Alhamdulillah! Zaman da na yi a gidan Aunty Lami sai ya kasance min tamkar shan maganin wasu daga cikin matsalolina ne, zama ne wanda ba rashin ci da sha a tare da ni, ina samun kulawa yadda ya kamata daga Aunty, mijinta da ƴaƴanta da sauran jama’ar gidan.
Mutane da dama na faɗin maganganu marasa daɗi game da dangin uba wanda kusan haka ne, amma a nawa bangaren sai nake ganin kamar da sauƙi, ko da yake masu iya magana sun ce ruwan da ya dake ka shi ne ruwa, amma sai na ga da banbanci sosai a wuri na, wannan ya sa duk inda zan shiga sai inuwar Aunty Lami ta min rumfa, kowane mataki na taka za ka samu gurbin kyautatawarta a gare ni ya mamaye, ita ta maye min gurbin Amma a rayuwata.
Sannu a hankali na soma samun sauƙi, ranar da za a cire ɗaurin ƙafar ban ji zafi ba, da duk zato na zan ji zafi kamar sanda aka naɗe wurin da farko.
*****
Asalinsu daddy Auwal ƴan Katsina ne, aiki ya kai babansu Kaduna, sanadin Uncle daddy Auwal ya haɗu da Aunty Lami suka ƙulla alaƙa har ta kai su ga yin aure, shi ma likita ne, bayan gudanar da bincike har garin Katsina aka je, suna da asali mai kyau, asali mai kyau kuwa shi ne aure.
Bayan auren suka fara zama a Kaduna, daga nan kuma aiki ya dawo da Daddy Auwal Kano, suka tattara suka dawo nan da zama.
*****
Ranar wata Alhamis da Yamma, a lokacin na warke gaba ɗaya, ban dai koma gida ba muka yi baƙo, ba kowa ba ne illa Habib ƙanin Daddy Auwal ne, da yake ina kitchen kuma ta nan zai wuce ya shiga babban falon gidan shi ya sa muka haɗu, duk da dai ban cika son mu hadu ba saboda kallo ne da shi kamar wani tsohon maye.
Gaishe shi na yi bayan ya shigo yana sana’ar tasa ta kallo.
Ya ce “Ah! Halima kina nan kenan?”
Nace masa “Eh!”
Ya ce,
“Da kyau, ya mutan gida?”
Na ce masa,
“Duk suna nan ƙalau.”
Kallo na yake yi ba kamar yadda muka saba da shi ba da, don kallo yanzu ya ninka wanda yake min a da baya, sai duk na ji na takura, ganin ba shi da niyyar shigewa sai na shige daya falon na bar shi nan tsaye.
Ina tsaye jikin labule ya shiga babban falo, nan ya tadda Aunty Lami da dady a zaune.
Sun jima suna tattaunawa ban dai san akan meye ba, ina kitchen muna girki da Nana da mai aikin gidan, fitowa Aunty ta yi ta ce da mai aikin,
“Ki haɗa wa Habib tea sai ki ba Nana ta kai masa.”
Tana faɗar haka ta yi saman bene, ita kuma ta ɗora masa shayin a kettle, cikin raina na ce, “Ɗan takura fa ya zo.”
Nana ce ta kai masa kamar yadda Aunty ta umarta, bayan ta kai ne ya ce a soya masa ƙwai amma ni yake so na soya masa, tsaki na ja cikin raina na ci gaba da mita “Da ya san yana son kwan amma bai ce a soya masa ba dan iyayi.”
Ganin magriba na ƙaratowa ya sa na hanzarta na soya masa, Nana ta kai sama, Atine kuma ta fita ta tace shinkafa, don haka na juye na yi a plate na ɗauka da kaina na shiga falo da sallama, yana zaune yana shan shayin ya amsa min idanunsa ƙuri a kaina, ce masa na yi,
“Ga shi.”
Ya ce “Yauwa, sannunki.”
Na ce “Yauwa.”
*****
Toh tun daga wannan rana ya kasance Habib na yawan zuwa gidan, kuma in dai ya zo sai ya kirawo ni mu yi hira, tun ba na sakin jiki da shi, har dai na fara sabawa, har ta kai idan ya yi sati bai zo ba sai na ji ba daɗi.
Akwai wani lokaci da ya tafi Kaduna, akai rashin sa’a ya yi accident, ranar na shiga tashin hankali, a halin da nake ciki zan iya cewa ko matarsa ba ta kaini shiga damuwa ba, don da aka kira ta a waya aka faɗa mata ta taho gidan Aunty Lami a tafi da ita gano jikinsa da yake can asibitin Zariya aka kai su bayan faruwar hatsarin, sai da ta ɓata lokaci, ganin ina Farawa ina Hotoro ya sa Aunty ta tambaye ta.
“Ke kuwa Maryam zaman me kika tsaya yi an faɗa miki abu ne na ujula, amma kika daɗe haka?”
Buɗar bakin matar nan sai cewa ta yi.
“Wanka na tsaya yi, na yi wa Hafsa, kuma lokacin da aka yi min wayar ma girki nake yi, shi ya sa na tsaya na gama na ci sannan na taho, kuma ma ai an ce bai ji ciwo ba buguwa ce kawai.”
Tsaye nake a lokacin, hannuwana tallafe da haɓa ta na yi tagumi kamar wata wadda ubanta ya mutu, idanu na jawur da su, na ci kuka na gode Allah, kallon Aunty Maryam kawai nake, tun daga kan shigar da ta yi, da kuma kwalliyar da take fuskarta sai haushin maganar da take ya fi komai ɓata min rai, ƙululun baƙin ciki ya tokare mini ƙirji, Anty kuwa dan takaici ba ta sake cewa komai ba, ciki na shige don ba na son ganin ɗagawar motarsu, dama kuma mun yi sallama, na yi musu fatan Allah ya kiyaye hanya.
Ina jin ƙarar tashin motar, hawayen da nake riƙewa cikin idanuwa na ya silalo kan kumatu na, cewa na yi a fili, “Allah ka tashi kafaɗun bawanka.”
Kwanciya na yi kan katifa, Nana ta zo gefe na ta zauna, Fatima na tsaye jikin windown ɗakin, Abdul kuwa yana wurin Atine da take ta faman gyara ɗakunan ƙasa.
Katse mana shirun na yi da cewa,
“Fatima kin ci abinci kuwa?”
Ta ce,
“E, na ci.”
Na dafa kan Nana da ke kwance jikina na ce,
“My Nana kin ci abinci?”
Ta ce “E na ci.”
Sai lokacin na tuna tun shayin safe fa ban ci komai ba, da rana ma wata ragowar shawarma na samu a frigde na dumama na ci, ashe rashin daɗin da nake ji wannan abin ne zai faru, Allah kenan.
“Allah ka bawa ya Habib Lafiya.”
Jin sun haɗa baki sun ce “Amin.” Ya sa na san maganar ɓoye ce ta fito fili.
Ban tashi ƙara shiga tashin hankali ba sai da dare ya yi, yau ni kaɗai a gida sai yara, Atine na ɗakinta, kuka na ringa yi bayan su Fatima sun yi bacci, agogo na duba na ga ƙarfe ɗaya saura na dare, ganin ba bacci nake ji ba na tashi na shiga toilet don yin alwala, bayan na fito na tada sallah, sai da na yi addu’a bayan na idar na shafa, na kwanta.
Da safe da wuri muka tashi, wanka da alwala na sa yaran suka yi, sannan suka yi shirin makaranta.
Ni kaɗai na shiga kitchen na haɗa musu breakfast nan da nan na gama, tea suka sha kowa ta ɗauki abincinta suka fice, dama driver na jiransu a waje.
Bayan fitarsu kuwa wanka na yi na karya, shayin ne dai, ko burodi ban ci ba, na koma na kwanta, Atine ce ta gyara gidan gabadaya, sai karfe shabiyu da rabi na rana na tashi a gajiye kamar an yi min duka, haka na miƙe na saka hula a kaina na sakko ƙasa, nan na samu Atine na gyaran kayan miya, gaisawa muka yi sannan na samu wuri na zauna na ce,
“Atine ba ku yi waya ba?”
Ta ce,
“Wallahi ba su kira ba har yanzu.”
Abincin rana muka ɗora duk da cewa masu gidan ba sa nan, ƙarfe biyu mun haɗa, jellop rice ce sai hanta, na so haɗa salad amma raina ba daɗi, sai na haƙuri.
“Halima kin iya girki, ji yadda abincin nan yake ta ƙamshi, komai naki a nutse kike yi, yadda kike tsaftace kayan aikin yana ban sha’awa ke dai mijinki ya huta.”
Dariya na yi ina jin daɗin yadda take yaba min na ce,
“Wai har na iya abinci haka?”
Ta ce,
“Sosai kuwa.”
Na ce,
“Na gode Atine.”
Da yake mu kaɗai ne sai na kwashe abincin a kula, na bar shi a kitchen ɗin, ɗaki na koma na yi sallah, Atine ma haka, muna nan zaune na kunna Tv muna kallo sai ga su Fatima sun dawo, taro su na yi suna ta murnar dawowa, Nana na ce wa,
“Yaya kin yi kyau, wa ya yi miki kwalliya?”
Dariya na mata na ce,
“Ni na yi da kaina.”
Fatima da ke zaune kan kujera tana cire socks ta ce,
“Nana akwai surutu, sai kin gaji da ita Yaya.”
Na ce,
“Inaaa! Ai ba zan gaji da my Nana ba, ko kin manta sunan Amma na ne?”
Kwatsam Fatima ta jefo min da tambayar da a kullum na yi wa kaina ita sai na yi kuka,
“Yaya wai ina Ammanki take? Ban taɓa ganinta ba.”
Abdul da ke jingine da jikina na kuma riƙewa, take bugun zuciya ta ya canja, idanuwa na suka cika da ƙwalla, duk yadda na so adanasu sai da suka bani kunya suka silmiyo saman kuncina, take kuma zafin da nake ji na rashin lafiyar ya Habib ya kuma taso min, hannuwana na sanya na goge fuskata da ta yi jawur, na ce da ita,
“Nima ban san ta ba Fatima.”
“Ta rasu ne?”
Ta ƙara jifa na da wata tsattsaurar tambaya, mai wuyar amsawa, da ace ina da wannan amsar da tabbas sai na ba wa Fatima ita, amma ba yadda na iya haka na yi shiru ban amsa mata ba, kuka na ci gaba da yi.
Sai cewa ta yi,
“Yi hakuri Yaya, ban san ta rasu ba da ban tambaye ki ba, don Allah ki daina kuka.”
Ko ba komai Allah ya cece ni don ba ni da amsar da zan iya ba ta, shirun ya yi min amfani.
Kayan da suka cire na adana, na sa su suka yi wanka, muka koma kasa muka ci abinci, shirin islamiyya suka yi suka fice.
Sai magrib suka dawo, bayan mun yi sallar suka ɗakko littattafansu don yin homework na taimakawa Abdul ya yi na sa.
Abinci muka ci daga ƙarshe muka yi sallah isha’i, muka yi wa Atine sallama, muka hau sama, shirin bacci kowa ya yi, ni da Abdul katifa ɗaya muke Fatima da Nana a katifa ɗaya.