Skip to content
Part 9 of 12 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Aunty Lami ta ce da ni, “A dawo lafiya, amma kada ki zauna kin ga Abbanku ya kusa dawowa.”

Amsa mata na yi da “To.” Na fice su kuma su ka shige wurin Anty Zaituna.

A soron ƙofar gida na yi kaciɓus da takwara sanye da uniform za ta tafi islamiyya, Allah ne ya yi za mu haɗu, ai kuwa muka rungume juna muna murnar yaushe gamo, kallo na take tun daga sama har ƙasa tana dariya ta ce,

“Gaskiya kin yi kyau kawata, gidan Anty ya karɓe ki wlh.”

Dariyar nima nake yi na ce mata, “Mu je ciki Hajiyata akwai labari fal a bakina.”

Ta ce, “Mu je ciki to yau Aminta ta lashe wlh don ba zan je ba.”. (Aminta, sunan islamiyyar su takwara ne.)

Cikin muka shiga muna ta murna, a tsakar gida muka tarar da Umma tana kwashe tuwo a kula gaishe ta na yi, ta tambayi jikina na ce mata,

“Alhamdulillah Umma na warke sosai.”

Ta ce, “Masha Allah, ya Lami ɗin da yaranta?”

Na ce mata, “Duk lafiya lau suke.”

Ɗaki muka wuce muka fara hira, can na ce da takwara, “Ƙamshin manja nake ji wlh.”

Ta ce, “To mayya tsakiya da manja na yi, kin san ba na son tuwon can.”

Ta jawo food flask ta ce, “Ki ɗiba ki bar min sauran, kuma wallahi kada ki cinye min salad ehe don na san hali.”

Na ce, “To jarababbiya, na ce miki zan ci salad ne, ban yaji kiga.”

Bayan na kammala na sha ruwa muka shiga wata hirar, labarin haɗuwa ta da ya Habib kaf na kwashe na faɗa mata na kuma tabbatar mata da aure na zai yi nan ba da jimawa ba, na ce, “Takwara dole na so shi fa, kinga yadda yake nuna min so a gaban kowa kuwa.”

Bi na kawai take da ido, to ganin yadda yanayinta ya sauya lokaci guda sai duk na damu, cewa na yi mata, “Ya kika yi shiru kuma?”

Sakin fara’a ta yi duk da dai na ga kamar a takure ta ke, kamar ba saurare na take ba amma sai ta ce, “Ba komai, na miki murna Allah ya sanya alheri.”

Na yi mamaki da iya abin da ta faɗa kawai dai na ce “Amin, kuma kin san zan ci gaba da karatu, yanzu haka ma maganar da ta kawo mu kenan wurin Abbanmu.”

Gabaɗaya yanayin takwara ya gama sauyawa, dole akwai damuwa a tare da ita, ko dai game da abin da nake faɗa mata ko kuma dai wani abin daban, saboda hankalinta ba a kaina yake ba sam, girgiza ta na yi ina faɗin,

“Dalla kin yi shiru ina ta zuba ni kaɗai kamar wata kanyar da ba zaƙi.”

A ɗan firgice ta juyo gare ni, ko ba ta faɗa ba na san tunani ne fal cikin ranta, sai cewa ta yi,

“Ke ƙyale ni, tunanin irin hidimar da zamu gudanar yayin bikin nake yi.”

Dariya na kyalkyale da ita tare da da cewa, “Duk saurin unguwar zoma ta bari dai a haihu ko?”

Dariya ta yi ita ma ta ce, “Haka ne, amma mai kwarmin ido da wuri yake kuka, na ce mata “Haka ne kuma.”

Miƙe ƙafata na yi na jawo ƙaramar jakata, na zuge zip na ciro mata robar Humra da na taho mata da ita na miƙa mata, ta karɓa tana dariya ta ce,

“Na gode.”

Sannan ta fesa a bayan hannunta ta ce,

“Gaskiya tana da ƙanshi.”

Anty ce ta ban dama na kawo miki, godiya ta shiga yi na ce mata, “Ki riƙe godiyar nan idan kun haɗu kya yi mata ke da ita.”

“Kya ji da shi.” Ta faɗa tana adana humrar kan madubi.

Tambayar ta na yi, “Kin dai ƙi fidda mana da gwani?”

“Hmn.” Ta ce.

Na sake cewa, “Idan ba ki da niyyar fitarwa ki bari na fitar miki da kaina.”

Harara ta ta yi sai kuma ta yi dariya, ta zubawa waje ɗaya idanu, kasa jurewa na yi na ce mata,

“Wai lafiyarki daya kuwa?”

Ta ce, “Me kika gani?”

Na ce mata, “Yanayinki ya nuna akwai damuwa.”

Kafewa ta yi akan ba abin da ke damunta, ni kuma na ce, “Ƙarya kike wallahi, amma bari na ƙyale ki idan ta fadi ma ji.”

Tsaki ta ja ta ce, “Ke ko?”

Na ce, “Ni me, me na yi?”

“Ba za ki canja ba.”

Na ce, “Ai gaskiya ce ba kya so shi ya sa.”

Can ta nisa duk ina hankalce da ita ta ce, “Gaskiya ga yadda kike faɗar halayyar Habib sai nake gani matarsa Maryam ta yi wata.”

Ai sai wani daɗi ya lulluɓe ni, ashe tunani ta tafi kan abin so na shi ya sa ta yi shiru.

“Haka kowa yake cewa.”

Duk hirar nan da muka yi ban faɗawa takwara Habib ya taɓa ni na mare shi ba, a ganina wannan sirrina ne, komai aminci ka da mutum ba komai ne kuma za ka fito ka faɗa masa ba, shi ciki ba don tuwo aka yi shi ba, wani lokacin mutum shi ke cakawa kansa wuƙa sai maƙiyi ya taya shi burma ta cikin cikinsa, ashe wannan abu da na yi shi ne babban kuskuren da zai canja min akalar rayuwata gabadaya, shi ne babban sanadin da zai sa na yi hankali a duniya.

Takwara ce ta katse ni da cewa, “Kika ce yan Kaduna ne su ko?”

Na ce mata, “E! Gidansu sun yi suna a Kaduna fitattu ne.”

Ta ce, “Ai kuwa Umma na da ƴar uwa a can, amma su a Rigasa suke da zama.”

Na ce, “Alhamdulillah, ki ce ni lafiya lau da ni, ko zaman Kaduna ya kama ni ina da uwa a can, ba wata matsala.”

Ta ce, “Sosai kuwa, Anty Hindu na da kirki, ga son mutane.”

Na ce “Irinsu ake so Hajiyata.”

Ba na iya gani na yi shiru, don haka na sake cewa,

“Takwara Allah yaƙe kike yi, amma kin ƙi faɗa min damuwarki.”

Ashe tambayar da na yi mata ƙara jefa ta cikin ƙunci na yi ban sani ba, murya shaƙe da alamun ɓacin rai ta ce,

“Ai sai ki yi, na ce miki ba komai ba komai amma kin ƙi yadda, idan da wani abu ai zan faɗa miki ko dole za ki min na faɗa, ni ba na son takura a rayuwa.”

Tunda na ji haka sai na kame bakina, amma dai ina ta mamaki ba mu taɓa haka da ita, a da can baya asalin halayyata ba mai don magana ba ce ni, amma sannu a hankali sai da takwara ta canja min wasu daga cikin ɗabi’u na na furta zance, yau ga shi ita ta ƙosa da tbayoyin da nake mata, ganin ta yi fushi sosai sai na ce mata,

“Yi hakuri ki maida wuƙar.”

Ta yi fushi sosai, shi ya sa na ƙyale ta, kuma ba na so mu rabu cikin ƙunci tunda ba haka na same ta ba da farko.

Fitowa na yi zan tafi, mayya ta na biye da ni, Umma ta ce, “Har za ki tafi, kin dai zama ƴar hotoro.”

Na yi dariya, sai ta miƙo min leda ta ce, “Ga shi nan ki kaiwa Lami, kuka ce da zoɓo.”

Karɓa na yi na ce mata “An gode Umma Allah ya saka da alheri.”

Ta ce, “Ke kin ji ni da Halima kamar wani abu na bayar.”

Na ce, “Duk da haka Umma.”

A hanya muka haɗu da wani saurayi, ya yi mana sallama yana daga ɗan nesa damu kaɗan sai ya ce, “Ɗin Allah Ina son magana da ke.”

Sa’adiyya ta yi saurin cewa, “Ni?”

Ya ce, “A’a, wannna balarabiyar.”

Sai sannan na ɗaga ido na ganshi, saurayi ne matashi, kallo ɗaya za aka gane kyawunsa, haiba da kuma cikar kamalarsa, cewa na yi masa, “A’a malam sauri muke, kuma ma nan ai kan hanya ne, idan magana kake son yi da mu ka ke gida.”

Na kama hannun takwara za mu tafi ya sha gabanmu ya ce, “Haka ne na ji daɗi da ba ki min mummunar fahimta ba, sunan ki da gidanku za ki faɗa min Please.”

Na ce masa, “Suna na Sa’adiyya.” Sannan na kalli takwara ta ce, “Ina ruwa na ba sunanki kika faɗa masa ba.”. Gaba ta yi ta bar ni da shi.

Ya ce, “Na gode, gidan su wa zan ce idan na shiga layin.”

Na ce, “Gidan su Aminu.”

Ya min godiya sannan ya ce, “Ya kuke da waccen ne?”

Na ce masa, “Hasana ta ce.”

Ya ce, “Ban yadda ba, amma dai ko ma ya kuke, ki yi hankali da ita.”

Ji na yi gabana ya faɗi, nan na caccaɓa masa magana na yi gaba, saboda ya ɓata min rai, kawai son gulma da son munafurci ka zo kana faɗa min wannan maganar, a raina na ce da ka san wace takwara da ba ka daɗi haka ba, ita ɗin wani ginshiƙi ne cikin rayuwata.

Ko da na tad da ita cewa ta yi, “Me ya ce miki?”

Na ce mata, “kwatancen gida na yi masa, sai lambar waya na ba shi taki.”

Mun shiga farfajiyar gidanmu lokacin da ana faɗa mata don haka ta kawo min dukan wasa ta ce, “Ko ya zo ba zan fita ba muguwa kawai”

Ni dai na yi dariya kawai, samun ya Habib ya fiye min komai a rayuwa, na kasa dena godewa Allah akan kyautar da ya yi min, ban taɓa jin son wani mahaluƙi ba a rayuwata sama da shi ba, dama ni ba mai tara samari ba ce.

Kafin ta fita sai ga su Ummee sun shigo, suka gaisa sama-sama sananne ta tafi mu kuma muka shiga gida.

Sun gaishe da Aunty Lami cikin girmamawa wanda a da baya tsaf za su iya ganinta su wuce saboda hudubar mahaifiyarsu. Bayan sun fita ne Mama take fadawa Anty abin alheri, Ummee ta samu admission sannna saurayin da yake zuwa wurinta zai turo iyayensa a ya yi magana, sosai Anty ta yi murna, ni kaina na ji daɗi sosai, a raina nake cewa shi kenan sai a haɗa aurenmu. A lokacin ina matuƙar son aure saboda ban san meye aure ba, a baki na san shi, amma ina ganin aure ne kadai zai ban damar sake haɗa fuska da mahaifiyata, aure ne zai bani damar sake sabuwar alaƙa tsakani na da mahaifiyata, wannan ya sa nake ɓoye burina na yin karatu, duk da ina fatan cimma shi.

Ledar tsaraba Anty ta miƙa musu, su ma dai mayafai ne da kayan kwalliya, sosai mama ta yi ta godiya, su ma suka yi wa Anty godiya, abin mamaki yau mama har da tambaya ta ko zan ci abinci, na ce mata “alhamdulillah a ƙoshe nake.”

Ana daf da kiran magrib Abba ya shigo, muka yi masa asannu da zuwa, “Mutanen hotoro ne yau a gidan.”

Da fara’ata na ce masa, “E Abba, sannu da dawowa.”

Anty ta fito daga ɗakin Mama tana gaishe shi, ya ce,

“Ashe tare kuka gabaɗaya.”

Anty ta ce, “E wallahi.”

Ya ce, “To madalla, bari na yi sallah, dama ina da niyyar zuwa can gidan naki ai.”

Aunty ta ce, “Ai da mun sani sai mu bari sai ka zo sai mu zo.”

Ya ce, “A’a gwara da kuka zo, kun hutar da ni ai.”

Alwala Abba ya yi ya fita masallaci, alwalar muka yi mu ma duk da dai ni ba sallah zan yi ba amma dai ba na barin alwala ta wuce ni, saboda muhimmancin ta, idan mace na jinin Haila yana da kyau ta yawaita yin alwala saboda samun kariya daga shaidanu.

Ɗakina na buɗe wanda tun bayan tafiyata ban ƙara shiga ba sai yau, don ban zo gidan bako sau ɗaya sai wannan rana, muka shiga yana nan a shirye tsaf da shi yadda na bar shi, sai dai ƙura kaɗan, ita ma saboda yanayin sanyin da ake yi ne ya sa, ga hazo kuma, karkaɗe darduma na yi na sake shimfiɗa ta a ƙasa, sallah suka yi har da su Ummee duk a nan suka yi sallah, wanda a dako kallon ƙofar dakin ba sa yi bare su shigo.

Bayan sun idar ne Ummee take cewa, “Yaya kin yi zamanki a can abinki.”

Dariya na yi na ce, “Zan dawo in Sha Allah.”

Haneefa ma na idarwa ta ce, “Yaya ni har na cire rai gani nake kamar kin koma can gabaɗaya, duk ba ma jin daɗi ba kya nan.”

Dariya kawai nake ina kuma mamakinsu, yaran da ko kallo ban ishe su ba a baya, amma wai su ne suke fatan na dawo.

Cewa na yi musu, “Zan dawo nan ba da jimawa ba.”

Miƙo min waya Ummee ta yi ta ce, “Kinga Nasir ne ya kawo min.”

Na karɓa fuska ta cike da murmushi, wayar ta yi kyau sosai, na ce, “Ummee wayar nan ta yi kyau sosai wallahi, amma ki kula da ita, kuma ban da ba ƙawaye, domin waya sirri ce.”

Ta ce, “Haka ma mama ta ce min.”

Na ce “Yauwa ki kiyaye.”

Kallo ta saka mana a cikin wayar, wani Hausa Film mai suna Jaruma.”

Muna tsaka da kallon Abba ya dawo daga masallaci, shi da dady suka shigo har parlon Abba, kiran Haneefa ya yi ta kai musu abinci, bayan ta kai komai ya ce ta kirawo Anty Lami.

Suna ɗaki su duka suna hira, sai ya sake kiran Haneefa, da ta dawo daga kiran ne ta ce nima na je Abba na kira na.

Tashi na yi cike da kunya, na san dai maganar ba za ta wuce ta Habib ba, ko da na shiga ɗakin zaune na tadda su kan kujera, na je na zauna kasa daga gefen Anty, na gaishe su sannan na ce “Abba ga ni.”

Ya yi gyaran murya ya ce, “Yanzu iyayenki suke min maganar abin alheri, na ji daɗin hakan, Allah ya sa abokin haɗin ki ne ya kuma sa muku albarka har ƙarshen rayuwarmu. Ni dai na amince, Lami ta faɗa min kina son sa, Allah ya baku nasara.” Daga nan ya ce Na tashi na je, ina ji kan na ƙara sa fita daga ɗakin Anty ta ce, “Sai kuma roƙo na biyu Yaya, ina so ta koma makaranta.”

“Kayya Abba ya faɗa.”

Take na ji gabana ya faɗi, a gaskiya ina son karatu, don zan iya hakura da duk wani abu na rungume karatu na na san da izinin Allah zan samu mafita don ba a ilimi a tashi a banza.

Abba ya tauye ni ta ɓangarori da dama, na kuma yi masa haƙuri amma tauye wannan ɓangare daidai yake da dakushe min rayuwata.

Komawa ɗaki na yi jiki a sanyaye, bana fahimtar kallon ma da suke yi na dai yi shiru, zuciyata cike da ɓacin rai, na rasa me ya sa Abba yake min haka a rayuwata.

Ban san ya suka karke ba, ina dai zaune ina jiran tsammani, a hirar da su Fatima suke yi ne na gane butulci aka yi a Film ɗin.

Sai wurin goma saura muka isa gida, hakan ya ban damar hayewa sama ba tare da na haɗu da ya Habib ba, wanka na yi na yi brushing na fito, ba kowa a ɗakin sai Abdul kwance tun a gidanmu ya yi bacci, rigar bacci na saka na daura zani a kai na saka hijab na kwanta, gabadaya na gaji, ga damuwar ban san ya Anty suka yi da Abbanmu ba, ga rashin ya Habib take abin da na yi amsa ɗazu ya faɗo min, sai nake ji kamar ban kyauta ba, kamar ban fahimci shi ba, kamar na yi hanzari, a yadda yake nuna min so bai kamata na yi amsa abin da na masa, kawai ji na yi hawaye na silalowa daga cikin idanuwa na.

Ina kwance suka shigo don ba bacci nake ba, ina ji suna zancen ya Habib ba lafiya ai ban ana sanda na tashi zaune ba ina tambayarsu me ya same shi.

Nana ta ce,. “Zazzaɓi ne da ciwon kai.”

Fatima ta ce, “Mama na kiranki.”

Wata faduwar gaba na ji, sai na mike kawai na zura takalmi na sauka ƙasa, suna falo a zaune dady na shan coffee, Anty ta ce, “Don Allah halima dafawa Habib shayi ki kai masa, ba shi da lafiya yana ɗakinsa.” Tana maganar tana hamma da alamu bacci take ji ita ma.

Fitowa na yi na haɗa duk abin da ta ce na wuce ɗakinsa, knocking na fara bai buɗe ba don haka na tura ƙofar na shiga da sallama, shiru ba motsin kowa a parlon nasa, sai na wuce bedroom din Ina sallama nan ma dai shiru ba’a amsa ba, switch na lalubo a hankali na kunna fitilar ɗakin, take haske ya gauraye ko ina na ɗakin, idanuna suka sauka kan gadon, kwance na gan shi ƙudundune cikin bargo ya rufe har kansa, ajiye tray din shayin nayi kan table na ƙarasa inda yake na fara bubbuga filon ina kiran sunansa a hankali “Ya Habib.”

Buɗe idanunsa ya yi, sun kada ja jawur da su, jijiyoyin kansa duk sun tashi, duk da wannan halin da yake ciki a hasale ya tashi zaune cikin raunananniyar murya ya ce, “Me kika zo yi min a ɗaki.”

Kukan da nake rikewa ya kwace min na ce, “Shayin na kawo maka.”

Ɓata fuska ya yi ce, “Fita da shi ba na so, ni Fatima na ce ta kawo min ba ke ba, idan ba za ta kawo ba ba na son naki.”

Kuka nake mara sauti tare da ba shi hakuri, ya kalle ni, “Ni za ki mara Leemat, ni masoyinki.” Ya yi ƙwafa sannan ya ci gaba da magana a hankali, “Don kawai na rike hannunki, mu fa ƴan uwa ne, kuma aurenki zan yi kin kuma sani, to meye a ciki, yau ko kanki na ce ki ba ni kya saka hannu ki mare ni, ba ki duba girma na da girman son da nake miki ba, meye don na taba ki? Faɗa min, wannan amsar kawai nake son ji, idan babu kuma ki dauki shayinki ki fice min na daina ganinki ina jin zafi a cikin raina.”

Magana na fara yi cikin kukan na ce , “Ya Habib ni ba muharramarka ba ce, kuma abin nan ka sani ba kyau, idan ka fasa aure na ya zan yi.”

Murmushin takaici ya yi ya ce, “Shi kenan tashi ki fita min a ɗaki.”

Hakuri na ringa ba shi, ina jin tsoro ina gudun ɓacin ransa, ya ki hakura sai ma cewa da yake, “An faɗa miki ni mayaudari ne, ko kin taɓa ganin na zo kusa da ke ba sai da maganar aure ta shiga tsakaninmu ba, tashi ki fita.” A lokacin ya miƙe tsaye daga kwancen da yake da, ganin yana ta masifa ga shi da gani jikinsa ba ƙwari ya sa na tashi na shige jikinsa ba tare da tunanin komai ba, umarni ne daga zuciyata, na ƙanƙame shi ina kuka, kamar jira yake ya saka hannu ya zagaye ni tare da manna ni a jikinsa tantsan. Sai sauke ajiyar zuciya yake, zuciyarsa na bugawa da sauri.

Karkarwar da jikina yake yasa muka zauna bakin gado, tuni ya cire min hijabin jikina ya shiga shafa sassan jikin nawa, ban aune ba na ji hannunsa saman kirjina, ga shi ba ko bra a jikina.

Wani abu nake ji yana yawo a jikin nawa, da sauri na tashi tsaye, na ɗauki hijabina na saka, na ce masa, “Zan tafi sai da safe.”

Kallo na yake yana wani shu’umin murmushi, ban jira ya yi magana ba na fice daga ɗakin.

<< Halimatus Sa’adiya 6Halimatus Sa’adiya 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×