Dariya ya yi min sai kuma ya tanƙwashe ƙafa ya juyo ya fuskanceni sosai ya ce,
“Da sannu zan amsa miki tambayoyinki.”
Ban matsa akan lallai sai na ji ba nima muka shiga wata hirar, daga can kuma ya ce zai fita ya xaga gari, Allah ya kiyaye hanya na yi masa ya tafi ya bar ni da kewarsa, tuni na faɗa duniyar tunani.
A wannan lokacin na riga da na kamu da matsananciyar soyayyar Habib, duk kuwa da cewa ban taɓa hasasowa kaina auren mai mata ba, saboda ba na son kishiya, don ina da tabonta a ƙarƙashin zuciyata.
Sakin wannan tunanin na yi na kama aikin gabana, ni kaɗai na gyara gidan sannan na dawo kitchen, cooler na duba na ga abincin da ya rage a gidan ba shi da yawa sai na shiga kiciniyar ɗora wani.
Semovita na ɗakko leda biyu, sai nama da na ciro a freezer, tuwo na ɗora sannan na shiga haɗa miyar kuɓewa.
Ina tsaka da girki su Fatima suka dawo, tun a gate suke ta murna Mamansu ta dawo, da gudu suka shigo gidan suka min sannu sannan suka wuce ciki, Abdul yana ta kiran Mama Ina iya jiyo Muryar Anty da ta buɗe ƙofa tana faɗin,
“Ga Abdul ga Nana.”
Fatima ta yi kicin-kicin da fuska ta ce,
“Mama ko ta ni ba kya yi.”
Anty ta yi dariya lokacin da suke sakkowa ƙasa ta ce,
“To ga Fatima! Ga Fatima.”
Duk suka saka dariya har nima da nake kitchen, ganin ina ta haɗa tuwo da miya Anty ta ce,
“Halima ba kya hutawa ko kaɗan, da kin bari na zo na yi da kaina ai.”
“Haba Anty ai kin daina girki in dai ina nan.”
Anty ta ce,
“To na gode, Allah ya yi miki albarka ya kawo miji nagari.”
A zuciya na ce, “Ai ya kawo Anty.”
A zahiri kuwa murmushi kawai na yi, ala dole kunya nake ji.
Falo suka shiga, suna ta ba Anty labarin hidimar da na yi da su kwana biyu, Nana da ke tsaye bakin ƙofar falo tana cire kaya ta ce,
“Mama kin san me?” Ta ce, “A’a sai kin faɗa Nana ta.”
“Da ba kya nan ya Halima ce ke shirya mu ta yi wa Abdul wanka, ta sa mana Uniform, ta ba mu abinci a baki, idan za mu tafi makaranta ta saka mana biscuits da chocolate a jaka.
Fatima ta ce,
“Sosai kuwa ni sai da ma na je makaranta na ga chocolate a jaka ta.”
Abdul ma ya ce “Mama nima ta ba ni.”
Kwala min kira Anty ta yi duk da dama ina kitchen Ina jin duk tattaunawar su, daidai lokacin kuma Atine ta shigo da kwanuka kife a kwando, jera kowanne ta shiga yi a muhallin sa, ni kuma na tafi amsa kiran Anty.
“Ƴan uwanki ne suke ta ba ni labarin yadda kuka yi da su kwana biyu.”
Da alamu ta ji daɗi na fuskanci hakan ne daga yanayin yanda take ta murmushin jin daɗi, a ganina ko me na yi wa Anty ban faɗi ba wallahi tunda masu iya magana sun ce gaishe da mai gaishe ka.
Ta ce, “Na gode, Allah ya yi miki albarka.”
Na ce, “Amin.”
Shiru ya ɗan ratsa, dama tuni yaran suka tafi ɗakinsu don yin wanka, Anty ce ta katse shirun da cewa,
“Ni da yaya zai bar min ke ma da ba haka ba.”
Cikin jin daɗin maganar da ta yi na ce,
“Ke za ki tambaye shi Anty, ni kaina na fi son zama a wurinki, ba na jin daɗin zaman can wallahi.” Na ƙarshe maganar da raunananniyar murya.
Anty ta fuskanci haka, sai cewa ta yi,
“Ki yi hakuri, duk abin da yake faruwa muna sane da shi, amma ba mu da wata power a kai, kin dai san halin yaya sam ba ya ɗaukar shawara.”
Sosai na san halin mahaifi na, na san waye shi, na san yanda yake idan ya kafe akan abu to fa ba mai juya shi, haka zalika idan yana son abu to ba wanda ya isa ya dakatar da shi. Wani lokacin sai ka rantse aljanu ne da shi kuma lafiya lau yake, kawai shi mutum ne mai tsattsauran ra’ayi.
Ko abin da mama take yi son da yake mata ne ya jawo ba ya iya ɗaukar mataki a kanta, da wannan son ta yi amfani idan ta shirya masa ƙarya da gaskia a kanmu yake yarda.
“Haka ne Anty, amma don Allah ki gwada roƙonsa, idan ya yarda shi kenan na huta.”
Anty ta lura da halin da nake ciki sai ta ce,
“Bari za mu yi magana da dady, idan ya amince shi zan sa ya masa magana da kansa.”
Godiya na shega jerawa mata, cikin zuciyata kuwa farin ciki ne fal, idan wannan ƙudirin na Anty zai cika na fi kowa murna da haka.
Ktchen na koma kafin magariba na haɗa komai, gida ya ɗauki ƙamshi girkin da nake yi, zuwa sannan yaran duk sun yi wanka, suna jiran abinci ya sauka, don Nana har ta nemi wuri ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun dinning.
Sai da muka yi sallah gabaɗaya sannan na zubawa yaran abinci, ƙa’idar Anty ne dole a ci abincin dare da wuri, musamman idan da nama a ciki, tunda nama ba ya narkewa da wuri a jikin ɗan adam musamman da daddare, hakan kuwa aka yi tunda tuwo ne yana da nauyi shi ya sa suke cinsa tun kafin sallar Isha’i.
Sosai zamana da Anty ya sa na fara sanin abubuwa ma su amfani ga lafiyar ɗan Adam, kasancewarta Health Educator.
Washegari da wuri muka tashi, shirin islamiyya na sa su Fatima suka yi, Atine kuma ta haɗa breakfast, suka ci sannan suka tafi makaranta.
Gyara gidan muka yi na koma sama na yi wanka, sannan na sake komawa bacci, sai shabiyu muka tashi har su Anty.
Muna tsaka da cin abinci ya Habib ya shigo, chips ya ce na zuba masa da romon naman kai, bayan na zuba na miƙa masa na ce,
“Ƙwai fa?”
Ya ce “Kyale kwan nan.” Shayi na haɗa masa mai kauri, ya karɓa yana min shu’umin murmushi, raɗa ya yi min a daidai kunne na ta yadda su Anty Lami ba za su ji ba.
Na zare idanu na cike da firgicin abin da ya faɗa min, girgiza masa kai na yi murya can ƙasa na ce,
“A’a.”
Dariya ya yi muka cigaba da cin abinci.
Muna gamawa na miƙe na haɗa kayan wurin wanke-wanke na kaisu, lokacin Atine ma ta gama cin nata abincin. Komawa na yi parlon na na gyara a lokacin dady ya shige ɗakinsa Anty ma ta koma ɗaki parlon ya rage daga ni sai ya Habib.
“Kin yi kyau.”
Ya faɗa yana karewa fuskata jikina kallo.
Murmushi na sakar masa na ce,
“Na gode.”
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi, ya fara magana da sautin da ni kaɗai nake iya jinsa.
“Halimatu tambayarki nake son yi kuma ki faɗa min gaskiya kin ji ko.”
Fuskantarsa na yi sosai, don da alamu magana ce mai muhimmanci yake son mu yi.
Cewa na yi “To, ina jinka.”
Yana daga zaunen ya miƙa hannu ya ɗauki remote ya rage ƙarar Tv, ya soma magana cikin nutsuwa.
“Wato Halima ina cikin wani hali da matata, na san dai ko ban faɗa miki ba, kin san wasu abubuwa, don an ce gabanku ranar da su dady za su je wurina bayan na yi hatsari ta yi, to a can ma hakan ta kuma yi, abin dai ba daɗin faɗa, daga ƙarshe dai a asibiti na mata saki ɗaya.”
Zaro idanu na ya waje cike da mamaki kuma na ce,
“Saki kuma? Me ya sa ka biye mata?”
Murmushin takaici ya yi ya ce,
“Halima ba ni da sakat a gida na, sai Maryam ta hau yi min rashin kunya, ga binciken wayata, ba ta girki, ga kiwar tsiya da son jiki, ke abubuwa dai kala kala marasa dadin ji, na rasa yanda zan yi.” Shiru ya yi, kamar ya yi kuka, take kuma wani mugun son shi da tausayinsa ya mamaye min jini da tsokar jikina.
Mamakin Anty Maryam ne ya kama ni, ni ban san me zan ce masa a kan wannan matsalar ba kawai dai na ce,
“Gaskiya ba ta kyauta ba, amma kai me take ƙorafi da shi a kanka?”
Ɗan zamewa ya yi kan carfet, ya jingina bayansa da jikin kujera ya ce,
“Ƙorafin dai bai wuce na ban dawo gida da wuri ba, ko ban bari ta fita unguwa ba, sai ko rashin fuska da ba na ba wa ƴan uwanta da ƙawayenta.”
Haushin Anty Maryam ne ya turniƙe ni a wannan lokacin, in dai haka ne ita ce da laifi gaskiya
“Ya Habib ka yi hakuri gaskiya ba ta kyauta ba, ai ba a haka, yakamata ace ta yi aiki da tunani ta ringa banbance matsayin miji da na ƴan uwanta, don abin haushi har da wasu kawaye.” Na ja tsaki.
Mamaki na ya shiga yi, bai taɓa jin na yi doguwar magana tare da bayyana tsantsar ɓacin raina ba kamar yau, take ya fara dariya har da tafa hannaye ya ce,
“Sweetheart dama kina magana haka?”
Ƙasa na yi da kaina don ji na yi kunya ta kamani, ganin ba zai daina tsokana ta ba yasa na dake na ce,
“Allah ya Habib Anty Maryam ɗin ce da abin haushi.”
Cewa ya yi,
“Wallahi kuwa, ai ita duk ba ta san salo da yadda za aya ja hankalin mijinta ba, ke idan zan zauna na zayyane miki halin da nake ciki da Maryam Allah sai kin raina tunanin ta saboda haushi, gabadaya ba ta da daɗin zama wallahi.”
Don na sanyaya masa rai sa ne ce,
“Ka yi haƙuri, amma da ba yi saurin biye mata ba wallahi.”
Ya ce,
“Ke ba za ki taɓa fahimtar halin Maryam ba, ita zuma ce sai da wuta.”
“Allah ya sawaka.”
Na ce, sai cewa ya yi.
“Amin! Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son maye gurbin Maryam da ke, saboda na yarda da tarbiyyar ki, sannan ina saka ran samun kulawa a wurinki, zan yi alfahari idan aka ce Hafsah ta dawo hannunki da zama duk kuwa da ƙarancin shekarunki kina da hankali da nagartattun halaye.”
Rufe fuska ta na yi da tafukan hannaye na, maganar da ya yi ta zo min bazata, saboda ban yi tsammanin zai bayyana min maganar da wuri ba, don har ga Allah na daɗe da son ya Habib cikin zuciyata, kuma shi ma na san ya fuskanci haka, ga yadda nake sakewa idan ina tare da shi ya san so ne kaɗai zai sa haka.
Katse min tunani ya yi da cewa,
“Idan ba ki amince ba ki faɗa min, ba zan takura miki ba don muna da zumunci mai karfi da Anty.”
Kasa ba shi amsa na yi, na dai gyaɗa masa kai kawai, bayan ya sake tambaya ta na amince ko ban amince ba.
“In sha Allah za ki ji daɗin zama da ni Leemat.”
“Allah ya sa.” Na ce masa, daga nan ya tashi wai zai koma ya kwanta tunda yau Sunday, sai yamma zai fita training.
Nima tashi na yi bayan ya fita muka shiga hidimar ɗora girki da Atine, ta gidan kowa ce shinkafa da miya sai naman sa, sai pineapple juice da zoɓo da ya ji kayan ƙamshi.
Ƙarfe uku saura muka gama girkin, kashewa na yi a cooler, ni na zubawa Atine nata sannan na gyara kitchen din, wanka na je na yi da yake yau ina fashin sallah sai na yi light makeup kawai, lace na saka milk color da adon Orange a jiki, kayan sallah ta ne dama, sosai kayan suka yi min kyau, ban ɗaura ɗankwali ba, sai na saka ƙaramin mayafi orange ne shi ma, sosai na yi kyau, ƙasa na sakko daidai lokacin kuma ya Habib ya fito shi ma muka haɗu a corridor.
“Tsarki ya tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki .”
Dariya na yi tare da yi masa fari da idona, ɗan ja baya ya yi kaɗan ya ce,
“Wayyo Leemat za ki kashe ni da gayunki.”
Dariya na shiga yi, sosai ya Habib yake burge ni, ba ya jin nauyin yabawa duk wani abu da na yi, dama kuma ina son hakan, ina matuƙar so na yi abu a yaba min, wannan halin nasa shi ya sa kullum nake mamaki yadda Anty Maryam ta yi sake ya kufce mata, wata zuciyar ta ce min da ba ta sake shi ba ai da ba ki samu ba.
Zuwa ya yi daf da ni ya tsaya, ƙare min kallo ya yi sosai sannan ya ce
“Leemat ke kyakkyawa ce ma sha Allah.”
Ɗan zame ɗankwalin kaina ya yi sai na ji wani iri, ban saba ba, wani namiji bare bai taɓa kai hannunsa kan mayafi na ba amma ya Habib har da taba min kai.
“Masha Allah.” Ya faɗa bayan ya yi tozali da kwantaccen baƙin gashi na.
“Zuba min abinci.”
Ya faɗa tare da shigewa parlor murmushi ne kwance saman fuskarsa, daidai lokacin kuma su Anty ma suka sakko tare da dady, sannu da gida na yi musu, sai na haɗa abinci duka na kai musu ciki, har zan fita ya Habib ya ce,
“Ba ki ƙarasa ladanki ba ƴar gidan Anty.”
Na gane nufinsa don haka na dawo zan zuba masa dady ya ce,
“Wallahi halinka sai kai.”
Anty dai dariya take yi, can ta ce,
“Ai ni dai ina cikin farin ciki, tuwo na mai na, Allah ya tabbatar mana da alkairi.”
Dariya suke yi duka, ni kuma kunya ta cika ni kamar na nutse.
Wato zaman gidan Anty na burge ni wallahi, sun iya gudanar da soyayyar su ita da dady, zubawa ya Habib abincin na yi na fice daga parlon cike da kunya.
Ina sama bayan na gama cin abinci su Fatima suka dawo, da gudu suka hawo saman, jin motsinsu ya sa na tashi ina musu oyoyo, Fatima ta ce,
“Anty yau na sha dariya a ajinmu, kin ga wata ta tada aljanu, ta yi kan ya mu’allim ai kuwa da gudu ya fice daga ajin.”
Labarin ya ba ni dariya sosai, na ce,
“Ai dole, wasu mazan ba sa son mace mai larurar aljanu, tsoronta ma suke ji.”
Haka dai muka yi ta dariya, Anty ta leƙo ta ce mana sun fita ita da dady, a dawo lafiya muka yi musu muka wuce da yaran parlor, nan suka ci abinci, muka kunna kallo bayan sun yi wanka.
A ƙage nake juma’a ta yi mu je gidanmu, so nake kawai na je na ba wa takwara labarin Ya Habib, na san za ta karfafa min guiwa akan soyayyarmu, ina ƙaruwa sosai da shawarwarinta.