Ni da kaina nasan na samu sassauci ba wai wani canji na samu a gidanmu ba, amma yar tsabtar da nake yi wa kaina tana yi min dadi tana kuma yi wa Yaya Dijah.
Har Yakumbo Halima ma da ta ganni sai da tayi min maganar, gashi kuma a yanzu ba sosai nake jin yunwa mai tsanani ba.
Saboda in dai Mubarak yana gida to ka’ida ne a wuni zai bani wani abinda zan ci mai dadi ko da kuwa sau daya ne.
Kwanaki hudu bayan wannan ranar sai ya kasance ranar ta Asabar ce ina gida da safe bayan na kammala ayyukana na dauko allona za ni Makaranta, sai kawai muka gamu da Mubarak yanzu ne lokacin zuwa Makaranta? Yayi min tambayar yana kallon agogon hannunshi.
Sai yanzu na gama ayyukana, na ba shi amsar a natse. Ki ka gama ki ka fito ba ki yi wanka ba? Sau nawa zan gaya miki wanka biyu ya kamata ki rinka yi?
Ban amsa mishi ba, to in dai Makarantar Baba Mallam za ki je bai fi saura minti talatin ba a tashi, don haka wuce muje ki gaida Ummata da nake ta fama da ke kina kakkaucewa.
A gidan su Mubarak kin yarda nayi in fara shiga dakinshi, kafin in shiga wurin Umman tashi, don haka muka rabu shi ya shiga wurinshi ni kuwa na wuce cikin gidansu wajen Umman tashi.
Tana ganina ta soma murmushi alamar taji dadin ganin nawa, Maryamun Mubarak. Na yi maza nasa hannayena duka biyu na rufe idanuna saboda kunyar yadda ta hada sunan nawa da nashi a wuri daya.
Kurarrajin sun warke ko? Na yi maza na ce mata eh, bata tambayi kwarkwatar ba sai ta ce ai gashi nan da gani an san kin samu saukinsu, don har jinin jikinki ya fara dawo miki, muga kan naki.
Na matsa kusa da ita na bude mata shi don ban jin kunyar bude shi a yanzu, babu shakka yayi kyau yayi tsaf, gashi ne da ke mai kyau sai rashin kulawa, ki kula da kanki kar ki jira sai an ce kiyi.
Kitso a kai a kai kin ji ko? na ce to Umma. Na maida dankwalina ina daure kan nawa, sai naji ta ce min, Yaya cikin naki dai? Mubarak ya ce min kwanan nan kina yawan ciwon ciki?
Na ce yayi sauki, na dauka karshen maganar kenan sai naji ta sake tambayata, kina ganin wani abu ne bayan kin yi ciwon cikin?
Da sauri na dago kai na kalleta cikin mummunar faduwar gaba nan take kuma na sake sunkuyar da kaina.
Na ce kina ganin wani abu ne bayan ciwon cikin yana fito miki ta jikinki? Kuka na kama yi mata kamar yadda dama kukan nayi tayi lokacin da na fara ganin nashi.
Ai ba abin kuka ba ne Maryamu, hali ne da dabi’a ta kowacce mace a kan haka a ka halicce mu, hakan kuma alama ne na girma.
Sai ki kara natsuwa ki kuma kara kama kanki kar ki yarda wani namiji ya kusanci jikinki daga yanzu kuma kar kina yarda lokacin sallah yana wuce ki ba ki yi ba.
Don ta hau kanki, haka nan Azumi in dai na ganin shi kuma za ki yi wanka tai tayi min bayanin yadda zan yi wankan, sai dai ban ji komai ba saboda kukan da nake yin ya tsananta.
Mubarak ya shigo ya same mu da Umma, bai tsaya ba ya juya ya fita saboda shigowar nashi bai sata ta daina maganar da take yi min ba.
Tashi ki share hawayenki ki wanke min wadancan kwanukan, sanya umarni na aiki a cikin maganar ya sanya ni hanzarin mikewa naje na kama aikin da ta sani, na gyara wurin fes na debo su na kawo mata, to ungo wannan gyara min shi, na ce To. Nasa hannu na karba na gyara shi na mika mata.
In ce ko uwar taki tana koya miki girki ne? Na ce a’a a gidan Yaya Dijah nake yi, Umma tayi maza ta ce iko sai Ubangiji, har na mance Dijah tana garin nan tana nan a nan inda muka kaita?
Na ce, eh Umma sai dai mijinta yayi nashi ne a can ciki suka koma, tayi addu’a kafin ta tambaye ni, ni yanzu ‘ya’yanta nawa ne? Na ce mata uku mata biyu namiji daya.
Hira sosai muka yi da Umma har ta gama abincinta ta zuba min nawa naci na koshi wanda tuwon shinkafa ne miyar shuwaka sannan na fita na koma gida.
Da yamma ina cikin gida Mubarak yazo yayi sallama da ni na fito na same shi a zaure, leda ya miko min nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya na juya cikin gida.
Dakinmu na fara shiga na zauna a kasa ina cicciro abubuwan da ke cikin ledar, kayan mai ne guda biyu da a ka rubuta 10.0.6 lotion a jiki da sabulanshi suma guda biyu, sai hoda da turare duka na 10.0.6 din ne.
Sai sabulan wanki da kwalin omo shima guda biyu, sai wata leda da ta bani sha’awa sai dai ban san meye a ciki ba, na shiga kokarin budewa don in gani.
Sai kawai Asabe da ke kwance a kan gado tayi maza ta fige tana fadin “Lahhh! Kan uba, lalle yau an kama ki wannan ai iskanci ne, ya sayo wannan ya kawo miki, da gudu ta fita ta kaiwa Babah Lantana ta barni nan a zaune jikina yana ta faman rawa saboda an ga abin iskanci a wurina. A to, ai ni kam dama na fada ai na gayawwa ubanta abinda suke yi bai kula zancen ba ne in ta dauko mishi cikin shege ai yasan abinda yake ciki.
In banda isklanci ace har abin jinin al’ada saya mata yake yi? Na sake tsorata, tsoro kuma mai tsanani. Maimakon in tuna na dade ina ganin Asabe tana yi in saki zuciyata sai na zauna nayi ta kuka.
Babana yana dawowa kuma Babah Lantana taje ta kai mishi audugar al’adar nan da Asabe ta dauke cikin sayayyata ta nuna mishi a matsayin huijar da zai gasgata maganar da take fadi, na’ cewar ni din lalacewa muke yi da Mubarak tunda har ga shi yasan ina al’ada yana saya min abin amfaninta.
Bakin ciki mai tsanani ne ya same ni, irin wanda ba zan iya kwatantawa ba, gayawa Babana da a ka yi na rinka ganin tanfar wani gagarumin laifi na aikata irin wanda ba a taba aikatawa ba a duniya.
Rannan Babana ya buge ni duka irin wanda ba a taba yi min ba a rayuwata, karo na farko kuma da ya taba taba jikina da sunan duka.
Sai dai ni kam ba azabar da na sha ne babban matsalata ba, irin kukan da na ganshi yana yi da hawayenshi.
Na samu kaina cikin kunci mai tsanani da bakin ciki, nayi dalilin da Babana ya zubar da hawayenshi a kaina, to ni kuwa ina zan shiga in tsoma rayuwata in ji dadi?
Da yake akwai al’ amarin kuruciya mai yawa a tare da ni, a lokacin sai na rinka jin tanfar eh da gaske ne iskancin da ake cewa nayin nayi shi tunda a ka ga wannan abin a wurina, donni a lokacin ban ma san asali menene a ke nufi da iskancin ba.
Tsawon lokaci ban sake yarda wani abu ya sake hada ni da Mubarak ba, ko da kuwa wane iri ne komai kuma kankantarshi, ko a waje ya hango ni ya soma kirana ko kokarin zuwa in da nake zan ruga da gudu in tafi in ba shi wuri.
Zauren gidanmu da kofar gidanmu kuma Babana ya hana shi zuwa, sai dai shima bai san dalilin faruwan hakan ba.
Ana cikin haka ne kuma muka rubuta jarrabawar mu ta gama aji biyu zamu tafi uku a tsawon wannan hudun babu abinda ya hada ni da Mubarak, bana ma ganinshi ko da kuwa a kofar gidansu ne in da wani lokaci yakan zauna tare da samari abokanshi.
Sai dai maimakon rabuwa da Mubarak din da nayi ya zama sanadi da zan samu wani sauki ko sassauci wurin Babana, tunda yayi min hukunci na yarda ya bani umarnin fita hanyarshi, na bi umarnin da ya bani ban samu sassaucin ba.
A gidan ma wani kuncin na sake shiga na koma zama cikin yunwa ga rashin abubuwan da da na daina nasa su. Asabe tayi matukar tasa ni a gaba babu halin in yi magana kan komai sai Babah Lantana ta ce, To ba taga tana jini ba.
Bakin ciki ya kama ni in mance da wanda nake ganin Asabe tana yi, kusan kullum sai tayi min duka, duka kuma irin na zalunci irin wanda babu mai ceto ko mai tambayar dalilin yinshi sai ta gaji kawai ta bar ni don kanta.
Rannan na dawo daga makarantar allo a lokacin nan an kai kusan watanni shida da faruwar abinda ya farun, sai kawai gani ga Umman Mubarak a hanya ta fito gaida mara lafiya a makwabta.
Rike baki tayi tana kallona, haba ke kuwa Maryamu, me yayi zafi haka da ba za ki shigo ki gaishe ni ba? Na sunkuyar da kaina cikin wani yanayi da ni kadai nasan abinda na shiga, in don Ahmad Mubarak ki ka daina zuwa wurina shi kamma ai ba ya nan…Da sauri na kalle ta sai dai ban san lokacin da na dago na kalletan ba, ta ce eh ya tafi hidimar kasarshi yana can Ibadan inda aka tura shi, dama yana kin tafiya Ibadan dinne yayi a nan kusa saboda ke, da kuwa kika biyewa sharrin da mutanen gidanku suka yi mishi nasa shi ya kama hanya yayi tafiyarshi.
Wuce muje gidan ai dama na dade ina neman in gan ki ko da kuwa a hanya ne ba mu gamu ba sai yau.
Kunya da nauyin Umma yasa na bita, to wai me yayi miki ne a ka ce yana yi miki iskanci? Shiru nayi na sunkuyar da kaina kasa na soma yin kuka.
Yana taba ki ne? Na yi maza na girgiza kaina alamar a a, sun gan shi ya rungume ki ne? sake girgiza kai nuna a’a, ya gaya miki wata magana ne suka ji? Na sake nuna a’a, to menene?
Ta tsare ni da tambayoyi, na kasa cewa komai har dai ta gaji tace duk mai yiwa dan wani sharri dai zai gani a kwaryarshi, tunda ni kam ai an ce ba a shaidar mutum amma ni zan yi wa Ahmad Mubarak shi ba mai irin wannan iya shegen ba ne, to yaushe ma ya kula wata da har a ka zo a ka samu ubanshi ana yi mishi togaciya a kanki?
Ga dambun zogale can nayi da za ni gaida mara lafiya, debo kici, na ce na koshi. Ta galla min harara tare da daka min tsawa, ke tafi ki debo bana son iya shege.
Na debo nazo na zauna ina ci ita kuma tana kara jaddada bacin ranta kan abinda a ka yi wa Mubarak, kewar Mubarak din nima ta kara kama ni, musamman da na gane ashe ma baya nan ne yasa na daina ganinshi.
Da hikima da jan hankali Umma ta shawo kaina har nayi mata bayanin sabon halin da nake ciki, ta ce uhun dama abinda take so ke nan ta raba ki da duk wani wanda zai taimake ki, in ba haka ba ita kuma Dija me tayi miki da aka ce ta kafa miki dokar zuwa gidanta ita ma?
Kai wannan uba naki? Ta dan yi shiru zuwa wani lokaci kafin ta sake cewa, to sai a hankali.
Kin ga in gari ya waye daina jiran abin karyawarta, rinka zuwa nan kawai ki karya ki tafi Makarantarki na te mata to.
Kashedin da tai tayi min ne yayi dalilin da na gama abinda zan iya na dauki Jakata nace wa Babah Lantana Baba a bani abin karyawana in na dawo sai in gama.
Ta ce, a’a ai sharadin karyawa gama aiki, ko nima da ki ke ganin kamar ina daga zaune ne kawai nake ci ba haka ba ne, da amfanin da nake yi wa uban naki ita kuma Asabe ita take girkawa, shi kuma sallau yana karbo cefanen.
Don haka kema sai kin gama naki nace to a bani kudin makarantar ta dago ta kalle ni, da su zan biya wadanda za su karasa aikin in kin tafi kin bar shi.
Na juya na kama hanyar fita daga gidan ina tunanin lokacin da Babana kan goya ni a kekenshi ya kai ni Makaranta, muna tafiya muna hirarmu komai na gani a hanya na ambaci sunanshi ya tsaya ya saya min.
Tun ma ba a ce lokaci ne nasu tsada su lemon tsuntsu su malmo ba amma wai a yanzu sai a hana ni abin karyawa da kudin Makaranta a kan idonshi yana kallo ba zai ce komai ba.
A gidan Umma nasha kunun gyada lafiyayyen alalan ganye sai da na koshi na dauki jakata zan tafi, ta ce min in an taso ki biyo ta nan kafin ki je gidan naku na ce to.
Muna tasowa gidan nata na fara zuwa, na samu dafadukan shinkafa da wake mai manja ya kuma ji busasshen kifi a ciki da dan yaji-yaji.
Na ci na koshi na nufi gidanmu, Babah Lantana bata bani ba nima ban tambaya ba, tunda dama ko nayi mata aikin duka ba kasafai nake samun abincin da zan cin ba.
Kusan wannan satin abinda ya rinka faruwa kenan, don haka har ranar Asabar ban saurari aikin Baba ba, balle in je ina jiran abin karyawanta, Umman ce kuwa ta koya min yin hakan.
Da yamma na shigo gida na samu Babana zuane kan tabarmarshi an kawo mishi abincinshi.
Ina kike tafiya ne Yaacuuwuna? Na kalle shi cikin ladabi na ce mishi, “Gidan Umma. Ban san yadda aka yi ba bai yi min fada ba, sai naji ya ce min to dauki wannan abincin kici, na ce to.
Ina daukan kwanukan Asabe ma ta zaburo da saurinta nima zan ci nima ban koshi ba Baba.
To ku ci mana, yayi maganar a hankali. Tayi maza ta biyo ni, To ki ajiye mana. A ha ina za ki kai? Kan in ce zan ajiye sai ga, Babah Lantana tazo ta fige kwanukan da ga hannuna ta tafi da su tana fadin aikin banza aikin wofi, ba ka iya komai ba sai lalatawa mutum tarbiya, a ina ake yin haka? ‘Ya’ya gansun-gansun kowacce a ka kaita gidan miji zata zauna sai kuma a ce kullum sai an basu sudin uba, to ban yarda ba”.
Ta juya ta tafi, duk da nasan ita ta koyawa Asabe irin wannan iya shegen saboda kyashin dan abincin da wani lokaci Babana rage min amma ban damu saboda na riga na koshi.
An kai maka maganar yawonta ba ka ce komai ba kazo kana rage mata abinci, don daurin gindi duk abin da ta kwaso dai ai a kanku zai kare kai da ita, yaja bakinshi yayi shiru, to balle kuma ni.
Washegari da safe na sake tambayarshi zuwa gidan Yaya Dijah cikin sa’a sai ya bar ni na tashi cikin zumudi da murna naje na gayawa Babah Lantana ta tabe baki ta ce sai kiyi ta tafiya.
A gidan Yaya Dijah ranar kamar zata lashe ni don dadi saboda na dade sosai ban je ba, itama kuma yanzu bata cika zuwa gidan sosai ba tunda Babah Lantana ta ce ta yafe amma wai babu sauran mu’amallah a tsakani.
Muka yi hira na bata duk labaran da ke cina a cikina, tunda yanzu na kara sanin darajarta, kullum kuma kara sonta nake yi.
Da yamma da zan tafi gida sai ta debo zannuwanta kala hudu da ta ce za su yi min da wasu sabbi da ta dinka man kala biyu ta hada min har da takalma guda biyu suma sababbi.
Nayi ta murna na dawo gida zuciyata cike da farin ciki, na shiga daki na adana kayana a cikin dan akwatina a zuciyata ina tunanin tun da jibi ne Juma’a to sai jibin zan fara saka su.