Skip to content
Part 1 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

A duk sanda naci karo da wata kalma da ta danganci rayuwa gabana kan fadi in tsinci kaina cikin wani matsayi na tsoro da razana, wani lokaci ma in ji na samu kaina cikin halin da zuciyata kan samu kanta cikin yanayi na kaikawo saboda tunawa da al’amuran da suka shafi jiyana da yau dina, in suke jin wani mummunan faduwar gaban idan na tunan ba ni da tabbatas ko masu niya bisa gobena.

A mafi yawancin lokaci kuma in har nayi irin wannan tunanin to nakan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sanya mana wani tabbataccen al’amari ba in dai cikin wannan rayuwar tamu ne ta wannan dunyar, duk abinda ka gani zai wuce.

Farin ciki ko bakin ciki yana da lokaci, komai yayi farko wata rana zai yi karshe. Wani Karin maganar ma sai ya ce abin da ya baka tsoro a yau babu mamaki gobe ya baka tausayi, wasu ma da suka yi wa rayuwa irin fahimtar da suka yiwa rayuwar irin fahimtar da suka yi mata sai suka ce wai ita din tamfar hawainiya ta ke, ta kan iya canza launinta a kowane lokaci.

Al’amuran da na gani a shekaruna na kuruciya sun sanya ni son bayar da labarina ga na kasa dani ba don wani labarin dadin bayarwa ke gare shi ba, a’a sai dai don ya zamo hannunka mai sanda a gare su. Ya zamo musu wani darasi da za su rika don su kauce daga aikata kura-kurai irin na kuruciya kura-kurai da kan zamo tanfar na tsalle daya mai jefa mai shi rijiya.

Wannan labari da nake nufin bayarwa a yau labari ne da ya danganci halin da rayuwata ta kasance shekaru talatin baya da suka wuce a lokacin da na ke da shekaru tara kacal a duniya.

Ni Maryam Abubakar, na taso ne a gidanmu gaban iyayena uwa da uba cikin gata kulawa da kuma tarbiya, a wancan lokacin da nake magana a kai iyayena uwa da uba suna matukar sona musamman ma Babana wanda Sunan Mahaifiyarshi ke gare ni bisa hakanne  bai fadin sunan nawa sai yake kirana da kalma ta Yacuwuna’ kalmar da ke nufin mahaifiya ko uwa cikin harshen barbarci.

Wani dalilin da ya kara tsananin soyayyarshi gare ni ko in ce mu, ni da Yayata Khadija wacce take ta girme ni da yawa, don a lokacin da nake da shekaru taranne a ka yi bukinta da wani saurayinta da suka so juna tun suna ‘yan yara, Ibrahim shi ne din bai da kowa sai mu, bai da dangi ko kuma in ce ya dade rabonshi da yayi mu’amalla da su ba ya ma maganarsu.

Nasha jin Innata a wancan lokacin tana ce mishi Mallam ko ba don mu ba kai ni wurin ‘yan uwannan namu in gano su saboda yaran nan su gansu su san iyayensu da danginsu saboda in mu ne yau ba mu ne gobe ba, su kuwa dangi musamman na uba ko don maganin gori a neme su.

A mafi yawancin lokaci ta kan yi irin wadannan maganganunne har ta gama ba tare da ya tanka mata ko ya ce mata uffan ba. Sai dai wannan bayani da nayi a kan Babana bai hana shi zamowa daga cikin mutanen kirki ba, mutum ne mai tsananin hakuri mai gudun bacin ran wani, mai girmama makwabci wanda ba ya shiga harkar da ba tashi ba, ba mai yawan magana ba ne mafi yawancin lokaci hirarshi takan yi nisa ne kawai da makwabcinshi Mallam Hodijo wanda suka zama tanfar yan uwa shi da shi ga shi kuma sai aka yi dace Babana Babarbare ne wanda ko zanen da ke fuskarshi ya isa ya bayyanar da asalinshi.

Haka shima Mallam Hodijo Bafulatani ne da bai bukatar sai an tsaya bayani a kan shi, don haka sai abin nasu ya kara zamowa gwanin sha’awa kullum a cikin zolayar junansu suke suna raha tare da barkwancin wasan fulani da Barebari, haka kuma alaka take tsakanin Innata da matar Mallam Hodijo mai suna sumaye.

Wani dalilin da ya karawa Babana sonmu ni da ‘yar uwar tawa shine, kasancewar matarshi mata mai wabin ‘ya’ya cikin haihuwa bakwai da aka yi ne aka samu mu biyun muka rayu.

Rashin sanin dangin Babana ko rashin mu’amallar da su bai hana gidanmu zamo wa gidana Jama’a ba Innata mai ‘yan uwa ce ban da haka kuma mata ce da ta iya mu’amalla da mutane da ke kuma iyakacin kokarinta wajen kiyaye hakkin makwabtanta.

Ita din kuma mata ce da yawan mu’amallarta da ‘ya’yan da ba nata ba, ya zamo dalilin da ta zamo uwar yara da yawa maza kuma da mata kanana da kuma ‘yan samari.

Gwanar kitson ce da kuma lalle bata laima da kwiya kan hakan sannan bata taba damuwa dayi don a biya ta ba, don haka kullum ta zaunar da ni da nufin yi min kitso ko lalle to zata hada ne da duk yaran da muke wasa da su a wannan lokacin tayi mana kitso da lallen tare da wannan dalili sai tayi sabo da iyaye da yawa na yaran da take yi mana kitson nan ko lallen tare wasu daga uwa godiya bayan sun aiko mata da abin hasafi ta mayar su biyo baya.

Wasu yaran da ta zamo uwa gare su kuma musamman yan mazan daga yawan ciyarwarta ne tana ganin yaro cikin wani zata zaunar da shi ta zuba mishi abinci in har ya yarda yaci zata gaya mishi gobe ma kazo daga haka har sai zuwa wurin nata ya zame mishi jiki ko kuma dabi’a, don haka a ko ina yara suka ga Inna za ka ji suna Mama’ Mama ina za ki? Mama kin dawo?

Mama kin ga wane ko? Hatta wasu iyayen yaran da suka san Inna uwa ce a wurin ‘ya’yansu, za ka ji suna gaya mata laifin yaran nasu don nufin ta taya su yi musu fada kan laifuffukan nasu ko kuma kin da suke yi wa makaranta.

Cikin yaran da Inna ke yin mu’amallah mai karfi da su akwai Mubarak da Mansur wadanda su ba suna zuwa wurinta don cin tuwonta bane a’a sukam ma yan gata ne a gidajensu musamman Mubarak wanda shi shi kadai ne da namiji a gidansu a wurin kuma ubanshi Alhaji Mühammadu wanda a unguwar tamu duka babu maigidan da ya kai nashi girma da kuma kyau.

To haka shima Mansur ko da suke da yawa a gidansu gidan nasu na rufin asiri ne, su suna zuwa wurin Inna ne kawai saboda gidannata ya zamo wurin zuwan yaran unguwar har kuma sai ka ji suna tambayarta Mama da wani abu ne mai dan dumi in akwai ta ce akwai in babu ta ce sai garin rogo, wani lokacin ma har sai ka ji tana yi musu fada kan abin da tasan suna yi musamman Mubarak, kusan kullum ya shigo za ka ji tana tambayarshi kaje Makarantar ko yau ma ba ka je ba? In yaje ya ce yaje in bai je ba ya dan tsuke fuska yana yi mata bayani Mama ke ba za ki gane ba ne? ta ce Eh, ba zan gane ba in ba ka gaya min damuwarka ba amma in har za ka bude baki ka gaya min ai zan fahimci daidai gwargwado, tayi mishi nasiha.

lyayena ba masu hali ba ne, amma a cikin rufin asiri muke rayuwarmu, sana’ar Babana sana’a ce ta rufin asii, kayañ miya yake sayarwa a saman layinmu ba shi da tsawwalawa kan  kayanshi, don haka wurin nashi matattara ce ta cinikin yara.

Mallam ban tumatir, Mallam ban attarugu, Mallam ban alayyaho, aikin ke nan. Don naka inhar ban je Makaranta ko gidan Yaya Dijah ba to yawanci na kan je wurinshi ne in rinka taya shi in yana bada kaya in rinka karbar mishi kudi saboda wasu yaran da tarbiya bata ishe su ba sukan karbi kayan miyan su tafi ba tare da sun ba shi kudin ba saboda ganin hankalinsi ya tafi wajen masu kokarin ya ba su nasu.

Babana ba mutum ba ne mai dogon buri ko mako game da kudi, don hakan kullum ya dawo daga kasuwarshi ya kan tattara duk cinikin nashi ne ya mika mata ko kuma ni ya miko min in shirya su in je in ajiye su a inda nasan tana adana kudi.

Shi kuma ba mai yawan sa ido kan abubuwa ba ne, balle ka ji shi yana kididdiga ko tuhuma, don haka kusan komai Inna ce take tafiyarwa tana ganin wani rami a çikin gidanmu za ka ji ta kira wani daga cikin samarin da suke shigowa wurinta ta basu kudi ta ce maza su siyo siminti ka toshe mnin wannan wurin.

In kwata ce take nema ia cika zata sa su nemo mai kwasheta ya gyara suyi ciniki ya kwashe ta basu kudin suje su biya haka nan rufin kwano in ta hango alamar zuwan damina zata basu kudin foti su sayo su nemo mata mai hawa kwanon ya kara bin kusoshi da fotin din maganin yoyo.

Haka nan kuma ko wata hidima ce ta taso bata jiran Babana sai dai ta ce mishi an yi kaza an yi kaza ko da kuwa ta sallah ce ko azumi ya ce mata to, ko da kuwa a kan shi ne zata yi tayi mishi tuni musamman da sallah, Mallam in fa baka sayi yadi ka bada dinkinka yanzu ba zaka rasa dinki, ya ce mata to don na rasa dinki menene tunda dai ke da yaran kun samu ai shi ke nan.

Ta yi murmushi ta ce, Haba Mallam ana hidimar sallah ai zan so nima in ga mijina fes in kara jin dadi da yiwa Ubangiji godiya, yayi kamar bai ji ta ba. Inna da makwabciyarta Babah Sumaye wani irin zama suke yi da yafi na ‘yan uwan da babu fahimta da kauna ta zumunci a tsakaninsu dadi.

Kusan kullum sai wata fa shigo wurin wata duk abin da suka girka sai sun aikewa juna, wata rana ma ka ji daya tana cewa dayar in za ki yi girki kiyi tare da nan gidan, don kasala nake ji ko kuma aiki zai yi min yawa-za a yi abu kaza da kaza su ce to.

To haka Babana yake da mallam Hodijo ko’ina za su suna tare ko da kuwa Masallaci ne kullum kuma naje karbo cefanen gidanmu, to nakan hado ne da na gidan su Babah Sumaye. Innata ba wata jaruma ba ce in dai a ka neman kudi ne bata da wata sana’a da take yi ta maida taro ya zama sisi nima tana cikin wadata saboda halin mijinta na komai nashi a wurinta yake ajiye shi bai da kuma matsala don ta ce mishi ta kashe kaza kan abu kaza na hidima da ya taso haka nan ita din gwana ce kwarai ta shirya abinci mai dadi aci shima Baban nawa mai son cin dadin ne.

Sannan ta iya zama da shi ta iya tarairayarshi da tattalinshi duk da shi ba mai yawan magana ba ne, ko yawan dariya amma in suna tare shi da ita fuskarshi bata rabo da murnmushi, bini-bini kuma za ka ji shi yana yawan ambaton sunanta Ramatu.

Gidanmu karamin gida ne dan madaidaici, dakuna hudu ne a ciki, ciki da falo guda daya wanda ni da Inna muke ciki, sai daidai guda biyu, daya Babana daya kuma tarkace na kwandunan tumatir din Babana da sauran kayayyakin Inna na aiki, kullum ka shigo gidanmu daga zauren gidan ka ke soma shakar kamshin turaren Innata.

Ana cikin hakanne aka wayi gari a gidan namu Inna tana wani irin rashin lafiya da Babana yayi ta zarya yayi ta zirga-zirga da dawainiya mai yawa a kai, cikin wani irin farin ciki da zumudi mai yawa.

Haka nan itama Babah Sumaye tayi ta hidima aikin gidanmu gaba daya ya zama nata, ta rinka kai kawo tana ta faman murna ashe, ashe wai Innar tawa wani cikin ne da ita, ni kam nayi farin ciki saboda ganin zan samu kani watakila mace watakila namiji, wanda dama nasan Babana yana son samun shi.

Sai dai kuma gabana ya fadi da na tuna da irin haihuwar da Innan tayi shekara guda da ya wuce inda ta kubuta da kyar. Kankana, abarba, lemo da ayaba basa yankewa a gidanmu, saboda kullum sai Mallam Hodijo ya kawo ya ce a kawo mata saboda abin sana’arshi ke nan a bakin asibitin garinmu.

Haka a ka yi ta fama da ita har dai ta samu sauki ta wartsake ta koma kan al’amuranta.

Muna nan a haka har cikin Inna ya bayyana ya fito sosai, dama kuma ita din mai katon ciki ne ina jin ta rannan a hirar da suke yi tana gaya mishi ni dai ban taba jin ciki irin wannan ba Mallam, ko kuma don mutum ya fara girma ne yake jin hakan oho.

Yayi murmushi ya ce, “Ramatu ke nan, kina yar shekaru talatin da biyar kina gayawa kanki girma da kuma ni ne nayi kuskuren ba ki nace miki kin girma da kin ce.na hango wata yarinyar ne a waje yáa sani kiranki tsohuwa.”

Tayi murmushi ta ce, “Uhun! Mallam ke nan, to tunda a ka yi auren yarinyar nan kuwa har gata yanzu da juna biyu ai dole in kirawa kaina girma ni da kaina.”

Ya tayata murmushin kafin ya sake kallonta cikin natsuwa ya ce mata, ai ba Dija ce mizanin da za ki rinka dubawa wajen gane girmanki ba, ni za ki rinka dubawa ai ni ne ma’aurinki ya ya ki ke a wurina? Shi ne maganarki, yaya nake kallonki? Shi ya kamata ya zama abin lurarki, to in kuwa ni ne ban taba kallonki na gane canzawarki ko bambancin da ke tsakaninki a yau da na ranar da mahaifinki ya kira ni ya ce min in dawo da yamma inga ‘yar da yake da ita in tayi min in kawo sadaki a daura min aure da ita babu wata rana da nake wayar gari ko zan wayi gari ban yi wa wannan mutumin kirki addu’a ba Ramatu.”

Ta kalle shi ta dan yi murmushi ta ce, Uhun kai Mallam babu halin in kawo maka wata magana sai ka kawo wannan zancen ya ce, Eh ai bana gajiya da bada labarin ne saboda ya bani abin da ban taba tsammanin samu ba na karbi aurenki cikin tsananin tsoro saboda nayi zaton za ki bijire sai kuma ki ka zamo yarinya mai albarka mai ladabi da biyayya, mai sanin darajar iyaye da aurenki.

Halin Rayuwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×