au Wai ba kin zo mana nan kenan ba sai aure ya zo ki tafi.”

Dariya na shiga yi, a raina ina ƙiyasta ina ma nice Aunty Maryam matar Ya Habib, wataƙila da nan gidan ya zamar mini wurin zuwa na koyaushe.

A fili kuwa cewa na yi,

“Ciwo ne ya kawo ni Baba Atine, kuma tunda na warke gida zan koma.”

Atine ba ta ji daɗi ba, amma ba yadda za ta yi da gaskiyar da na faɗa mata, domin na fidda mu daga yanayi marar daɗin da na ambato sai na ce mata,

“Amma zan ringa zuwa ina kwanaki ai.”

Sai sannan Atine ta ce,

“Yauwa ko da na ji.”

Ƙarfe uku saura muka ji shigowar motar dady da hanzari na leƙa ta window, kan idona suka ƙarasa shigowa gidan, cikin murna na ce,

“Atine wallahi su ne.”

Sakin labulen na yi na ɗauki mayafi na na yafa, na zura takalmana flat shoe da Aunty ta saya min gurin wata abokiyar aikinta, sun yi kyau kuma sun shiga da atamfar jikina.

Da gudu na fito parking space ɗin, sai dai na cika da mamaki ganin har da ya Habib aka taho, farin ciki ya cika ni mara misaltawa, na kasa rufe baki na, Aunty na fitowa daga mota na je na rungume ta, ina ta murnar ganinta,

“Ga ƴata ga ƴata ta kaina.”

Na ce “Aunty kun dawo lafiya, ya hanya?”

Ta ce, “Lafiya alhamdulillah ƴar albarka.”

Gaishe da dady na yi, za mu shiga ciki ne ya Habib ya ce “Ni ba za ki gaishe ni ba kenan? Ko ya jiki ma babu?”

A hankali na juya gare shi na ware masa dara daran idanuwa na sannan na kashe masa daya daga ciki ina dariya ba wanda ya gani na ce, “Yi hakuri ya Habib, ya jiki?”

Ya ce “Riƙe abarki, sai da na roƙa.”

Dariya muka yi duka, dady ya ce “Lallai ja ya tafi ja ya dawo kenan, to Allah ya shige mana gaba.”

Na ji kunya sosai, a zahirin gaskiya ganin su Aunty tsaye a wurin ne ya hana ni duba jikin ya Habib, ashe hakan shi ne zai janyo fasuwar ɓoyayyen sirrinmu, ni dai kunya kamar na nutse wallahi, take kuma jikina ya ɗauki rawa, haka kawai duk sanda na haɗu da shi sai na ji rawar jiki, bugun zuciya da kuma kasala. A haka dai muka shige ciki gaba ɗaya.

A ciki kuwa kuwa falo suka zube gabaɗaya, inda ni kuma muka shiga kawo musu abinci da ruwa da lemo mai sanyi, tun kan na kawo farantin cin abinci ya Habib ya fara buɗe kulolin abincin kira yake,

“Girkin nan zai bada ma’ana.”

Dariya suka yi masa, idan da sabo sun saba da halin Ya Habib, mutum ne mai barkwanci da jan mutane a jiki, ba iya ni kaɗai ba har masu aikin gidan haka yake musu. Aunty sam ba ta gajiya da shi tunda ya zauna da su har ya gama jami’ar Bayero, aure ne ya raba su, shi aka yi masa gini a Farawa.

Cin abincin suke yi cikin nutsuwa, ya Habib ya ce,

“Amma ba Atine ce ta yi girkin nan bako?” Aunty ta ce,

“Wannan sai dai Halima, ka san ta, tana da ƙwarewa ta fannin girki.”

Take ya Habib ya ce,

“Ai na sani, daga jin ɗanɗano na san ita ta yi, wallahi yarinyar nan ko shayi ta dafa sai ka ji ya banbanta da na saura, kamar yar larabawa.”

Dady ya ce, “Ka cika surutu wallahi, ka sarara mana mu ci abinci.”

Aunty ta ce, “Kyale shi zafin da Maryam ta haɗa masa ne yake sa shi sambatu.”

Jin an faɗi sunan Maryam ya sa na ji ina son ƙara maida hankalina ga ƙofar falon don na ji me za su ce akan Aunty Maryam ɗin, haka kawai nake jin haushinta, sam matar ba ta yi ba ko kaɗan.

Ina iya hango su amma su ba sa ganina saboda ba su san ma ina tsaye a bakin falon ba, ya Habib ne ya kurɓi ruwan lemo ya ce,

“Ai wallahi yaya da a ce kai da Aunty ba kwa wurin nan ba abin da zai hanani kwakkwaɗa mata mari, kuma wallahi sai ta dawo min da Hafsah don ba zan yarda ƴata ta taso cikin irin wannan gidan ba.”

Dady ya ce,

“Ka daina faɗar haka, ba ka sani ba ko zamanku bai ƙare ba, amma ni kaina yarinyar ta ba ni haushi wallahi.”

Sai sannan Aunty ta ce,

“Na fuskanci duk yayarta Asma’u ɗin nan ce take zuga ta, don a jiyan da aka ce ita za ta kwana a asibiti yayar tata ce ta ce a’a , wai meye amfanin dady da ba zai kwana ba.”

Habib ya ƙara hasala kamar Asma’u na gabansa ya ce,

“Ai da kin faɗa min da tun a jiyan zan sake ta ba sai yau ba, wallahi na gaji da halin yarinyar nan, ƙazanta, rashin kunya, ba ta iya girki ba, sam ba ta iya tarairayar miji ba, wallahi Aunty wata ranar tana zaune zan dawo daga office tun biyar na yamma, amma wallahi sai na kai goma na dare in dai ba ni da kaina na je in da take ba wallahi ba za ta zo ba.”

Dady ya yi dariya ya ce,

“To me take yi a ɗakin?”

Habib ya ce, “Tana kwance kan gado tana chat da kawayenta, babban abin haushin har da maza take chat, mun yi faɗa sosai akan haka amma ta ƙi ji.”

Ƙarƙare maganar Habib ya yi da faɗin,

“Gobe in Sha Allah da ku za mu je ku ga wurin kayan Hafsah Allah sai kun sha mamaki.”

Aunty ta ce, “Ka dai ringa sassautawa, idan da rabo sai ka ga ta shiryu kun dawo da zamanku.”

“Da wa za ta ci gaba da zaman? Ni!”

Ya nuna kansa da yatsan manuni, Aunty ta ce, “Kai mana.”

Ya ce, “Allah ya tsari Gatari da saran danga, kina zaton waɗannan mutanen haka suke, ai wallahi ko ta yarda za ta dawo ƴan uwanta ba za su bari ba.”

Dady da ya kammala cin abinci ya ce, “Me ya sa ka ce haka ka ringa kyautata musu zato?”

Habib ya ce, “Na farko suna da kwaɗayin abin duniya, na biyu kuma ba auren ne a gabansu ba, na uku suna da taƙama ta banza da hofi, duk kuwa macen da ka same ta da waɗannan halayen, zai yi wuya ka zauna lafiya da ita, dole za ka same ta da rainuwa, ga rashin sirri, da kuma isgili.”

Dady ya ce “Sannun ka ƙanina, ka horu a hannun matar nan, da ba ita ka aura ba watakila ba za kai experiencing wadannan abubuwan ba, ka ga ni da ƴar tsuntsuwata lafiya muke zaune, ni duk ban san waɗannan matsalolin ba.”

Dariya suka yi duka jin dady ya ce ƴar tsuntsuwa.

Habib ne ya ce “Ai Aunty Lami ƙarshe ce, na bata lambobin yabo da yawa, kai kaso saba’in cikin ɗari.”

Aunty ta ce, “Me ya ci sauran talatin ɗin kuma, a bani su duka mana.”

Habib ya gayara zama kamar abin arziƙi zai faɗa, sai cewa ya yi,

“Sauran na amaryar da dady Auwal yake shirin yi miki ne.”

Duk da cewa da wasa ya Habib ya faɗi maganar sai da yanayin Aunty ya canja, ina kallonta ta tsakanin ƙofa, ɗan haɗe rai ta yi ta kalli dady sai kuma ta kauda kai, dariya ya Habib ya shiga yi, saboda ya kunna wuta. Wato dai shi kishin nan kumallon matan ne dai da gaske.

“Haka za mu yi da kai ko? Na maka rana za ka min dare? Ya yi kyau tashi ka fita ka ba ni wuri.” .

Ya juya ga Anty ya ce,

“Kin yarda da abin da ya ce kenan.”

Aunty ta ce, “Ka ji na ce wani abu ne.”

Ya ce, “A’a na ga kina harara ta ne.”

Dariya Habib yake ta yi, ban san ya tashi zai fito ba sai da ya zo daf da ƙofa na ji motsinsa, da sauri na yi ƙoƙarin barin wurin amma ina, tuntuɓe ya yi da ƙafata, garin na yi baya kuma sai nima na buge da kofar, saura kiris na kai ƙasa ya riƙoni da hannu ɗaya, ban da haka da sai na faɗi,

“Bismillahi! Sannu, ba ki ji ciwo ba ko.” A hankali na miƙe tsaye na ce “Eh!”

Allah shikara dady ya yi masa, dama sharri ya yi masa ga shi nan ya koma kansa.

Cewa Habib ya yi, “Yaya daina Allah shi ƙara ƴar ku na yi tuntuɓe da ita za ta faɗi.”

Dady ya ce “Subhanallah! Garin yaya? Wace ƴar ta mu?”

Habib da yake riƙe da hannuna har dady ya ƙaraso bakin ƙofar ya ce “Ƴar amanar Aunty.”

Yana faɗar haka Aunty ma ta miƙe ta biyo bayan dady, sannu suka shiga jera mini, don da Anty ta zaci Nana ce ko Fatima, amma jin Habib ya ce ƴar amana ya sa ta taso d asauri, don ba makawa ta san ni ce, “Sannu Halima, ke da ba ki jima da warkewa ba.”

Dady ya ce, “Allah dai ya kiyaye gaba.”

Rasa abin da zan faɗa na yi, na farko dai ba zan iya cewa laɓe na yi musu ba tunda laɓe ba kyau, sannan kuma na ji kunya sosai don ina kyautata zaton ya Habib ya gane a laɓe nake a wurin, cikin sakanni na ji dabara ta zo min na ce,

“Kwanuka zan ɗauka, Atine za ta wanke su.”

Aunty da fuskarta take cike da tausayawa ta ce,

“Ke dai ba kya gajiya Halima, don Allah ki je ki huta, kirawo Atine ta kwashe kwanukan.”

Kafewa na yi akan zan iya, duk yadda Anty ta yi dani na ce zan iya, haka suka haƙura, Habib ne ya taimaka min na kwashe komai, dady ya fita, Aunty kuma ta haura sama, wurin ya rage daga ni sai Ya Habib, sunkuyowa ya yi saitin kunne na ya ce, “Ina missing ɗinki Leemat.”

Rufe fuskata na yi da tafukan hannaye na, ya zauna gefe na, yadda ya gamu da hatsarin ya bani labari, sosai na tausaya masa, don Allah ne ya yi da sauran shan ruwansa a duniya da tuni motar tirela ta take shi har motarsa.

“Allah ya kiyaye gaba, kuma ka ringa kula.”

Ya ce, “Amin.”

Sai kuma muka yi shiru, can dai ya katse shirun da cewa, “Yanzu da na mutu ya za ki ji?”

Da sauri na ce, “Allah ma ya kiyaye, in sha Allah sai ka yi shekaru irin na dabino.”

Muka yi dariya gabaɗaya, baya na ɗan ja kaɗan saboda kusa da ni ya zauna sosai ina jin jikinsa na gogar jikina, wannna rawar jikin na damuna, kasala da bugun zuciya suka sake mamaye jikina.

Kamar na tambaye shi Aunty Maryam sai na ga ba hurumi na ba ne, sai na canja akalar tambayar kan ƴarsa, kawai sai na ce masa,

“Ya su Hafsah?”

Ya ce, “Suna nan ƙalau, so nake ma na ɗakko ta, ta dawo wurinki da zama gabaɗaya.”

Dammm! Na ji ƙirji na ya buga, dakewa na yi na shiga jera masa tambayoyi har guda biyu.

“Ka rufa min asiri, a wane dalili riƙon Hafsah zai dawo wurina? Ina mahaifiyarta?”

<< Halimatus Sa’adiyya 5Halimatus Sa’adiya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×