Skip to content
Part 8 of 12 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Ranar Alhamis da wuri muka gama komai, muka koma ɗaki ko wanka ba mu yi ba, tsefe kai muka shiga yi, dama ni kalba ce a kaina, su kuma kitso ne, muna tsifar ne Anty ta leƙo ɗakin ta tarar da mu, to tunda ta ga tsifa muke sai ta ce,

“To ku yi sauri ku gama, dama zan fita da ku ne, sai mu je saloon.”

Na ji daɗin haka, dama na kwana biyu ban yi steaming ba, ƙarasa tsife nawa na yi, na taya Nana ma ta ƙarasa nata, sannan muka yi wanka, Fatima sai rawar sanyi take yi wai yau ana sanyi sosai.

Na ce mata, “Ni kam ba na jin sanyi yau.”

A gurguje na shirya, baƙar abayar mai adon silver da Anty ta saya min na saka, na zagaye kaina da ash ɗin mayafi, baƙin takalmi na saka mara tudu halayya ta ce sanya flat shoe, na ƙarasa gaban mudubi na tsaya ina kallon kaina, maganar Allah ni kyakkyawa ce, ga farar fata, uwa uba manyan idanuna a fili na furta, “Alhamdulillah.”

Fatima ta ce, “Ya Halima wai Ammanki balarabiya ce?”

Dariya na yi ba tare da na kalle ta ba na ce mata,

“Me kika gani?”

Sai ta fara zayyano min abubuwa kamar haka,

“Kina da farar fata ba irin tamu ba, kina da dogon gashi kuma mai laushi kamar na Queen jodha, sannan kyawun fuskarki ya wuce a ce ke bafulatana ce kawai, a taƙaice dai kina kama da India.”

Dariya kawai na yi don ba ni da amsar ba ta, rabon da na ga mahaifiyata tun ina da shekaru biyar a duniya, saboda haka ba abin da zan iya ɗorarwa game da ita, kuma ma dai ganin Abba ba ya son maganarta ya sa ban cika ma yin bincike a kanta ba, kawai sia na ce mata,

“Ni bahaushiya ce, saboda Abba na bahaushe ne.”

Goga lipgloss a bakinta ta ce,

“Na sani ai, shi ya sa na tambayi Ammanki ita ce ban sani ba.”

Jin da na yi idona na son kunyata ni da hawaye, sai kawai na ce mata,

“Kin yi kyau ma sha Allah.”

Ta ce, “Na gode.”

Muna haka Ya Habib ya hawo saman yana faɗin,

“Me kuke yi ne har yanzu ba ku fito ba, ku fa muke jira.”

Shiru ya yi lokacin da ya turo ƙofar ya yi tozali da adon da na yi, ƙarasa shigowa ɗakin ya yi, kallona yake tun daga sama har ƙasa, gabaɗaya kunya ta lulluɓe ni, dama tuni Abdul ya bi bayan Anty tunda ta shigo ta sanar damu fitar da za mu yi, a hankali ya ce min,

“Kin yi kyau my Leemat.”

Dariya na yi masa ina ji son sa yana ratsa kwanya ta, kashe masa ido na yi na ce,

“Na gode.”

Tare muka fita har ya Habib ɗin, kafin mu ƙarasa inda motar take ya ce,

“Wai ba ki da waya ne?”

“Eh!” Na ce masa, bai kuma cewa komai ba muka shige mota.

Ya Habib ne ke tuƙi, Fatima a gefen sa, daga bayansa kuma ni ce, sai Nana a gefe na, Abdul ne ya raba tsakanin Nana da Anty.

Yasmin sloon muka je, nan aka wanke mana kai, duka steaming aka yi mana, ban da Nana da aka yi steaming ake kuma Straightening gashinta don yana da tauri.

Bayan an gama komai Anty ta biya kuɗi, Habib ya ce, ya biya mana gabaɗaya.

Anty ta ce, “To an gode.”

Kwari muka wuce daga nan, kantin El-samad muka tsaya, mayafai Anty ta saya medium size kaloli mabanbanta, sai dankunnaye su ma kaloli ta kwasa, sai wasu turaman atamfofi da ta saya muka je ta biya kuɗi muka fito, na ji dadin fitar don mun zaga gari sosai.

A gajiye muka shiga gida, sallah muka fara yi a parlor, sannan aka kwance kayan, fito da mayafan Anty ta yi ta zube su gaban mu ta ce,

“Zaɓi kala biyu.”

Dark green da yellow na ɗauka, saboda ina da wani yallon lace mai fulawoyi dark green, sai kuma atamfa ta da Abba ya dinka min da sallah, ita ma ba ta da mayafi, da ma wasu kayan masu yellow a jiki duk ba su da mayafi.

Fatima kuwa peach color ta ɗauka da light purple, sannan Anty ta kwashe sauran kayan, ta ce mu bi ta da su sama.

Da yake ba mu yi girki da daddare ba, Anty ta ce mu yi indomie da ƙwai idan muna so, ita kuma a dama mata fura a sa a freezer, muna tsaka da haɗa indomie dady ya shigo shi ma, muka yi masa sannu da zuwa, ya c tunda ya ji ƙamshi dahuwar ya ce, a sa indomie da shi.

Muka ce, “To dady.”

Fatima na biye da ni, don tun da na warware na soma girki, tare muke yi, in dai ba su da makaranta, don kafin na zo ba sa shiga kitchen, da na zo na canja musu akala, har Nana koya mata nake yi.

Ya Habib ne ya shigo shi ma dai cewa ya yi a haɗa da shi zai ci, nan da nan na haɗa komai na dafa indomie, yankakkiyar albasa da tumatir na ringa ɗiba ina fasa ƙwai a kai ina soyawa, sai ɗan maggi, sai dambun nama da na saka, ƙamshi sai tashi yake.

Anty da ƙamshi ya gama ziyartarta a sama, sakkowa ta yi daga benan tana cewa,

“Iyeee! To a zuba min, a bar furar nan sai gobe.”

Muka yi ta mata dariya kuwa, ita da dady a plate ɗaya na zuba musu, ya Habib kuwa zubi na yi masa na musamman, shi ma na siya masa ƙwai.

Fatima ce ta kai musu parlon, Atine ta ɗauki nata, mu kuma muka ɗauki namu muka tafi ɗaki, kowa ya ji daɗin dahuwar tawa, yau har dady ya yaba da abincin.

Anty ce ta zo wai dady na kira na a parlor, faɗuwar gaba na fara ji jikina har rawa yake don na san kwanan zancen, hijabin sallah ta na saka na bi bayanta.

Parlon na shiga da sallama suna zaune duka, Habib na gefen dady yana danna waya, guri na samu daga gefen Anty na zauna, ina zama dady ya soma magana.

“Alhamdulillah! Na ji daɗin yadda kuka haɗa kanku, amma dai ina so na ji ta bakinki Halima, don ba na son a yi miki dole, idan ba ki amince ba ba za mu takura miki ba.”

Shiru na yi zuciya ta cike da farinciki, zancen ma na ce ban amince da ya Habib ba ai bai taso, son shi ya zama jini da tsokar jikina, a zahiri kuwa kunya ce ta hana ni magana, ganin na yi shiru ba yi magana ba Habib ya yi caraf ya ce,

“Dady ta amince fa, mun gama magana da ita.”

Dady ya ce, “Ba kai nake tambaya ba, na san ka da son kai tsaf sai ka takura ta da shegen surutunka.”

Dariya Anty ta yi ta ce,

“Bari na ari bakinta na ci mata albasa.

Habib ya ce “Yauwa Anty.”

Anty ta ce,

“Halima ta amince, amma gaskiya akwai shirin da nake mata, ina so ta ci gaba da karatu, kuma dama na faɗa maka tun jiya.”

Ta dubi dady da yake kallonta tun da ta fara magana.

Daɗi ya ce, “Ƙwarai kuwa, ai karatu kusan dole ne ma za mu ce, idan ya amince shi kenan sai manya su shiga maganar.”

Anty ta ce, “Yauwa dady.”

Ta dubi Habib ta ce, “Ka amince da haka?”

Habib ya yi dariya ya ce,

“Ina da wannan burin dama ko da ba ku shirya mayar da ita ba, ni zan mayar da ita da kaina.”

Godiya muka yi wa Allah gabaɗaya, duk da dai a zuci na yi tawa.

Dady ya ce mana mu tashi mu je, Allah ya yi mana albarka baki ɗaya.

Ina miƙewa Habib ya biyo baya na, ya jawo ƙofar parlon ya rufe, a kitchen ya tsayar da ni, abin mamaki kuma abin tsoro sai kawai na ji ya rungume ni ta baya, a tsorace na ce,

“Innalillahi! Ya Habib meye haka?”

Jikina na rawa na fara ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da ya yi min, amma sai ya ƙi cika ni, tuni ya gama yawo da hannayensa ilahirin jikina, ture shi na shiga yi, amma inaaa! Ya haɗa ni da ƙirjinsa gam, magiya na shiga yi masa baki na na rawa, hawaye tuni ya gama wanke min fuska, ban taɓa haɗa jiki da namiji ba, yau da Habib ya ƙanƙame ni, sai nake jin wani shocking a jikina.

Ganin ba shi da niyyar cika ni ya sa na sanya dukkan ƙarfi na na ture shi, na haye sama da gudu, ƙirjina sai bugawa yake, ina ji yana kira na ko waigowa ban yi ba bare na amsa masa.

Ɗakinmu na shiga na kulle, har da danna key a ƙofar, don gani nake kamar ya Habib zai biyo ni saman, na lafe daga can ƙarshen katifa, na tsorata sosai, haushin ya Habib kawai make ji, saboda tsabar tsoro daren ranar nan ban rintsa ba ko sau ɗaya, da na rufe ido ya Habib nake gani da abin da ya yi min, addu’a na yi ta yi, na nemi tsarin Allah akan ya kare ni da irin wannan ƙazamar soyayyar.

A kunne na aka kira assalatu, don haka na na yi alwala da yake ina fashin sallah sai na yi bitar karatu, komawa na yi na kwanta sai da gari ya fara haske wani nannauyan bacci ya ƙwamushe ni, ai kuwa na yi mai isa ta, ban san lokacin da su Fatima suka tafi makaranta ba, sai farkawa na yi na ga lokaci ya ja, shabiyun rana saura kwata, da sauri na tashi zaune, ganin ba su Nana a kan katifa na ce,

“Alhamdulillah!” Na san sun daɗe da ficewa makaranta.

Toilet na shiga na yi brushing sanna na watsa ruwa mai ɗumi a jikina, take kuma fuskar ya Habib ta fara yi min gizo, faduwar gaba na ji, da sauri na gama wankan na fito ɗaure da zani, hular kaina na cire na shiga shafa mai, kamar motsin mutum na soma ji a bayana da sauri na juya amma banga komai ba.

“Bismillahil Hakim.” Na faɗa lokaci ɗaya kuma na isa gaban madubi, gashin kaina na fara tajewa, saboda na ƙagu na taɓa gashin ya yi kyau sosai, mai na shafa, na koma bakin closet.

Riga da skirt na ɗakko na saka, na pink ɗin atamfa mai adon light blue a jiki, ban ɗaura ɗankwali ba na dai yafa babban mayafi shi ma light blue ne.

A hankali na fara sakkowa ƙasa gabana na ta faduwa sai addu’a nake, Atine na samu a kitchen tana fere doya, gaishe ta na yi da fara’a, ita ma fara’ar take yi min bayan ta amsa gaisuwa ta ta ce,

“Na ji abin arziƙi, ashe yar gida za a yi mana.”

Ban ce komai ba illa dai na yi dariya, cewa ta kuma yi,

“Allah ya sanya alheri.”

Na ce “Amin.” A kunya ce.

Tambayar ta na yi ina Anty, ta ce tana can farfajiyar gidan.

Fita na yi wajen tun ban ƙarasa wurin ba na hango Anty na watsawa mota ruwa dady na wankewa, dariya na yi a raina na ce “Anty ba dama.”

Ina isa wurin na gaishe su, suka amsa cikin sakin fuska, Anty ta ce,

“Ba dai har kin shirya ba.”

Na ce “A’a, ai kin ce sai bayan masallaci za mu tafi ko?”

Anty ta ce, “Eh sai huɗu ma nake tunani.”

Komawa na yi ciki abina, abinci na ɗauka na koma sama, na ji daɗi da Allah ya sa ba mu haɗu da ya Habib ba, don da farko har na yi hanyar parlor na fara tsinkayo muryar Habib ɗin, ai da gudu na canja akalar zuciyata na haura sama a guje, Allah dai ya taimake ni ba mu haɗu ba.

Haka muka yi ta wasan ɓuya da shi har lokacin Masallaci ya yi, suka tafi shi da dady da Abdul don bai je makaranta ba a ranar, ko ta kan girki ban bi ba, daman Anty ta ce huta a ranar, ita za ta yi abinci.

Ashe fitar da Habib ya yi su Fatima ya tafi ɗakkowa a makaranta, na san haka ne a bakin Abdul da ya kawo min wata ƴar takarda daga ya Habib, na karɓa ban ce komai ba.

Wanka yaran suka yi sannan suka ci abinci, canja kaya na yi daga atmafa zuwa wani material red ne shi kuma, da adon stonse golden. Ɗinkin doguwar riga ne ya min kyau sosai, duk sun fice ni ake jira, da sauri na sakko hannuna riƙe da mayafi da ɗan kunne, ina fitowa cikin rashin sa’a muka yi kaciɓus da ya Habib shi ma ya fito, yana hango ni ya tako da sauri, caraf ya kama hannu na lokacin ina ƙoƙarin guduwa, ɗaya hannun nawa da ba komai na saka na kwaɗa masa mari, take ya sakar min hannu, ina kallonsa ido cikin ido ya dafe kuncinsa, na ce, “Wannna shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zaka sake dora hannunka a jikina, akan haka kuma zan iya rabuwa da kai wlh.” Ina kaiwa nan na wuce na bar shi tsaye dage da kunci. Ina shiga mota dady ya tada ta muka bar gidan.

Cikin ikon Allah muka isa ƙofar gidanmu, nan dady ya yi parking muka shiga ciki, shi kuma ya wuce sabgoginsa.

Mama ta karɓe mu ba yabo ba fallasa, bayan sun gaisa da maman ne Anty take tambayarta,

“Ina su Ummee ne?” Mama ta ce,

“Sun tafi bikin ƙawarsu.”

Miƙewa Anty ta yi ta ce,

“Bari na shiga wurin Zaituna.”

Zaituna matar Abbaa Ibrahim ce, tana da kirki, sai dai tana da rowa da ƴar ƙazanta, ganin Anty ta tashi nima na miƙe tsaye ina faɗin, “Anty bari na je gidan su Sa’adiyya.”

<< Halimatus Sa’adiya 5Halimatus Sa’adiya 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×